A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

fad’amasa mgna.”
Bakinsa yacije ya kaiwa gado daushi.”
” impossible. bazai yuyuba.” Yazama dole nasan ko ita wacece?.” Waye ubanta?.” a fad’in duniyar nan.” dame take tak’ama?.” Dolene nasanya a abincika mun asalinta domin nasan ko ita
wacece?” Sanan na d’auki kwankwaran mataki a kanta.”
Kai tsaye toilet yashiga, domin yai wanka koda zaiji sanyi avrayuwarsa.”
Gimbiya bahijja sun sauka lafiya.”
Motocinsu ne, ke tsayawa a harabar gidan sarkin kano.”
Lokacin, Yayi dai dai da fitowar, yarima Fahad da prince Adnan zasu fita.”
Tsayawa yayi yabi motocin da kallo, domin a xahirin gskya kowaye a cikin motar yabashi sha’awa. prince Adnan yasaki baki yana kallon waye zai fito a cikin motar.”
yanayi motocin, da kuma yanayin wadda ke cikin motar, tabbas yasan yanaji da mulki da saurata.”
Sai yadinga maganar xuci, inama shine a cikin wnn daular.”
Sai mgnar Bilkisu tafad’o masa a rai.”
datake cewa. “Idon mulki kake tak’ama dashi.” to kasani, mulkin wata masarautar, yafi mulkin masarautarku.”
Idon kuma sarauta kake tak’ama da ita.”
To kasanya a ranka sarautar wata masarautar tafi sarautar masarautarku.”
Ganin wad’an nan motocin kawai ya i’sa, yabawa kansa amsar, maganar da Bilkisu tafad’a masa.”
Yarima Fahad yanufi motar da murmushin sa, a kan fuskarsa, motarda gimbiya Bahijja ke ciki, yanufa,
Domin shi tun shuguwarsu, yagane tambarin masarautar yola.” Domin yana yawan zuwa yola sada xumunta.” Allah yayiwa yarima Fahad son ‘yan uwa, da kuma sada xumunta.” Sab’anin prince Adnan, daba kowa yasaniba a cikin ‘yan uwansaba.”
Prince Adnan kuwa tsaye yayi yana kallonsu. Yaga waye zaifito a motar.”????
Lokacin gimbiya Bahijja, fadawa suka bud’e mata mota.” fitowa tayi, cikin shiga ta alfarma, wadda tafito mata da kyanta, da kuma mulkinta, fitowa tayi cikin k’asaita da i’sa da kuma mulki.” sukuwa kuyanginta mata sai fifita sukemata suna jeramata sannu, had’ida yimata kirari.”
Yarima Fahad naganin ta, ya shedata, domin shi rabonda ya ganta, tun lokacinda yakaiwa Ammi wata Zayara shekara shidda da suka wuce.”
Itama hakan. taganesa, sai kawai tasakar masa murmushi tanufosa.”
Cikin k’asaita, take mgna, “yaya kafa ganni amma ka kyaleni bakaje kataroniba.”
Shima murmushi yayi, yace “gimbiya Bahijja barka da xuwa.” Bagashi natafo nayiwa k’aunata oyoyo ba.”
Gaba d’ayansu sukasanya dariya.”
prince Adnan dake tsaye yana kallonsu, yakasa k’arasawa a inda suke, sai k’okari yakeyi yaga fuskar kowace Fahad ke mgnada da ita.”
lura yayi da fuskar,
Ai kuwa a take gabansa yafad’i.”
Domin yarasa a inda yasan wannan fuskar.”
Kuma tanayimasa kama da, wadda yasani, da fuskar.”
Bekawo Bilkisu a rywarsaba, domin, yasan ita bakowa bace face ‘yar matsiyata.” bare yayi tunanin ta had’a wata a lak’a da masarauta.”
Yarima Fahad ne yakatse masa tunanin dayakeyi, yace “Adnan baka ganeta ba ne,?”
Katsaya kasaki baki, da hanci , kana kallon mutane.”
Sai a lokacin ya k’araso a inda suke, yace “yaya naganeta mana, ba Bahijja bace ‘yar gidan Ammi?”
Yace “itace shine bazaka gaida ita ba?”
Kuma bazaka kirata da Anty ba.” Sai dai Bahijja kai tsaye?”
Yanayimasa mgna amma rik’e yake da kunensa.”
Yace “wayyo yaya sakarmun kunne.”
Amma fa nga sati d’aya kawai tabani.” Shine zance mata Anty.”
Kuma fa dataxo kai, d’aya tayiwa mgna. Ni ko kallona batayiba.”
Ya kuma jamasa kunne.” Yace ” maza ka gaida ita.”
kace Anty ina wuni.sannan zan sakarmaka kunne.”
Yace “to Anty ina wuni.”
Bahijja tayi dariya cikin k’asaita, tace “lfy k’alau d’an k’anena.”
Gaba d’ayansu suka Sanya dariya, suka d’unguma sai fadar maimartaba.”
, amma banda prince Adnan domin yanada muhimmin abunda xai aiwatar yau d’in nan
UMMU SAFWAN
????????????????????????????????????????
A WATA MASAUTAR…
????????????????????????????????????????
Writing by Ummu Safwan 07066214433
Pure moment of life writer’s
1⃣5⃣
A guje yashigar da motarsa cikin makarantar, bexame a ko inaba sai ofishin shugaban makarantar.
Betsaya neman ixininba , kai tsaye ya afkamasa batareda sallama.
Malam Sanusi dake xaune a kan kujerarsa yana rubuce rubucen takardunsa.
Sai ganin prince yayi a gabansa .”
Abun yabashi mamaki matuk’a, ko dadai yasaba da rashin sallamar prince idon xai tafo wurinsa, shima abun yana damunsa sai dai ba yadda zaiyi idon yanason yaci gaba da aikinsa.”
Kallo yabisa dashi yana murmushin dole yaimasa nuni da hannu, yace “zauna mana yarima.”
Anan Adnan ya maida kallonsa a kujerar da malam sanusi yanuna masa domin ya zauna.”
Yaja kujerar ya zauna, cike da i’sa da k’asaita,
Ya maida kallonsa a wurin shugaban makarantar,
Yace ” wurinka nazo. Inason kayi mun aikin kud’i, tun daga miliyan d’aya har xuwa miliyan goma
Idon kuma kud’in sunyima kad’an, kana iya kafad’i konawa kake buk’ata, xan iya Baka, idon har kacika mun burina.”
Malam Sanusi yayi murmushi yace “fad’i buk’atarka ina saurarenka Prince.
Prince Adnan yace ” wata yarinya nakeso a kora, a makarantar nan, idon akayimun hka, nayima alk’awari duk abunda kake buk’ata zanyima, komai girmansa.
Malam Sanusi ya kalli prince yayi murmushi yace “idon wannan ne bakada matsala prince, fad’amun wacece?” Kuma meye sunanta?.”
Prince yace”Sunanta Bilkisu Abdulrahaman yola
Jin prince ya ambaci sunan Bilkisu, yasanya malam Sanusi yayi saurin kallon prince a raxane,
Yace “a gaskiya wannan yarinyar bata koruwa a makarantar nan.
Prince najin hka, a nan take ya canxa fuska, yace “saboda me bata koruwa?” Ita wacece?” Kuma d’iyar waye?” Waye ubnta?”
Duka ya jeromasa wad’an nan tambayoyin.
Malam Sanusi shuru yayi, yana tuna abunda sarki Abdurhaman yafad’a masa gameda Bilkisu,
Ya d’ago kansa ya kalli Prince yace “kayi hakuri prince bawai don nak’i aiwatar maka da buk’atarka bane, a’a, ina mai Neman afuwarka, akan wannan buk’ata taka, sai dai idon zaka canza da wata zan iya aiwatar maka da ita, amma banda wannan.
Prince ya kalle malam sanusi, ransa a b’ace, yace “tambayarka nayi waye ubanta?” Dabata koruwa a karantar nan?”
Malam Sanusi yace “gaskiya bansan kowaye ubntaba, don hka kaje kayi bincike koda xaka samo labarin ubnta ko waye shi.
Bai kuma bi takan malam Sanusi ba,mik’ewa yayi, yafito ofishin a fusace, anan ya had’u da Abdullah abokinsa, yace ” waye yatab’a mazaje?”
Prince yyi murshin da yafi kuka ciyo, yashiga fad’awa Abdullah ynda sukayi da malam Sanusi,
Ya kalli Abdullah yace. Abdullah inason kabin cikomun asalinta dana iyayenta,
Abdullah yace ” bakada matsala a kan wannan.”
Prince yayi murmushin jin dad’i sannan yashiga motarsa yawuce gida.”
Bahijja zama yayi dad’i a wurin hajia Nafeesa,
Zamane Wadda take taka tsantsan da abunda zai b’atawa hajiya nafeesat rai,
Domin kuwa Bahijja akwaita da gudun zuciya, gata batada yawan magana, idon safiya tawaye abunda ke gabanta shitakeyi, tana gudun zuciyar hajiya nafeesat.
Yarima Fahad kuwa bayada wurin zama yanzun sai b’angaren hajiy Nafeesart,
Domin sunshak’u da Bahijja, Shak’uwa mai tsanani har yakai baya iya cin abincin kowa a gidan sai wadda Bahijja tadafa masa,
Shak’uwa mai tsakanin tashiga tsakaninsu har yakai kowa a gidan yanajin dad’in kasancewarsu a hkan,
Musamman maimarta sarki Bashir dayake addu’a Allah yasanya soyayya ce a tsakaninsu. Domin hakan shi zai k’aramasu dankon zumunci tsakaninsa da sarki Abdulraham.”