ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Kallon goggo yayi yana fadin”goggo yau wlh zanyi kisa a anguwan nan,ki matsamin daga hanya don Allah..”Yafada idanunsa sun chanza launi saboda Fitina ga naman jikinsa na cida,gabadaya Fuskar gadanga ta canza baya goggo taja tana kiran Sunan Allah da hanzari ya fice,ai da gudun hanzari goggo ta rufamai baya tana fadin”Kai kai..gadanga don Allah kadawo ka rufamin Asiri don Darajan ma’aiki..”Take fada tana binshi ko hijabi bata dashi taga ya shige gidansu Azeema ai da gudu ta maramai baya Hartana hardewa zata fadi saboda tashin hankali.
Inna Ramatu ta fito daga bayi kenan Aliyu ya fado gidan da bindiga tsirara,yana ganin inna ramatu ya nufeta ya Nunata da bindiga yana fadin”ina Yarki…? yafada cikin Tsawa,sandarewa Inna tayi saboda razana butar dake hannunta ta subuce ta fadi miyan bakinta ya kafe tana kallon Fuskar gadanga ga bindiga tana gani tsirara,wanda bata taba gani ba,sai afina finan indiya,ai batasan sadda fitsarin dabatasan yaushe yazoba, taji yana bin kafafunta kara dakamata tsawa yayi yana fadin”ina Azeeza..Nace ina Azeeza..? da ido Inna Ramatu ta nunamai Azeeza data fito daga daki jin muryan Gadanga cikin Fushi,ai yana ganinta yajuya kanta ya sakamata bindigan bisa goshinta kafin yace”Oy kneel down..”yafada yana zare mata ido,dai dai lokacin da goggo ta shigo ta haki tana fadin”bari gadanga don Allah Allurar taka tayi hakuri tabari in kakoma chan barikin ku sai tatashi kayi duk Abunda zakayi,ammh don Allah ka ijiye bindigarnan..”Take fada tana rokonsa ammh ina ko jinta bayayi itako inna dukewa tayi domin zawo da Fitsari ne suke biyo kafafunta saboda Tsoro Fuskarta kuwa ta jike sharkaf da hawaye saboda tsoron gadanga da Abunda ke hannunsa.
Azeeza dataga bindiga tsirara sai ta tsorata da hanzari tasaka gwiwanta akasa tana raba ido,Kara saitata yayi yana fadin”Duk Abunda na tambayeki juz answer me,and kuma wlh tell me d truth in ba haka i swear sai na hade kwakwalwar kanki da wannan garun..'” yafada yana kallonta baya Azeeza taja bakinta narawa tama kasa mgana,Kallonta yayi kafin yace”Ina Azeema,ina kika kaita,wlh in kika budi baki kikafadamin karya sai naci ubanki kinsan nasan komai ko? da hanzari tadagamai kai alaman hakane,Baya yaja kafin yace!”gayamin ina take,ina kika kaita bayan kun baro office din principle kin bada report kan cewa zata koma gida bata da lafiya,oya tell me daganan ina kika kaita..? Tuni Azeeza ta fashe da kukan tsausayin kanta,bakinta narawa tace”Gi…gi..dan..Ba…ba Ade..”Tace bakinta na karkarwa saboda tsoro sauke bindigar yayi ya maidata aljihu kafin yace”Toh maza ku shirya muje,goggo muje gida,bari na dauko mota muje gidan baba Ade,yau din zamu ji mai wannan yarinyar take nufi damu ne..”yafada kai tsaye yana Ficewa Kada kai goggo tayi kafin tace”Lalle karka raina mutum,Azeeza al”amarinki akwai ban Tsoro aciki,tana gama fadar haka ta fice,suna fita Inna ta rarrafo ta isa ga Azeeza tana fadin”Allah ya isa tsakanina dake,ban miki kashedi kan ki Fita harkan Azeema ba,ai gashinan kin jawoma kanki masifa kuma kin jawo mana..”Take fada tana Share kwallah,Kallonta Azeeza tayi kafin tace”Ni ba hanyar Azeema na Shiga ba inna Abun kaunata da muradina nake kokarin kwatoshi daga hannunta yazama nawa nikadai..”Tafada tana nuna kanta,Cikin mamaki inna Ramatu tace”Abun kaunarki kuma? ke Azeeza ko ganin bindigarnan ne ta saki kikafara zauncewa..? dariyan yake Azeeza tayi ba alamar nadama Aranta tace’Eh da gaske nake inna duk Abunda kika ga inayi,toh ba don kowa nake ba Sai don my Crush YAYA CAPTAIN..ina matukar sonshi Tun ina yar shekara shabiyu aduniya..'”
Baya inna taja tana dafe kirji saboda yadda kalmar ta girgizata bata samu zarafin mgana ba,goggo ta Shigo da hijabinta tace”maza Azeeza taso muje yau karyanki takare insha Allahu,har ita Azeemar zata fahimci ko ke wacece..’ko dar Azeeza batajiba, tashiga daki ta dauko mayafi ta fito tana fadin”muje dama na Shiryama zuwan wannan Ranar da Sirrin boye zai Fito sarari..”Tafada tanayin gaba,goggo ta take mata baya,ai da gudu Inna Ramatu tabisu har waje agaban idonta goggo tatura Azeeza abayan motan gadanga itakuma ta Shiga gaba yaja da gudu suka bar layin zuwa gidan Baba Ade.
_______________
Itako Azeema koda taje gidan Baba Ade banda gaisuwa babu Abunda ya shiga tsakaninsu Baba Ade tayi tambayan Duniyan tayimata banza,tacemata lafiya bataje mkranta ba tazo nan,kuma ta ganta da uniform,goggon nata tasan zata zo nan din? ammh Azeema tayi mata banza daga karshe baba Ade ta zuramata ido,sai taga Rana tayi sanyi ne kana ta farama Azeemar fada kan tatashi tatafi gida kada anemeta ammh Abunda yabata mamaki sai cewar Da Azeema tayi bazata kara komawa gidan goggo ba,ita anan zata zauna,da Baba Ade tanemi jin dalili sai Azeema ta sakamata kuka harda shessheka,saboda mamaki ma takasa mgana,Abun ya dauremata kai ba kadan,Aranta kudiri niyyar tana gama Tuwon dare zata Fice zuwan gidan goggo taji ba”asin Abunda yafaru.
Fitowarta kenan daga madafi taji sallamar goggo tana amsawa bayanta gadanga ne sai Azeeza data biyo baya kamar munafuka baki Baba Ade ta rike tana musu maraba da hanzari ta bude musu tabarman dake nade akofar dakin tana fadin”maraban ku Suwaiba,daman nima yanzu nake Shirin zuwa wajenku,maraban ku,ashe harda megida,ko daman dalilinkane Sakaryachan tayo muku yaji harda kukan bazata koma ba..”Kallonta kawai Aliyu yayi kafin yace”Baba ina Azeemar..? Yafada cikin kakkausan muryan Kallonsa Baba Ade tayi kafin tace”Lafiya kuwa tana ciki,?Azeema..”Tashiga kwalamata kira.
Itako Azeema Tun Shigowarsu taji tuni gabanta yaketa Faduwa bata kara tsorata ba,sai da taji Mganar yaya captain cikin Fushi,bayan kofa ta makale tanaji baba Ade na kiranta tayi mata banza takawa yayi zuwa kofar dakin yana fadin”Barta Baba bazata Fito ba,kila sai na Shiga na Fito da ita..’Ai Azeema najin haka tayi Wuf ta fito tana raba ido,ganin goggo yasa jikinta yayi sanyi,bata kara tsorata ba,sai dataga Azeeza agefe idanunta sunyi jawur alamun tasha kuka,gefe kuma ga yaya captain sai wani banzan kallo yake jefamata baya taja tana Shirin komawa daki,taku daya yayi zuwa biyu ya cafkota kai tsaye gaban goggo ya durkusheta yana fadin”Tambayeta goggo meyasa ta aikata Abunda ta aikata,don ni in kuka barni da ita wlh zan iya Sumar da ita da duka saboda yadda takebani haushi..”Yafada yana jaddada Abunda yafada din.
Baba Ade ta dunkuremata kai tana fadin”ai yanzu kya bude baki kiyi mgana tunda ni kin rainani kin ki fadamin me akayi miki..”kuka Azeema ta fashe dashi tadago tana kallon Azeeza wacce ta kauda kai tanawani hura hanci Hannunta goggo takama tana fadin”Azeema wai meyafaru ne,tunda lokacin tashinki mkranta yayi mukaga baki dawo ba,wlh ni da gadanga bamu Huta ba,meya faru in zaki zo nan ,ai sai ki fada mu san kina nan,kada hankalinmu yatashi..”Tafada idonta ya ciko da kwallah,kallonta Azeema take kafin ta kama hannunta tajuya tana kallon Azeeza tsawa Aliyu ya dakamata yana fadin”Kimana bayanin duk Abunda yafaru,domin itadin tace yau bata ganki ba kwata kwata amkranta,alhalin kuma Areport din mkrantan yanuna tare da ita kukeje Shigar da report din zaki koma gida bakijin dadi,ko ba haka ba..?”Yafada yana kallon Azeeza sadda kai tayi batayi mgana,ba mamaki yakama Azeema bakinta na Rawa tace,”A…Zeeza….,Haka mukayi dake..? Baba Ade da tashiga Rudani takara dungurema Azeema kai tana fadin”Toh mu fadamana yakukayi da ita don mai garinku..”Kai Azeema ta sadda kasa ta kwashe duk Abunda Azeeza ta fadamata tafada takara da cewa”Ita tace nazo nan,kuma ko Baba Ade tatambayeni karnacemata komai,kawai in ta matsa na Tubure nace bazan koma gidan goggo ba,bayan an kwana biyu kuma sai nadata balli,nace…Nace…”Kice me…!”? Baba Ade ta katseta cike da takaichi Hawaye suna zubomata tace”Nace ya sakeni..”