A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Yau ga Adnan ya kwanta ciyo saboda yana Neman wani abu a rayuwarsa besamuba,
Fahad menene shi?”
Menene d’an uwanka yake nema yarasa wadda har yake Neman rasa rayuwarsa?”
Fahad ya kalli mahaifinsa, idonsa cike da hawaye saboda tausayin mahaifin nasa,
Yace “Abba nasan baka ragemu da komaiba a rayuwa, duk abunda mukeso kanayimana shi in dai har kud’i na sayensa,
Amma Abbah na alak’anta ciyon Adnan ga Bilkisu,
Fahad yanuna Bilkisu
Likita shima ita yake kallo,
Domin Adnan yanason Bilkisu kamar rayuwarsa, gani yakeyi kamar baza a aura masa Bilkisuba,
Sai sannan likita yayi magana yace “tabbas ciyon Adnan yanada alak’a da Bilkisu, idan akayi dibon yanda aka kawosa ko numfashi bayayi, amma jinta da yayi a kusa dashi, yasa haryake iya bud’e idonsa,
Ya kuma jayo hannunta ya rike da hannunsa,
Abba yayi murmushi irin nasu na manya,
Yace doctor yanxun meye mafita?”
Docter yace “mafita d’ayace a aura masa Bilkisu,
Gaba d’aya d’akin suka amsa da tabbas ahakan shine mafita,
Bilkisu na durkushe a a gab gadon Adnan, hannuta rike da na Adnan tad’ora kanta a kan k’irjinsa tana sauraren numfashinsa dan ganin takeyi da zarar tad’a daga daga wurinsa mutuwa zaiyi,
Tana sauraren duk maganganun da sukeyi harda anty Bahijja amma bata kulasuba ita dai burinta Adnan yatashi karya mutu ya barta,
Shi kuwa likita sai kokarin yake yaga fuskar Bilkisu, yaga wacece wannan Bilkisu wadda Adnan d’an sarki yakeso har yake neman rasa rayuwarsa a kanta,
Ganin batada niyar d’ago fuskarta bare ya ganta,
Yace to gimbiya kitaimaka kiceto rayuwar Adnan,
Sai anan tad’ago fuskarta sukayi ido biyu da doctor,
Doctor yace Bilkisu dama kece Adnan ya haukace a kan sonki?”
Doctor yamaida kallonsa ga maimartaba, yace ranka ya dad’e wannan itace
Wanda ta taimakesa tabashi kininta aka Sanya mashi lokacin da mota ta tureshi,
Amma ta rok’emu da cewa don Allah karmu fad’i sunanta, ta taimakesane domin Allah,
Ai kuwa maimartaba yashiga sanya mata albarka,
Bahijja ta matso kusa gareta ta rungumeta cike da jin dad’i,
Bahijja tace wannan kad’an daga cikin kyawawan halin Bilkisu,
domin a kwaita da jink’ai da tausayin, da kuma taimakawa duk mai buk’ar taimako,
Saboda kyawawan halayanta Abbanmu yake alfahari da ita cikin ‘ya’yansa,
Duk abuda ake fad’a a kunnen Adnan,
Jin dayayi likita yace jinin Bilkisu ne aka sanya masa, sai ya kuma jin wani tausayinta dawani sonta yana k’ara shigar masa a cikin zuciya, jiya yake gaba d’aya ciyonda kedamunsa bayajinsa,
Mik’ewa yayi tsaye yanufi Abbansa ya rungumesa yana fad’in Abba Bilkisu Abba ka auramun Bilkisu, idan narasa Bilkisu zan iya rasa rayuwatah,
Mai martaba yashiga jinjiga bayansa, kamar wani yaron goye,
Yana fad’in ka kwantar da jankalinka insha Allahu Bilkisu takace, zata kuma zama matarka da yarda Allah,
Yasaki Abba yanufi wurin Bilkisu dake tsaye kusa ga Bahijja ya durk’usa wurin k’afarta
Yashiga yimata magiya,
Pls Bilkisu kisoni ki k’aunaceni wlh inason so nagaskiya ba nawasaba
Ki manta da abunda yafaru a baya shairin shaid’an ne, son gaskiya nake maki, pls Bilkisu Dan Allah kirabu da zaharandin wlh idan ina ganinku a tare zan iya rasa rayuwata,
Bilkisu ta runsuna k’asa ta d’ago Adnan sama ta tsura masa ido cikin so da k’auna,
Tace kadaina duk’amun kana Neman soyayyata na dad’e da Amincewa da kai, da kuma soyayyarka,
prince inasonka, kuma zan aureka kadaina d’aga hankalinka a kaina nitakace har abada,
Adnan yaji dad’in kalaman Bilkisu jiyaye kamar ya rungumeta, amma yaji nauyin yin hkan,
Murmushi yake sakar mata naso da k’auna,
Sannan yace “nagode beautynah had’ida yashafo fuskarta,
Likita naganin hka yace “dama ciyon Adnan na Bilkisu ne,
Kuma gata kusa gareshi ya warke, don haka na sallameshi, gaba d’aya d’akin suka sanya dariya,
Bahijja tace prince basu ciyon love,
Sukadinga yimasa dariya,
Sannan daga k’arshe suka fito gaba d’ayansu zasu tafi gida,
Likita yacewa dady yana son magana dashi a office d’insa,
Dady yasame doctor, doctor yasoma cewa dady
,
“Allah ya taimakeka ranka ya dad’e dama shawarace zanbayar gameda Adnan,
Tunda dai har wadda yakeso itama tana sonsa mexai hana ayi bikinsu a cikin satin nan,
Saboda yanayin ciyonsa,
Idan ya kuma shiga damuwa haryakai da fad’uwa to tabbas komai yana iya faruwa dashi,
Shiyasa nake ganin maganin ciyonsa ayimasa abunda yakeso wato a aura masa Bilkisu cikin satin nan,
Maimarta ya kalli doctor yace “nagode likita da shawararka kuma insha Allah Adnan zai kawo maka IV aurensa cikin satin nan,
Doctor yayi dariya yace Allah yanuna mana danafi kowa jin dad’i,
Sannan maimartaba yafito office d’in likita ya tararsu a mota suna jiransa tareda fadawansa suka d’unguma suka nufi gida,
Bilkisu saida ta nuna alamar bazatafisu gidansuba ita dai gida zata koma wurin jakadiya,
Adnan yarik’e mata hannu gam,
Yana fad’in bazata kuma zama a wannan gidanba,
Shikenan tadawo gidansu,
Inda zaharandin be isa yasanya k’afa yatako wannan masarautarba,
Haka dai tabiye masa suka nufi gidan Nasu,
Saboda tana gudun kartayi jayayya dashi ranshi ya b’aci harya kai ciyon zuciyarsa yatashi yafad’i yarasa rayuwarsa,
Agurguje
Bayan komawarsu gida,
Maimartaba yakira sarki Abdulrahaman, mahaifinsu Bilkisu, yasheda masa da duk abunda yake faruwa,
Gameda Adnan da Bilkisu,
Yashiga ruk’onsa a kan yajanye k’udiriinsa na cewa Bilkisu saita kammala karatu, sannan ayi aurensu, ya taimaka yaceto rayuwar d’ansa Adnan ayi aurensu,
Adnan yayi alk’awalin zaibarta tayi katun, tun daga nan har k’asar waje,
Babu abunda ya d’agawa maimartaba mahaifin Bilkisu hankali, dayaji mahaifin Adnan yace “Adnan yana iya rasa rayuwarsa idon besamu Bilkisu ba,
Shikuma ya tsani a sanadiyarsa wani ya rasa rayuwarsa,
Yanisa yacewa Bashir mahaifinsu Adnan,
“Wannan batsala bace,
Zankira ita gimbiya Bilkisu naji nata ra’ayi akan hkan,
Sukayi sallama akan cewa zuwa anjima zasu kuma yin mgna,
Bilkisu na kwance a d’akin Bahijja,
Adnan ya sanyata a gaba sai shagwab’a yake mata,
Bahijja sai dariya takeyimasa tana fad’in Ashe Adnan da Bilkisu an iya soyayyah,
Saiji tayi wayarta na ringing, tayi saurin kai hannuta ta d’auka saiganin kiran Abbantane tayi murmushi tayi,
Takara wayar a kunnenta
Had’ida yimasa sallama,
Maimartaba cikeda murna da jindad’i, jin muryar gimbiya Bilkisu,
Nan suka gaisa, yashiga fad’amata yanda sukayi da mahaifin Adnan metagani,
Ta Amince ayi auren nasu?” daga baya tayi karatun kobata amince ba?”
Bilkisu tace Abba na Amin
Allah yasa hakan shiyafi alkhairi,
Abba yace “Amin gimbiya,
Anan sukayi sallama da ita,
Yakira sarki Bashir mahaifinsu Adnan yashaida masa, ya Amince da buk’atarsa,
Anan suka yanke shawarar sanya ranar biki sati maizuwa,
Bilkisu takira safeenat tana fad’amata duk yanda akayi,
Safeenat tashiga murna tareda sheda mata gobe tana nantafe tareda jakadiya,
Sukayi sallama ta’jiye wayar cikin murna da farin ciki
Kowane gida biyun nan sunshiga murna da jin dad’i,
Yaya Abdul, yazo garin kano, maimartaba da Ammi suka turosa akan yatafi da Bahijja da kuma Bilkisu,
suka shiga shirya kayansu domin komawa yola, shirye shirye biki,
Rakiya akayimasu Fahad da Adnan tareda safeenat kowannesu sai fatan alkhairi akeyimasu,
Adnan da Fahad sunyibak’in cikin komawarsu sai don bayada zasuyine,
Yaya Abdul kuma dashida safeenat Ashe sun fahimci junansu, tun wani zuwa da yatab'ayi domin kawowa Bilkisu ziyara,
Amma Bilkisu bata saniba,
Sai yanzun yake shaidawa maimartaba Bashir mahaifinsu Adnan akan cewa shimafa yaga wadda yakeso
Ya wakilta maimartaba da a nemamasa auren safeena haka kuwa akayi, maimartaba ya aika akakira masa mahaifin safeenat, yanemawa Abdull aure,
Anan take aka sanya rana lokaci d’aya dasu Bilkisu,