A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Bayan antashi daga makaranta Adnan da Abdullah sukayi zaune a mota suna jiran fitowar Safeenat tareda Bilkisu,
Domin subi safeenat gida dansuyi magana da ita ta fahimta,

Sai hangosu sukayi sunfi Zaharandin yabud’e masu mota sunshiga yaja suka bar makarantar,

Prince yacije Baki, ya duki sitiyarin mota,
Had’ida kallon Abdullah yace “wlh Bilkisu sutake takasheni, ita bata lura da sonda nake mata takeyimun wannan wulak’ancin, amma nasan maganinta,

Yaja motar yabi bayansu.”

Luv u all????. Writing by Ummu safwan✍????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR…..

????????????????????????????????????????

    Writing by 
       Ummu
          Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 4⃣3⃣ 4⃣4⃣

Abdullahi ya rik’ashi yashi gardashi mota, saboda b’acin rain abunda Bilkisu tayimasa be iya tuk’a motarba,
Saidai Abdullah yaja motar suka tafi.”

Gida Abdullah ya nufadashi,
Yashigar dashi d’akinsa ya kwantar dashi a kan gadonsa,
Adnan sai zubar da hawaye yakeyi idan yatuna irin abunda Bilkisu tayimasa a gaban zaharandin,

Abdullah sai hakuri yake bashi,
Yana kuma lallashinsa,

Adnan ya kalli Abdullah idonsa jajir,
“Yace wlh Abdullah a kan Bilkisu komai zan iya aikatawa Zaharandin, dama tun a makaranta nake ganin take takensa a kanta, Ashe dama sonta yakeyi?”
To be i’sa yaja dani a fagen soyayya ba,
sai dai nasanya a b’atar dashi b’acewa ta har abada,
Ba d’an minister bane shi koda d’an shugaban k’asa ne be i’sa yayi ja yanya dani a fagen neman aure ba, musamman a kan Bilkisu.

Zubbur yayi yamik’e tsaye,
yanufi hanyar waje yana wani huci,
Abdullah yayi saurin rik’o hannunsa yace “prince ina zuwa haka?”

Prince yace “wurin dady zan tafi, nafad’a masa yasanya ranar aurenmu nan da sati biyu,
Domin nahuta da rad’ad’in sonta dake andabata a rayuwatah,

Abdullah yarik’e hannusa yace “idan kayi hakan mekayi kenan?”
Prince kazamo namijin duniya mana, kajajirce kasamo soyayya gimbiya Bilkisu da hannunka,
har lokacinda ta yarda ta amince, tasoka, a sannan saikuyi auren,

Domin na hango k’iyayyarka tsantsarta a idon gimbiya Bilkisu,
Wadda mundun kayi amfani da damar da kake da ita ka domin aureta,
to tabbas komai zai iya faruwa bayan aurenku.

Pls Adnan ka kwantar da hankalinka mubi komai a sannu har kasamo soyayyarta da kanka ta yarda dakai sannan kuyi auren sai kunfiyin zaman lafiya da jin dad’in rayuwar aurenku.

Sai a sannan Prince yaji dad’i, hankalinsa ya soma kwanciya, sai ya soma tunanin ta ina zai fara gyara kura kuransa?”
Da musgunawar da yadinga yiwa Bilkisu, wad’anda yasan har abada bazata tab’ata mantawa dasuba.

Ya kuma mai da kallonsa a Abdullah yace ” Abdullah ta ina zan fara Neman soyayyar Bilkisu?”
Harta yarda dani ta kuma amince dani har muyi aure?”

Abdullah yace “wannan nabarmaka daga yau zuwa gobe kayi tunani kasamo mafita,

Tashi tsaye yayi yacewa prince “zantafi gida sai dai gobe idan mun had’u a makaranta,
Kashigo da wuri domin Kasan munada test k’arfe 8:30am

Prince yace” ai dole nashigo da wuri kodan saboda naga sahibatar zuciyata,

Abdullah yayi dariya yafita had’ida jamasa k’ofa yace “Prince Adnan ankamu dayawa a soyayyar Bilkisu.

Bayan Abdullah yafita,
Prince har zaishiga toilet domin yin wanka,
Sai ganin Abdullah yayi yadawo a guje yana fitarda numfashin gudun dayayi,

Prince cikin gid’ima ya tambayesa Abdullah lafiya?” Meke faruwa?” Naga kadawo a guje hakan?”

Abdullah yakai zaune dafe dakai, yacewa prince “inafa lafiya ina fita yanzun naci karo da wannan masifanfen sojan,
sanye da kayan sojoji, da k’atuwar bindiga rataye a kafad’arsa.

      Yanuna prince da hannu????????  Wlh duk abunda yasameni da kai zanyi kuka, 

saboda saidana fad’a maka bazan fitoba amma katilassamin saida nafito yanzun ga irinta nan abunda nakewa gudu yafaru. ya d’ora hannu a kai????????‍♂ shikenan yanzun kasheni zaiyi.”

Adnan mezaiyi inba dariyaba,
Yacewa Abdullah “mutafi ka nunamun kowaye wannan sojan dayakeso yafirgitarmun da Amini,

Abdullah yakaimasa harara???? Yace “saidai kai kafita,
kagansa amma ni daga nan babu inda zankuma matsawa.

Prince safe da ciki yana dariya???? yace “to fad’amun a dai dai wane wuri kaganshi?”

Abdullah yace “daka lek’a waje,
zaka ganshi zaune a kan kujera, da bindiga a hannunsa.

Prince yafito yana dariya,
Mahmud ya hango abokin Fahad sanye da kayan sojoji
Adnan yayi murmushi yak’arasa wurinsa, had’ida yi masa sallama, ya mik’amasa hannu suka gaisa,

Adnan fuskarsa cikeda murmushi yace ” yaya mahmud,Ashe dama kaine ka firgita aboki?”
Aduk lokacin da yayi ido biyu dakai saika firgitashi har saiyasaki fitsari,

Mahmud yayi dariya yace “wannan abokin naka shikuwa menaimasa hakan?”
wadda yasanyashi jin tsorona harda fitsari?”

Adnan yana dariya yafad’amasa duk abunda Abdullah yafad’amashi a kan shi,

Mahmud dariya yashigayi, yace “tuni namanta dashi, nayi cigiyarsa kwana biyu domin nabashi kayansa bangansaba, yanzun haka jakar kayansa na but d’ina dasu nake yawo, ina cigiyarsa ko zanganshi amma ko alamarsa babu,
Namayar da kayan na’ajiye a but d’ina.”

Adnan yace yaya mahmud d’aukomun kayan nakai masa, domin maganar da nake maka yanzun haka yana d’akina ya b’oye,
da yalek’o ya ganka a zaune,
Domin idan bada kayansa nashigar masaba nanuna masa shedar ka hakuri, to kasani tsogunne bata k’areba, domin Abdullah bazai tab’ata fitowa daga d’akin nan nawaba, saboda tsoron da yake maka,

Mahmud yayi dariya yatashi yabud’e but d’in motarsa ya d’aukowa Adnan jakar kayan Abdullah yamik’a masa yace, “kace masa nace yafito mugaisa,
Gaba d’aya suka sanya dariya harda Fahad dayake k’arasowa.”

Adnan yashiga d’akinsa rataye da jakar kayan Abdullah,
Da shigarsa d’akin yadinga yiwa Abdullah dariya yana fad’in matsoraci, to ga jakar kayanka nan na k’arboma, gobe ma ka kuma shiga motar soja kace yola zakatafi.

Abdullah ya k’arbi jakarsa be kuma cewa Prince komaiba,
Yafito yayi tafiyarsa.”

Bilkisu kuwa da shigarta gida, fad’awa tayi a kan makeken gadonta tashiga rera kuka,

Jakadiya tajiyo kukanta, taturo k’ofa tareda sallama, tashigo d’akin , taganta cikin yanayin tashin hankali,
Tashiga tambayarta,
Gimbiya Bilkisu meke faruwa kike kuka hakan?”
Nidai a iya sanina lafiya k’alau muka dawo, babu wani abu danasani wadda yake damunki,
Amma yanzun cikin lokacin k’ank’ani rayuwarki yab’aci harkike zubarda hawayenki.

Bilkisu tayi murmushin dole, tadafa jakadiya tace “karki damu jakadiya wani abu ne, take Neman sanyani gaba,
kitaimaka mun da addu’a, idan nasamu lokaci zanfad’a maki komai.

Jakadiya tace “Allah ya sausauta maki ko menene shi,shugabata,
Bilkisu tace Amin.”

Wayarta ta d’auka takira safeenat, take shaida mata da cewa tadawo,
Safeenat tashiga murna dajin dad’i daga nan take shaimata gobe sunada test da safe dan haka tashigo makaranta da wuri,
Bilkisu tayi murmushi tace Alllah ya kaimu my sis.”

Shiri takeyi domin tafiya makara,
atamfarce a jikinta tasanya hijabinta har k’asa, tad’auko jakarta ta rayata, tayi kyau sosai,
Tafito tayiwa jakadiya sallama tanufi makaranta,

Tafiya takeyi saiji tayi ana mata horn,
Bayanta, Bata waigaba, kuma bata fasa tafiyarba sai sauri take domin tak’arasa makaranta,

Ganin batada niyar tsayawa,yasanya, yayi saurin shiga gabanta, ya gifta mata mota ya tare mata hanya.”

Writing by fareeda Bashir
(UMMU SAFWA)
LUV U ALL????????????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button