A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Tashi yayi yashiga Motarsa, ya jata da k’arfi yanufi gidansu Abdullah,
Kai tsaye yashiga gidan taredà sallama ya tsugunna ya gaida mamansu Abdullah, ya tambayeta ko Abdullah na ciki kuwa,?”
Tasheda mashi da cewa eh yana ciki barci yakeyi domin tund’azun befitoba,
Ya mik’e yashiga d’akin Abdullah,
Ya tarar dashi zaune a kan kujera yana gyangyad’i,
Yadukesa a kafad’a yace “meye kuma abun zama a kan kujera kana gyangyad’i saikace wani maraya?”
Abdullah yaturo baki yace "kabari kawai prince abubuwa suntafaru kwana biyu nan bangankaba idan nakira wayarka akashe nakejinta,
kuma gashi nadaina fita waje,
saboda nad’auko mgna, wani soja kenemana ruwa a jallo,
Prince yayi dariya yace “aikaidaman aikinka kenan d’aukar magana,
Yanzun kuma a hannun soja kafad’a?”
Ai kuwa zakaci dukan tsiya domin kasan halin soja ba sauki ke gareshiba,
Nidai ba wannan yakawoni ba,
Abdullah bakada labarin ‘yar gidanka Bilkisu?”
Domin naje makaranta tund’azun nayi zaman jiranta tunda safe bangantaba,
Kuma nasan Yanda Bilkisu keda nacin karatu, babu abunda zai hanata zuwa makaranta
Sai da babban lalura ko kuma ciyo.
Don Allah Abdullah kanuna mun gidansu Bilkisu,
Nadibota domin na tabbatarda lafiya glau yake,
Abdullah bakida hanci yasaki yana kallon prince cike da mamaki
Sannan yayi k’arfin halin yimasa magana, yace
“Prince lafiya kake kuwa?”
Kokasan abunda bakinka yake furtawa kuwa?”
Idan banjika sosai ba,
kamar cewa kayi nakaika gidansu Bilkisu domin kadibo lafiyarta?”
Prince yace “kwarai kuwa,
Hakan nace.
Abdullah yarik’e baki???? cike da mamaki,
Yace “prince yaushe hakan tafaru da kai?”
Badai kacemun
Zakayi son Bilkisu kakeyi ba?”
Prince ya dafa Abdullah yace “Abdullah babu tantama son Bilkisu nakeyi,
So kuma mai tsanani, a yanda nakeji bazan iya rayuwa batareda Bilkisuba,
Rashin ganinta da banyiba kwana biyu jinake kamar nahad’e zuciyata na mutu,
Domin nikad’ai nasan irin yanda nakeji da kuma yanayinda nake ciki narashinta,
Abdullah cike da al’ajabi yake kallon prince,
Yace kaikuwa yaushe hakan tasameka nafad’awa tarkon son Bilkisu?”
Prince yace “nima bansaniba farka kawai nayi naganni nafad’a tarkon sonta so mai tsanani,
Pls Abdullah karka kuma tambayata komai katashi mutafi kakaini gidansu Bilkisu sannan daga baya kaci gaba dayimun tamboyin da kakeyimun a kanta,
Abdullah yayi murmushi yace to ‘prince Bilkisu bata garin nan tatafi yola.
Nima garin bintane zuwa yolar Allah yahad’ani da wannan sojan wanda a yanzun yahani fita ko ina,
Yashiga fad’awa prince abunda yafaru tundaga farko har zuwa k’arshe,
prince dayake cikin halin tashin hankalin rashin Bilkisu, saida yayi dariya harda rik’e ciki,????
Abdullah yahasala da dariyarda prince yake masa, ya mik’e tsaye yanuna masa hanyar waje????????yace “kaga malam fitarmun daga d’aki nagaji dajin dariyarka,
Nad’auka tausayamun zakayi, nayi awon arziki amma saika sanyi a gaba kanayimun dariya,????
To fita kabani wuri nibansan gidansu Bilkisu ba, kaje can kanema.
Prince ya gintsi dariyar dayakeyi,
Ya zauna a kusa dashi had’ida rik’e hannunsa yace “haba my friend wasanefa niba kai nakeyiwa dariyaba,
Yasanya hannu a aljihunsa yaciro bandir d’in 1000 bandir biyu ya dank’awa Abdullah a hannunsa,
Yace wannan nakane abokina sakamakon
Labarinda kabani dayasanyani nishad’i nakyawawan halayya Bilkisu,
Abdullah yayi dariyar jindad’i
Yace aiba anan labarin yatsayaba domin kuwa bayan sun kammala waya da mahaifin nata,
Naji tana shaidawa safeenat cewa zata tafi yola,
Amma kwana d’aya zayayi zadawo,
Saboda shirye shiryen jarabawa dazasu farawa,
Kaga kuwa inhar kwana d’ayan tayi,
To ayau d’in nan yakama zata dawo.
Prince ya girgiza kai alamar jindad’in bayanin da Abdullah yayi masa,
Yace wa Abdullah tabbas a yau ne zatadawo,
Amma don Allah my friend karakani gidansu, mugani koda tadawo,
Nidai muradina naganta nayi ido biyu da ita koda zanji sanyi a rayuwatah.
Abdullah yatashi tsaye yace “ba matsala Prince komai zan’iya yimaka indai befi k’arfinaba musamman a kan gimbiya Bilkisu
Suka mik’e tsaye gaba d’ayansu,
Suka nufi hanyar fita daga d’akin,
Sai Abdullah yadawo baya ya zaune,
Prince yabishi da kallon mamaki yace “lafiya dai Abdullah?” Naga kadawo kasamu wuri kayi zamanka?”
Abdullah yace kamanta halinda nake ciki ne?”
Koso kakeyi infita inci garo da wannan k’aton sojan,
Ya sanya bindiga ???? ya d’aukemun kai da ita, ya harbeni kaikuma kayi tafiyarka kabarni nan,
Saikaci gaba da rayuwarka a duniyar cikin jindad’i ko?”
Prince ya dinga dariya,
Yace haba Abdullah ina tareda kai har soja ya isa ya harbeka ina tsaye kuma na kyalesa?”
Abdullah yayi dariya dominshi cika bakin prince har dariya yakebashi saikace wani jarumi,
Yace “lokacinda gimbiya Bilkisu takira fadawanta suka sanyani a mota suka yafi dani a lokacin kana ina?”
Tsaye kayi kana kallona kakasa tab’uka komai,
To wannan ma hka zakaga soja yasanya bindiga ya d’aukemun kai, kuma kakasa hassala komai,
Prince yayi dariya yace ai ita Bilkisu ta da bance,
Kuma sarautarsu k’arfi ke gareta,
Shi kuma soja yana k’arshin masarauta dole yayi masarauta biyayya domin a k’arkashin masarauta suke,
Don haka tashi mutafi babu abunda zai faruwa harmutafi mudawo my friend saki jikinka,
Yaruk’o hannunsa suka fita.”
Writing by Fareeda Bashir✍????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR…..
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
page 4⃣1⃣ 4⃣2⃣
WANNAN PAGE D’IN NAKUNE DOMIN JIN DAD’INKU MEMBER’S OF PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S, ALLAH YAK’ARA HAD’A KANMU YATSAREMU DA SHAIRRIN MAHASADA????????????????
Gimbiya Bilkisu Sunshigo garin Kano lafiya tareda fadawanta,
Gosulun motoci ne ya tsayardasu a kan titi sun d’auki kusan minti 10 sannan sukasamu gosolun ya tsagaita sukawuce,
Tafiya sukeyi saigani sukayi wata mota na biyarsu a baya,
Fadawa sune suka lura da hakan
Suka fad’awa Bilkisu, domin tambayi umurninta su tsaya suga kowaye ke biyarsu?” kosu cigaba da tafiyar da sukeyi?”
Tabasu umurni da karsu tsaya,
Watak’ila basu yakebiyaba.
Harsuka k’ara masaukin Bilkisu, suka tsaitsaya.”
Shima wadda kebiye dasu ya tsayar da motarsa a daidai wurin da suka tsaya,
Fadawa sukanufesa da alamar tambaya a fuskarsu, Bilkisu ce ta dakatardasu,
Dacewa “kubarshi ya k’araso muji abunda ke tafedashi.
K’arasowa yayi dai dai a kusa da ita, Fuskarsa kan Bilkisu yana murmushi,
Kallon mamaki tabishi dashi tana tunanin a ina tasan wannan fuskar?”
Cigaba yayi da kusantota da murmushi a kan fuskarsa,
Ganin hakan dayakeyi,
Fadawa basujira umurninta ba sukayi saurin dakatardashi,
Suka had’a baki gaba d’ayansu, suka
Dakata d’an talakawa.
Mundad’e muna sanyamaka ido kana bibiyarmu tun a kan hanya,
Meke tafe dakai?”
Bilkisu tayi saurin dokawa fadawa tsawa, tace “banason hakan banason ana wulak’anta d’an adam a gabana,
da talaka da mai kud’i duka Allah ya haliccesu, indai ina taredaku karna kuma jin kunyiwa kowanne mutun wannan kalamin,
Kubarshi ya k’araso nace, domin naji abunda ke tafedashi,
Bilkisu na magana amma kallonta yakeyi cike da sha’awa, bedamu da abunda fadawa sukayimasa ba,
Ya k’arasa kusa da ita yace “gimbiya Bilkisu halayarki suna burgeni suna kuma bani sha’awa,
Saboda kyawawan halayarki yasanya nake bibiyar rayuwarki domin ganin nacinma burina a kanki na aurenki,
Da farko sunana Zaharandin Mansur nid’an minister garin nanne,
Tun lokacinda nad’ora idona a kanki Allah yasanyamin sonki a rayuwata,
Bilkisu kyawawan halayanki sune suka kuma dasamun wutar sonki a rayuwata,
Harnakai bana iya ganin kowace mace a duniya sai ke,