A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Tashi tsaye yayi yacewa prince “zantafi gida sai dai gobe idan mun had’u a makaranta,
Kashigo da wuri domin Kasan munada test k’arfe 8:30am

Prince yace” ai dole nashigo da wuri kodan saboda naga sahibatar zuciyata,

Abdullah yayi dariya yafita had’ida jamasa k’ofa yace “Prince Adnan ankamu dayawa a soyayyar Bilkisu.

Bayan Abdullah yafita,
Prince har zaishiga toilet domin yin wanka,
Sai ganin Abdullah yayi yadawo a guje yana fitarda numfashin gudun dayayi,

Prince cikin gid’ima ya tambayesa Abdullah lafiya?” Meke faruwa?” Naga kadawo a guje hakan?”

Abdullah yakai zaune dafe dakai, yacewa prince “inafa lafiya ina fita yanzun naci karo da wannan masifanfen sojan,
sanye da kayan sojoji, da k’atuwar bindiga rataye a kafad’arsa.

      Yanuna prince da hannu????????  Wlh duk abunda yasameni da kai zanyi kuka, 

saboda saidana fad’a maka bazan fitoba amma katilassamin saida nafito yanzun ga irinta nan abunda nakewa gudu yafaru. ya d’ora hannu a kai????????‍♂ shikenan yanzun kasheni zaiyi.”

Adnan mezaiyi inba dariyaba,
Yacewa Abdullah “mutafi ka nunamun kowaye wannan sojan dayakeso yafirgitarmun da Amini,

Abdullah yakaimasa harara???? Yace “saidai kai kafita,
kagansa amma ni daga nan babu inda zankuma matsawa.

Prince safe da ciki yana dariya???? yace “to fad’amun a dai dai wane wuri kaganshi?”

Abdullah yace “daka lek’a waje,
zaka ganshi zaune a kan kujera, da bindiga a hannunsa.

Prince yafito yana dariya,
Mahmud ya hango abokin Fahad sanye da kayan sojoji
Adnan yayi murmushi yak’arasa wurinsa, had’ida yi masa sallama, ya mik’amasa hannu suka gaisa,

Adnan fuskarsa cikeda murmushi yace ” yaya mahmud,Ashe dama kaine ka firgita aboki?”
Aduk lokacin da yayi ido biyu dakai saika firgitashi har saiyasaki fitsari,

Mahmud yayi dariya yace “wannan abokin naka shikuwa menaimasa hakan?”
wadda yasanyashi jin tsorona harda fitsari?”

Adnan yana dariya yafad’amasa duk abunda Abdullah yafad’amashi a kan shi,

Mahmud dariya yashigayi, yace “tuni namanta dashi, nayi cigiyarsa kwana biyu domin nabashi kayansa bangansaba, yanzun haka jakar kayansa na but d’ina dasu nake yawo, ina cigiyarsa ko zanganshi amma ko alamarsa babu,
Namayar da kayan na’ajiye a but d’ina.”

Adnan yace yaya mahmud d’aukomun kayan nakai masa, domin maganar da nake maka yanzun haka yana d’akina ya b’oye,
da yalek’o ya ganka a zaune,
Domin idan bada kayansa nashigar masaba nanuna masa shedar ka hakuri, to kasani tsogunne bata k’areba, domin Abdullah bazai tab’ata fitowa daga d’akin nan nawaba, saboda tsoron da yake maka,

Mahmud yayi dariya yatashi yabud’e but d’in motarsa ya d’aukowa Adnan jakar kayan Abdullah yamik’a masa yace, “kace masa nace yafito mugaisa,
Gaba d’aya suka sanya dariya harda Fahad dayake k’arasowa.”

Adnan yashiga d’akinsa rataye da jakar kayan Abdullah,
Da shigarsa d’akin yadinga yiwa Abdullah dariya yana fad’in matsoraci, to ga jakar kayanka nan na k’arboma, gobe ma ka kuma shiga motar soja kace yola zakatafi.

Abdullah ya k’arbi jakarsa be kuma cewa Prince komaiba,
Yafito yayi tafiyarsa.”

Bilkisu kuwa da shigarta gida, fad’awa tayi a kan makeken gadonta tashiga rera kuka,

Jakadiya tajiyo kukanta, taturo k’ofa tareda sallama, tashigo d’akin , taganta cikin yanayin tashin hankali,
Tashiga tambayarta,
Gimbiya Bilkisu meke faruwa kike kuka hakan?”
Nidai a iya sanina lafiya k’alau muka dawo, babu wani abu danasani wadda yake damunki,
Amma yanzun cikin lokacin k’ank’ani rayuwarki yab’aci harkike zubarda hawayenki.

Bilkisu tayi murmushin dole, tadafa jakadiya tace “karki damu jakadiya wani abu ne, take Neman sanyani gaba,
kitaimaka mun da addu’a, idan nasamu lokaci zanfad’a maki komai.

Jakadiya tace “Allah ya sausauta maki ko menene shi,shugabata,
Bilkisu tace Amin.”

Wayarta ta d’auka takira safeenat, take shaida mata da cewa tadawo,
Safeenat tashiga murna dajin dad’i daga nan take shaimata gobe sunada test da safe dan haka tashigo makaranta da wuri,
Bilkisu tayi murmushi tace Alllah ya kaimu my sis.”

Shiri takeyi domin tafiya makara,
atamfarce a jikinta tasanya hijabinta har k’asa, tad’auko jakarta ta rayata, tayi kyau sosai,
Tafito tayiwa jakadiya sallama tanufi makaranta,

Tafiya takeyi saiji tayi ana mata horn,
Bayanta, Bata waigaba, kuma bata fasa tafiyarba sai sauri take domin tak’arasa makaranta,

Ganin batada niyar tsayawa,yasanya, yayi saurin shiga gabanta, ya gifta mata mota ya tare mata hanya.”

Writing by fareeda Bashir
(UMMU SAFWA)
LUV U ALL????????????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR……

????????????????????????????????????????

   Writing by 
      Ummu
         Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 4⃣5⃣ 4⃣6⃣

Sai ganin xaharandin
tayi cikin motar fuskarsa d’auke da murmushi,
Ya bud’e murfin motar yafito fuskarsa cike sa fara’a,
Yake cewa gimbiya barka da fitowa tund’azun nake zaman jiranki fitowarki domin naga kyankyawar fuskarki koda zanji dad’i a rayuwata,

Bilkusu ta kallesa sama da k’asa, tace “nagode zaharandin da kulawarka gareni amma kasani idan ina tafiya ba’a tareni a hanya, ina fatan hakan yazamar makashine na k’arshe

Xaharandin yace insha Allah gimbiya hkan bazai kuma faruwaba,

  Nasan makaranta zaki tafi pls kishigo mutafi nima  can zantafi,

Tayi murmushi tace “nagode zaharandin a k’asa nakeso natafi,

Ya durk’usa k’asa yana rok’unta, yanafad’in gimbiya kiyi hkr kishigo nak’arasa da ke,
Banaso kina tafiya a hanya, kamun ki kai duk namijin da yaganki nasan sai ya kalleki, ni kuma yi hakan zai iya sanyamun ilah a rayuwata,
Pls Gimbiya Dan Allah badan halinaba kishigo nak’arasa dake makaranta,

Ganin ya had’ata da Allah yasanyata shiga motar suka nufi makaranta,

Tafiya sukeyi sai fira yakemata tun bata kulashi hartasoma fara kulashi,
A nan ta fahimci zaharandin mutum ne mai yawan barkwanci, a haka har suka isa makaranta,

Shigarsu makarantar yayi daidai da fitowar prince daga class,
Kallo yabisu dashi cike da tashin hankali da tsantsar kishi a fuskarsa,

Bilkisu ta hango prince tsaye ya tsura masu ido yana kallonsu, saida gabanta yafad’i, amma kuma ta dake tabiyewa Zaharamdin yaci gaba da bata labari tana dariya,

Jikinsa ne yasoma rawa alamar b’acin rai zuciyar maza ta motsa,
Abdullah yayi saurin matsowa kusa dashi ya rik’ashi ya zaunar dashi, yana bashimagana,
“Pls Adnan ka sansautawa rayuwarka, kadaina nuna kishinka hka akan Bilkisu, wadda batasan kanayiba,
Idan ta fahimci kana kishinta hakan, to tabbas na tabbata zatadingabi ta wannan hanyar domin ganin ta tadinga musgunawa rayuwarka ,

Adnan yadafa Abdullah yamik’e tsaye, yace “Abdullah son Bilkisu da kishinta suna neman kasheni, bakaji yanda nakeji a zuciyataba idan nasanya idona naganta tareda zaharandin Jina nakeyi kamar nahad’iye zuciya na mutu,
zansanya a d’aukemunshi, tabar ganinsa gaba d’aya,
domin ya daina d’aukemata hankali, har saina dasa soyayyata a zuciyarta harmuyi aure

Abdullah yace “haba abokina kazamo namijin duniya mana a fagen soyayya, idan kasanya aka d’aukesa tomekayi kenan?”
hakuri zakayi kafafata dashi harkasamu ka kwato soyayyarka awurin Bilkisu,

Duk maganganunda sukeyi a she akan kunnen Safeenat sukeyinsu,
Tazo wucewa, takusa dasu, basu d’ura da itaba,
Sai gani sukayi tarab’asu ta wuce, had’ida yimasu wani kallo na nuna alamar duk abunda kuke fad’i najishi a kunne na,
Tanufi wurin Bilkisu cike da mamaki ganinta tana magana da xaharandin harda dariya.

Adnan yabita da kallon mamaki,
Yajuya ya kalli Abdullah yace masa “ina ganinfa duk maganganun da mukeyi Safeenat tajisu,
Abdullah meye mafita?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button