ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Azeema kuwa tunda tabaje akasa take kuka kamar Ranta zai Fita data Runtse ido Mutumin take gani da maganganun dayayimata,da sanda Aliyu ya dakamata tsawa,dataTuna haka sai ta toshe kunni tana sakin kuka,Tana nan kwance tana kuka har sai da muryanta ta Shide dakyar ta Tatashi ta Koma tiolet tayi alwala tazo tayi sallar la”asar tanayi tana kuka,Tana idarwa taji Shigowar yaya captain da hanzari ta mike ta Fito,tsakiyar Falon ta ganshi zaune ya dafe kai,Tunda daga kofar bedroom dinta ta durkushe tana kuka,Matsowa take idanuwanta na tsiyayar hawaye yana jin gunjin kukanta ammh yakasa dagowa ya kalleta saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa,Zumbur ya mike yana juyamata baya da wani irin karfi da Tsawa yace,”Kada ki kuskura kizo kusa dani..Azeema kin cuceni kin ha”inceni,kin kuma cucu aurenki da Yardan da mahaifinki da mahaifiyata sukayimiki,Dame na rage?,meye bana miki,?na baki abinci na baki lokacina nabaki kulawata kai hatta da soyayyata na baki Azeema why”!Why Azeema meyasa kika zabi ki cutar da zuciyata da Abunda zai kasheni har lahira.ehe..Why..? yafada muryansa Tafara rawa.
Juyowa yayi yana kallonta,Yake fadin”Sai dai, kuma bani kadai kika cuta ba Azeema harda kanki domin bazan cigaba da zama dake ba,domin zamanki tare dani watarana zan iya shakeki ki mutu saboda bakinciki gwara na tattaraki na maidama mahaifinki ke,ngda da sakayyah Azeema ngd da yardan dana baki kika cutar da zuciyata Allah nagani bantaba zina ba,kuma…Kuma Ni banta sha’awarta ba,Sai dai in shegentakan da”ake kirana dashi,shine yake bibiyar Rayuwata..”Yafada yana Runtse ido,Dakyar da sodin goshi sililin hawaye ya zubomai guda daya,Azeema da gabadaya hijabinta ya jike da hawaye ta rarrafa da gudu zuwa kafan yaya Captain takama da hannun bibbiyu tana fadin”A”a..A”a kada kayi haka..Wlh tallahi banda masaniya Akan komai,wlh ban..Ban san komai ba don Allah ka tsaya ka bincika don Darajan ma’aiki..”Take fada tana wani Gunjin kuka.
Tsaye yayi yana jin yadda zuciyarsa na Tafasa,Kafa yasa ya shureta tatafi ta bugu da kujera,center table din dake gabansa ya Saka kafa ya buga sai da ya rabe gida biyu,kallonta yayi yana fadin”Saboda haka ki tashi yanzu ki hada duka kayanki,duka nace banison ganin ko Silin gashinki agidan nan,Gobe zan maidake gombe domin Zuciyata bata da karfin gwiwan Sake zama dake..”Daga haka ya shuru kafa yafada daya bedroom din yana huci.
Hannu Azeema ta dora akai tana kuka tana fadin”Innlillahi…Na shiga uku,waye yayimin wannan kazafin,wlh kowaye bazan taba yafemai ba Har Duniya ta nade..”Take Fada tana kuka,kafin tatashi da gudu tashige daki,tafada bisa gado tana ihu tana buga kanta jikin katifa babu mai lallashinta,Shiko Aliyu tunda ya Shiga bedroom din yafada Tiolet ya sakarma kanshi Shower yana sakin ajiyar zuciya.
________________
Dai dai wajen anguwan Rimi bus stop ta saukeshi Ta damkamai wani Abu abakar leda tana Fadin”Mungode,in wani aikin yataso zamu nemeka,and don’t forget ka lura Sosai inajin tsoron ganin Fuskarka dayayi..”Mirmishi yayi yana rike ledan dakyau yace”Bafa ki da mtsala Hajiya aikina ne nasaba..”Kada kai kawai tayi kafin taja motarta tayi cikin Anguwan Rimi.
Wani Mamaken gida naga tazuba hon megadi yazo ya budemata get ta Sulala ciki,aparking space ta faka motar kafin ta Fito ta nufi cikin gidan,tana Tafe tana cilla key din motar sama cike da Nishadi,ababban Falom gidan ta cikaro da Kanwar mom din nata ita da yaranta,da gudu suka tashi suna mata oyoyo,itama ta rumgumesu tana dariya,dakyar sula barta ta kariso Falon,tana fadin”Mommy kinga Ya”yana zasu kada ni ko? wacce aka kira da mommy na kallah yar matashiyace,wacce bazata wuce Shekara 40 ba,Kallonta tayi kafin tace”Wai ina kika je ne muneera..? Juya idonta tayi kafin tace”Anguwan Sarki naje,gidan wata Friend dina Seeyama,wacce mukayi Sch tare da ita..”Gyada kai kawai matar tayi kafin ta juya ta Nufi hanyar kichen tana fadin”Allah yasa da gaske ne…”Rantsuwar karya Muneera tafara jeromata da hanzari ta dakatar da ita tana fadin”Nifa ba Rantsuwa na tambayeki ba,kawai cewa nayi Allah sa da gaske ne..”Da kallo muneera ta bita tana Tura baki,kafin taja jakarta ta haura sama,tana kunkuni.
Tana Shiga dakin,wayarta ta dauki kara,sai da tazauna bakin gadon ne,ta cirota cikin jaka ta duba ganin mai kiran ne yasa tayi mirmishi ta daga tana Fadin”Sweetheart komai ya tafi kan Tsari harma na sallame gayen..”Dariyan jin dadi Ni”ima tayi kafin tace”Job weldon Sweetheart..Yanzu yaushe zaki dawo mukoma wajen yarinyar…? ajiyar zuciya Muneera ta sauke tana fadin”Gobe insha Allahu,buh wani hanzari ba gudu ba,ita yarinya bafa musan inda zamu sameta ba,kuma bazamu yi Saurin zuwa mujira ko nan da Sati dayane,muga shin aikinmu yayi duk da ina da tabbacin ko ta kwana Akaduna yau,toh ina tabbatar miki gobe a gidan Ubanta zata kwana…”Dariya Ni”ima tayi kafin tace”Kema mganarki Abar dubawa ce,Shikenan sai kin dawon,mganar yarinyar kuma ai bamu da mtsala tafadamama Sunanta,na tabbata in anan area take zamu sameta..”Muneera tace”Ok sai munyi waya..”Daga haka suka yanke kiran zuciyarsu cike da samun Nasara.
*******************
“”Koda garin Allah ya waye yadda Aliyu yaga Rana haka yaga dare,Ballatana Azeema data kwana kuka durkushe bisa sujjadarta tana kaima Allah kukanta,ada bata taba Tsorata da al”amarin Azeeza ba koda Abunda yafaru abaya,bata tsorata da Abun ba,sai da Abunda yafaru jiya ya Faru,nan ta yarda duk wanda yayi mata wannan sharhi ta tabbata baya kaunarta,kuma bazai taba Sonta,ba ta yarda ta amince bata da wata mafita domin Anrigaya da ansha Shiryamata Ta yarda bata da yadda zata Fidda kanta.
Kokafin Gare ya waye Fuskarta ta kumbura saboda kuka,idanuwanta kuwa sunchanza kala saboda kuka da Tashin hankali,Shiko Aliyu Tunda ya Shiga dayan bedroom din nan ko motsinshi bataji ba,ta nan zaune bisa darduma bayan ta idar da sallar Asuba,tana addu”a tana kuka,karfe bakwai na safe taji bude kofar bedroom din da Aliyu ke ciki,bata fargaba taji Shigowarshi dakin bai ko kalli inda take ba,ya Furta cikin kakkausan murya..”Ki Fito mu tafi malama..”Yafada kafin ya juya zai Fita,jin ta Fashe da kuka ne,yasa ya dakata yana jin wani Abu na mai daci aransa,Kallonta yayi ta gefen ido kafin yace”Bake ya kamata kiyi kuka ba,nine yakamata na koka,don ni kika zalunta,ammh wannan kukan dakike sai ki dinga nuna Cewa ke aka zalunta..”Daga Haka yafice daga dakin yana jin kamar ya kwanta akasa yayi ta kuka.
Azeema na kuka,ta mike daga ita sai Rigar barci wata doguwa Fara mai Ratsin pink ajikinta,Wani dogon hijabinta ke jikinta wanda take sallah dashi,Akwatunanta dake kan gado ta Shiga saukewa akasa tana kuka,dama tun jiya tahada komai nata,Daukan akwatunan tayi daya bayan daya tana kaisu Falo,harda da kayan kwalliyanta babu abunda tabari,ta kwashe komai nata kamar yadda yace,Dan kit din dake hannunta Shine na karshe ta juya tana ma dakin kallon karshe kafin ta kada kai Tafito tana zubar kwallah,koda Tafito babu Aliyu afalon,kamar da Farko data ganshi tsaye,sabanin yanzu sai wani Soja tagani yanata jiddan akwatunanta zuwa waje,kasake tayi tana share kwallah kafin tabi bayanshi zuwa waje.