ALIYU GADANGA Page 1 to 10

#Comment,share and Vote..#
#Janafy…#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty????_
*DEDICATED TO MY MOMMAH..HAUWA .S.ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_*Assalamu Alaikum janafty Freeking Fans,gawani albishir din danake tafe muku dashi,Ko kuna da lbrin shahararriyar marubuciyar zamanin nan,wacce ta dade aharkan Rubutu,tana fayyace muku,yadda yanayin zamantakewar rayuwar da kullum take,wacce tadade tana haskaka zuciyarku da dadaddan littafanta masu dadi da Fasaha,masu dauke da darussa masu dimbin yawa,kada nacika ku da dogon lbri Ina Nufin NABILANCY LUV(Antyn S&S) wacce tazo muku da wani Salon lbri mai Tafiya da salon zuciyar mai karatu bakowani littafi bane illah…,MAKAUNIYA..(Labarin cin Amanar kauna)kunemi naku kusha karatu domin amfana da Abubuwan ban mamakin dake cikin littafin,Karki bari karka bari abaka lbrin MAKAUNIYA..(Labarin cin Amanar kauna)*_
*Chapter5*
“”Cikin Nasara ya kammallah karatunshi yana gamawa ya tafi NDA wato Nagerian Defence Acadamy yayi wata ashirin da hudu ma”ana yayi Short Service kenan,yana gamawa yafito amtsayin SECOND LEUTANET,Tunda Aliyu ya Fito amtsayin Soja gwazonshi da kuma yadda yake Kaunar Abun Aransa yasa,nan da nan yayi Fice kowa ya sanshi,Saboda yana Bama Abu muhimmanci uwa uba kuma jarumi ne,mara tsoro shekaransa daya dawani Abu ya samu karin girma Zuwa LEUTANET,daganan yayi ta samun cigaba tare da karin mikamai Har zuwa yanzu dayake mtsayin CAPTAIN wanda yake karshinshin 1 DIVISION NIGERIAN ARMY KADUNA..
Shekarunsa na haihuwa kimanin 30 kenan,duk inda ake Neman cika da cikar zati da Haiba Aliyu Gadanga ya hadashi,Kyakyawane na gaske,sakamakon kamar dayake da mahaifinsa,in ka gansa akallo farko sai ka yankemai Hukunci dayana da girman kai,saboda mutum ne,mai iko da takama,yana da jinkai,in yana wani Abun sai kadauka yahada jini da Sarauta saboda yadda yake gudanar dawasu abubuwansa,Yana da karancin Fara”a Akan Fuskarsa wani lokacin ya hade Fuska sai yabaka,tsoro sai ka ga yana wani Abu kamar afilin daga,Aliyu gadanga miskili ne na karshe wanda Abokan aikinsa ke masa lakabi da *CAPTAIN A A TAMBARI BUZU..* gashi ya kasance mutum ne dabayason Raini da Sakarci,baya da wasa ko kadan,yana da mugun son Girma kamar gyambo,yana so ka bashi girma koda kai din ka girmesa atakaice dai,yana son Abashi respect na karshe,kana baya da wasa yasan salom mugunta kala,kala,A iya shekarunsa ya fuskacin kalubalen Rayuwa na yadda ake masa kallom mara Uba,wanda ba”a son Asalinsa ba,Shiko Mahaifiyarsa tarigaya datamai duk wani ,bayani,banda Sunan mahaifinshi da yanki daya fito basu san komai nashi ba,bai damu ba,saboda duk Abunda masu Uban zasu takama dashi,toshi ma zaiyi takama dashi harma ya darasu.
Madina da mardiya dukkansu sunyi Auren nan kaduna,sai Haisam dake aiki yanzu da First banka A kano,Sunan GOGGO Yasamo asali ne,saboda su Haisam da suke kiranta da hakan,sakamakon ita din kanwar mahaifinsu ce,sai Shima Aliyun yake cemata haka,har sunan ya bita kowa Goggo,Aliyu mata basa gabansa domin da suna gabansa da tuni ya lalace,don yana matakin farko a jami”a yake samun tayin yan”mata yasani sarai ba saboda komai suke manne masa ba,sai saboda kyansa da ajinsa,Shiyasa baya damuwa,bayajin kunya kartama mace rashin mutum agaban kowaye,Gashi da zuciya ta bala”i,baya da tsoro balle shakka Goggo ce kadai sai kawu ke iya tankwarashi in yayi irin wannan bakar zuciya,baya da bakin da zai Furtama Gaggo Rashin Sanin takamammam dangin mahaifinsa na damunsa,saboda goggo ta kasance wata uwace mai mallakama Danta komai saboda ta inganta nashi rayuwar,yawan nunamata damuwarsa tamkar butulceni agareta,shiyasa koda wasa bai taba nuna mata Abun na damunsa ba.
CAPTAIN JABIR Amini yake garesu ko nace dan”uwa,domin Tun Shigansa,NDA suka hadu,da farko In da Jabir yabiye ta halin Aliyu bazasu taba zama abokai,sakamakon Shi jabir Mutum ne,ma yawan Fara”a da sakin Fuska,uwa uba kuma ga barkwanci,sakamakon Aliyu da yake wani gim dashi Fuskarnan kullum babu alamu rahama,to sanin hali dakuma abota da Allah ya hada shikenan suka zama Aminai,tunda kowa yasan Halin kowa,Suna aiki awaje dayane Anan kaduna,Haka Shima Haisam babu ruwansa,mutum ne Shima mai fara”a Da son lbri sakamom Abokin nasu dayake wani murdadde mai iyamai sai Allah daya hallicesa.
Bayan kowani Sati uku yake zuwa gida,ganin Goggo to duk sanda yazo nan yake ganin Azeema tare da ita,duk da yana so ya tambayi wacece,ammh miskilanci da rashin son Raini yasa yake basarwa sai Goggon ne dakanta take shaidamai Diyar marigayiya Fatima ce tabe baki kawai yayi bai wani nuna wani tsausayi ba,ko yaba mganar goggon mahimmanci,itama sanin halinsa ya satakama kanta dashi,Tun ganin Farko da Azeema tayima Aliyu bayan dadewar datayi bata ganshi ba,Allah ya sakamata tsoronshi,saboda ita arayuwarta ta tsani soja,saboda yadda takejin lbrin Rashin tsausayinsu,to Ranar data ga Aliyun ma da kakinsa ne,yazo gidan Goggo fuskarnan babu Annuri kafarsa sanye cikin wannan katon takalmn nasu,wanda in suka taka ka dashi,ko baka mutu ba,sai kayi jnya mai tsawo,lokacin data ganshi ya shigo dakin goggo,itakuma tana sharemata dakin,goggo na ciki,yana dago labule suka hada ido,ai saboda tsoro batasan sadda tayada Abun sharan ba ta kwantsama ihu ba,Wata razananniyar tsawa ya dakamata yana hararanta,saboda ganin yadda take neman Raina mai,wayau shi da gidansu ya shigo ta faramai ihu,tsawan data kara firgitata ta tsorata sai ga fitsari,shar yana zubowa ta kafanta saboda tsoro,dama Azeema akwai dan banzan Tsoro kamar farar kura,Baki yarike yana kallon yadda take shatata fitsari tana kamkame jikinta,aiko karisa shigowa dakin yayi yana kwanto belt dinshi yana fadin”Bush girl yanzu zaki durkusa ki shanye kazantar dakikayi kuwa…”Yake fada yana Shirin kwanto belt Goggo ta fito tana zabgamai harara,kafin tamaida kallonta kan Azeema taga yadda take rawan sanyi saboda tsoro fada Goggo ta hau gadanga dashi kan yazo ya tsorata mata diya korashi tayi,dole ya fice yana tsaki yaso goggo tabari ya lallasa yarnyarnan,banda iskanci da samun waje kamartane zatayima mutane Fitsari a tsaye,shibaima fahimci shiya firgitata ba,to tundaga ranar Azeema take Tsoron Aliyu wanda take kira da YAYA CAPTAIN,bata yarda tadawo gidan ba,sai da yakoma,Baya zuwa gidansu,ammh yana zama wajen sana”ar baba lawal ta kayan gwari,saboda kamar kawu bala,yake kallonsa ko bakomai yaba da gudummuwa arayuwarsa duk da yanzu yadan manyanta.
AZEEZA tunda Allah yasa ta dora ido kan Aliyu,watarana sun dawo daga mkranta suka ganshi wajen babansu,Azeeza saboda kallo sai da takusa fadi,sai da Azeema ta riketa,kallonsa take bata ko kiftawa Azeema ta tambaya waye wanchan na tare da baba? Azeema ta bata amsa da cewa”La baki ganesa ba,Yaya captain ne fa,na gidan Goggo…”Aziza najin haka gabanta yafadi kardai ace dan Shegen nan ne,mara asali,ammh ko gayen yana da kyau,ya hadu,wasa wasa ranar Tunanin Aliyu bai bar Aziza tayi sukuni ba,Tun tana daukan Abun wasa hartazo ta tabbatar da cewa takamu da son Aliyu,gashi ko mgana basu tabayi ba,saboda yana ganin yarinyar yaji lbrinta bata da kunya ko kadan,shiko baya hulda da marasa kunya yanzunan yarinya tanemi rainashi sai yaci ubanta ko agefen kwalan riganshi,shiyasa koda wasa bai taba sakarmata fuska ba tasha ganinshi baknta na rawa tahau gaisheshi shiko sai yagadama ne ma zai amsa da lafiya lau,daga haka ya gimtse fuska,Wani lokacin yake kawai take tana biyema Ramatun intana zaginsa,saboda bataso ta fahimci halin datake ciki.