ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Jabir daganan bai koma gidan Aliyu ba ya Shige gida yana Fatan zaman lafiya atsakanin ma”auratan biyu,Shiko Gadanga daga lokacin daya Rumgume Azeema yaji wani Fitinannen kamshi ya ziyarceshi wanda sai da yasakashi ya lumshe ido,saboda yadda kamshin yake bin kofofun Hancinsa,Akasalance Aliyu ya isa ga Azeema ya zaunar da ita kan kujera yana bin ta da kallon yadda gabadaya ta cikwukwiya kanta jikin mayafin dake jikinta,Bai mata mgana ba, kawai sai ya samu kanshi da dukawa agabanta ya saka hannu yana jayemata mayafin yana fadin”Cire sai kiyi kukan da kyau,wannan sai ya tare miki kofar Numfashi..”Yafada kai tsaye Jin Abunda yace da kuma kokarin zare mata mayafin dayakeyine yasa ta tsaya da kukanta cak tana Sauransa jin Abunda yace ne,yasa ta sakarmai mayafin ya ida zameshi sai ga kanta ya bayyana tare da gashinta,wanda wajen zame mayafin Ribon dinta ya biyo,tuni gashinta ya bazu bisa gadon bayanta,yanayin gyaran gashin ne,yasa harta gaba ya zuraro ya rufemata ido,Galala Aliyu ke binta da kallo yana tamtamar kamar ba Azeema bace an samu saba nomba,saboda Mamaki,hannunta ya riko sai yaji wani santsi da laushi tare da wani dumi ya ratsashi Sakinta yayi da Sauri yana binta da kallon harda leka Fuskarta ganin haka ne yasa tayi mirmishi ta sanya hannu ta maida gashinta baya idonta karaf acikin na Aliyu wanda yake durkushe gabanta,baya yaja yana kallonta,itako kai ta lamgwabe Tana wani narkewa kamar wata mara lafiya,Da hannu Aliyu ya Nunata yana Fadin”Wai..Wai Az..Azeema ce? yafada bakinsa na rawa.

Mirmishi Azeema ta saki kafin tayi wani Far da ido tace”Eh Sunana Azeema buh found of correction yaya captain wannan ba Azeemar gombe bace dis one na be Azeemar kaduna,kadunan ma wacce tatare adakin mijinta yau..”Zaro ido Aliyu yayi yana bin bakin Azeema da kallo kalamanta sun basa dariya wanda baisan sadda yayi zaman yan bori agabanta ba,harda dora duka hannuwansa kan ciyarta yana dariya har saida duka hakoransa talatin da biyu suka bayyana,Azeema saboda mamaki itama shagala tayi ta kallon Aliyu saboda yadda Dariya tayi matukar yimishi kyau,nunata yakeyi yana dariya kafin ya hau tafi yana Fadin”woww..Very good Wato Ba Azeemar gombe bace ko? wannan ta kaduna ce..? gyada kai Azeema tayi tana lamgwaba kai hannu Aliyu ya mikamata yana Fadin”Congratulation Azeema..”mikamai tayi ayangance kafin tace”Thanks you..”Tafada tana matse hannunsa har sai dayaji alamun haka ajikinsa,Saurin zare hannunta tayi kafin ta dauki mayafinta ta maida tana fadin”Au na manta bakayi siyan baki ba..”kallonta kawai yake yana mamaki,shifa haryanzu bai gama tantancewa Azeema ce tadawo haka ba,mikewa yayi daga kan kujera ya zauna kusa da ita yana fadin”Au hakane fa Zeema kaduna,toh nawane bakin na siyeshi yanzu..”yafada yana lekan Fuskarta Shikanshi yana mamakin yadda ganin Azeemar ahaka take bashi wani Nishadi da Farinciki 

  

   “Ta cikin mayafin Azeema ta karya murya tana fadin”Ba da kudi nakeso ka siya baki na ba,da Abu mafi daraja nake ka siyeshi yanzu nan.”Tafada tana lankwashe murya Mirmishi Aliyu yayi kafin yace”Meye shi indai na mallakeshi ni zan baki shi yanzu..”kai tsaye tace” *ZUCIYARKA…*”…”Dam gaban Aliyu ya buga yayi kasake yana kallonta,itako tana kallon yanayinshi ta cikin mayafinta ganin yadda yayi yasa tayi Saurin cewa”karka damu in bazai Samu ba yau,zan bika bashi ko zuwa gaba zaka bani kayana,Kayi alqawari..? kallonta yake kai tsaye yana mamaki wai yaushe Azeema ta iya mgana cike da Tausasawa haka,kai gyada ya mata kafin yayi mgana ta mikamai hannunta dayasha jan lalle da baki tana fadin”mu kullah…”Hannun yabi da kallo kafin ya mikamata nashi ta sarke,lokaci daya tare da zare mayafinta ta barshi iya kafadanta,idonta ta saka anashi ayayin da Shima ita yake kallo,gabadaya wani yanayi ke fuzgarsu kuma sun kasa dauke idonsu akan juna wani Shauki na dibamsu,Azeema tayi kokari zare hannunta ammh Aliyu yaki Saima kara damke hannunta da yayi,Rausayar dakai tayi tana binsa da kallo tare da kayan jikinsa baki ta tabe kafin tace”Lalle ni Aure na ya bambamta da kowacce mace,hakama tarewata ta farko,ata biyu ma da bambamci sosai..”Tafada tana kallonshi gira yahade yana kallonta kafin yace”meyasa kikace haka?kai Tsaye tace”Saboda daren Farkon kowata amarya acikin bedroom ango ke tarar da ita,Ammh sabanin ni afalo angon nawa ya tarar dani,kuma kowacce amarya Ana siyan bakinta da kudi hannu,ammh nawa bakin abashi aka Siyeshi,abu na karshe kowanni ango yana Shigowa dakin Amaryarsa sanye da Manyan kaya harda babban Riga hannunsa kuma dauke da kayan ciye ciye,ammh sabanin nawa ango sanye da kakin Sojoji n….”Dariyan Da gadanga keyi ne ta dakatar da Azeema da mganarta,ta kuramata ido tana kallonsa Shiko gira ya dage mata kafin yace”Matar Soja kenan,komai Nasu na dabam ne,buh dont worry indai manyan kayane bari naje na sauya, mganar kayan ciye ciye kuma mai z

azaki ci,yanzu zanyi waya akawomiki,Tunda na lura wannan Azeemar ta kaduna da gaske takeyi..”Yar dariya Azeema tayi cike da Aji tace tana mikewa”Lala,Ai kuma indai yayi kwantai to sai da kowa ya hakura ni ban cika cin mike ba..”Tafada tana Fadawa bedroom da kallo Aliyu ya bita yana mamkin Azeemar gabadayanta.

  Tana Shiga bedroom din tayi Saurin Fadawa wanka Umarnin Anty madina ne,ta dade a tiolet din tana wanke lungu da sako na jikinta kafin ta fito,har ta fito Aliyu bai Shigo ba,ammh taji motsinshi afalo,a gurguje ta Shafa manta mai hade da Turaranka kamshi ta bulbule kowani lungu da sako na jikinta kafin ta dauki rigar barcin da Anty madina ta fito mata dashi,Farace mai budewa ta gaba botir daya ne ya rike gaban Rigan,Kuma gabadayanta Rigan Net ne,harta da kalan pant din data sanya fari ana Hangansa,hakama farar bra ce ajikinta gashin ta ta taje ta daureshi band,Kan dressing mirror ta isa inda Anty madina ta jera mata Kayan kwalliyanta nan taci karo da wani kwalbar Turare yar karama ta dagashi ta duba,hartazata ijiye sai kamshin shi ya Rinjayeta,tana kokarin budewa ya subuce yafadi ahannunta rabi duk ya baremata ajiki wani kuma asaman madubin,Haushi yakamata sai ta rufe Turaren kawai,tasa hannu ta dinga Shafo na saman madubin ta gogawa ajikinta,Ammh kan kace kwabo Kamshi ya bude dakin tana tsaye taji kamar motsin taba kofa ai da hanzari taja hijabin data Fito dashi ta saka takoma bakin gado tana raba ido.. 

.  

Yana Shigowa dakin yayi Turus yana binta da kallo,bata kalleshi ba,sai ma kwanciya datayi gefen gadon tana kara cikwikwaya kanta cikin hijab din,Hannuwansa duka suna Aljihunsa yace”Nan fa dakina ne? ya”akayi suka ijiyeki ciki..? bata dago ba tace”Mganar da gyara yaya captain ba Dakina zakace ba,nan Dakinmu ne zakace.”Kallonta yake kawai baice komai ba karisa shigowa dakin yayi hancinsa na Shakan wani kamshi mai dadi da sanyaya jiki,bai mata mgana ba ya fada tiolet,achan ya cire kayan Jikinsa yayo wanka da zai Fito ya fito Daure da towel babban Akugunsa karami kuma yana goge kansa dashi,tana ganin ya iso gaban madubin tayi Saurin Rintse ido kamar tana barci tana jinshi yana ta kaida kawo Ashe shiryawa yayi ya sanya kayan barcinsa,pjm masu ruwan toka masu Taushi,dama ya Dauro alwala ya shimfida darduma ya tada sallah Sai da yayi shafa”i da wuturi kafin yazo ya nemi makwanci,gefenta ya kwanta yana Sakin ajiyar zuciya saboda yadda kamshin na Azeema ke neman Rikitamai lissafi,itako tun tana jinsa har barci yayi awon gaba da ita saboda gajiya,Yana kwance ammh gabadaya kasala ya Rufeshi tun yana daurewa har baisan sadda yaja jiki ya isa ga Azeema ba,ya Rumgumota ta baya ya tusa kanshi jikin wuyanta Kamshin yana rikitashi sosai,shiyasa bai san sadda yasa hannu yana Shafa Fuskarta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button