ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Ummah tana kiran Madina awaya ta labarta mata komai tace”ga Azeemar nan Direba zai kawota,komai suke bukata kawai tayi mata waya,kuma karta sake ya fadama Captain ga Abunda suka shirya ko yakirata tacemai Taje mata kwana biyu”Cikin jin dadi Madina ta amsa ma Ummah suka rabu akan sai Azeemar tazo,suna gama wayar ta sauko ta shiga dakin da’a ka sauke su Azeema ta tarar da ita tsaye goggo na musu bayani,ganin haka yasa tace”Na shirya..? goggo tace “Eh..”Shiga dakin Ummah tayi ta dauko akwatin Azeema tana fadin”Wannan ne akwatun ta ko? amsa goggo ta bata,hanyar Ficewa tayi kafin ta riko hannu Azeema tana Fadin”Zo muje diyata direba na jiranki awaje..”albarka baba Ade tayi ta sakama Ummah,itako Azeema bata wani damu ba saboda jin ance gidan Anty madina,tana santa tana da kirki gashi tana matukar son yaranta yan biyu mata,Hibba da Hidaya,Yarane masu Shiga rai,in suka zo gidan goggo ta dinga hidima dasu kenan,kusan mai da wawa,nan da nan Azeema ta shiga ranta sosai,har alhere suna mata ita da Anty mardiya.

  Ummah ita tafita da Azeema har haraban gidan indan Direba ke jiranta,bata tare da bata lokaci ba,ta bude gidan baya na motar Venza2k19,tare da kayanta tana fadin”Toh diyata ki natsu kinji,ki kuma maida hankali wajen koyon Duk Abunda madina zata koya miki kinji ko? kai Azeema tagyada tana fadin,”Insha Allahu Ummah..”Rufe mata murfin motan Ummah Tayi tana fadin”Allah yayi miki albarka Sai munyi waya kenan ko? kai Azeema ta gyada mata kan Direba yaja mota su danna hon megadi ya wangale get suka Fice da gudu,Azeema tabi gidan da kallo tana jinjina kyau da tsari irin na gidan kawu bala.

  Bisa hanya haka Azeema ta saki baki da hanci tana karema Kaduna kallo,ashe haka take kyau da tsari,gidaje kerarru sai wanda yagani,Nan da nan Abun ya Shiga burgeta ko”ina suka wuce sai wasu classic mata take gani kowacce na harkan gabanta,wasu su suke tuka kansu cike da ilimi da wayewa,wasu kuma Direba ke tukasu suma din cike da wayewa,lokaci daya Azeema tagane Kaduna ba na zaman irinsu bane,don in baka da wayewa tuni za”ayi baka,nam da nan ta kudirta aranta zata cire komai takoyo duk Abunda aka koyamata domin nan Duniya bata wanda yafiyemata Yaya captain da goggo da Ahalinta,babanta kadai gareta,shikuma baida wani iko akanta inna Ramatu kuma bata da wacce ta tsana sama da ita,ga yar”uwanta kwaya daya datake kallo taji Sanyi Azeeza da bakinta ta Furta bata da wata makiyiya kamarta,Tundaga lokacin ta farka daga Nanannauyan barcin daya kwasheta Ta fahimci mutanen datake kokarin yima butulci sune nata ba wasu ba.

  Gidan Madina yana anguwar Sarki ne,mijinta Controller ne,yana lagos yana aiki,Suna zuwa mamaken get din gidan suka zuba hon maigadi ya budemusu,suka rankaya cikin gidan,Madina na haraban gidan da kanta tazo taran Azeema,tunda ummah ta sake kiranta ta Fadamata Azeemar na bisa hanya,tana sanye da wani leshi mai Ruwan hot,ta karya daurin Zahra buhari,fuskarta dauke da simple makeup kallo daya zakamata kasan yes ta amsa sunanta na mace,domin madina macece mai wayewa da sanin duniya,shiyasa Mijinta Ahmed kallo Sauran mata yake matsayin basu san komai ba 

  Da hanzari ta karisa ta budema Azeemar murfin motan Tana fadin”Maraba da Antyn Hibba da hidaya,yau in suka dawo mkranta zasuyi ihun murna in suka ganki..”Take fada tana mata dariya,Fitowa daga motan Azeema tayi,tana kokarin dukawa tagaisheta,tayi Saurin rikota tana fadin”Sannu da zuwa Azeema,kona ce matar yaya ko? Sunne kai Azeema tayi tana mirmishi Rikota tayi tana kwalama yar aikinta kira,tana fadamata tazo ta dauko akwatin Azeema,takai mata dakin dake kallon nasu hidaya.

   Suna Shiga babban Falon gidan sai Azeema tazama yar kauye balle da kafarta ta nutse cikin lallausan Chinese capet din dake malale afalon,Haka ta saki baki tana bin Falon da kallo,kan daya daga cikin Royal chairs din dake falon ta zaunar da ita,da kanta ta kawomata Ruwa da drinks,tasha kafin ta rakata dakin da”aka kai akwatinta,shima dakine nagani na Fada,gado da wardrope sai madubi da tiolet,shikanshi gyare tsaf,Madina ta Shiga toilet ta hadama Azeema Ruwan wanka ta fito tana fadin”Matar yaya,shiga Tiolet ki watsa Ruwa,kizo kici abinci ki kwanta ki warware gajiya kafin anjuma mu fara Aikin namu ko?”Mirmishi Azeema tayi kafin tace”Ngd Anty madina…”Itama mirmishin tamaida mata tana fadin”Ah bakomai,yayana fa zan gyaramawa,to meye namin godiya hop dai u are ready..? kunya takama Azeema sai ta Rufe fuska Ficewa madina tayi tana fadin”Wai kunyata kikeji,dankari,toh kinga kima daina Tun Wuri,don kunni zaki bude ki kwashi lacra yarinya..”Ta fice tare ds jawo mata kofa,Hijabinta ta cire tana bin dakin da kallo,kafin ta fada tiolet din,chan ma bakauya ta zama ashe bayin gidan goggo bakomai bane,akan wannam,dakyar dai Azeema tayi,wanka,ammh kusan Rabin wanka duk takareshine wajen kallon kanta amadubi,kafin ta fito,tana Fitowa daga Anty madina adakin tana Bude mata wani lotion tana ganinta tace”Yauwa kinfito,ga mai kishafa,bari na dauko miki wasu kayan ki chanza,ki Fara daukan karatunmu Tun yanzu kowani wanka to danashi sabon salon Dreesing din,kinji ko?gyada kai Azeema tayi kafin ta karisa Fitowa,jikinta dauke da kayan jikinta data Shiga dasu,Akwatinta dora bisa gado ta bude ta zazzage kayan ciki,tsaki taja tana daga kayan tace”Gaskiya muna bukatar kudi,domin chanjin kayanki,Lalle ne su goggo nan toh da Nufinsu da wannan kayan da zaki gidan miji,bari na kira Ummah yanzu sakawanan kila anjuma mu fita kasuwa ki zabi kayansawa,daganan mu biya ki wanke kanki ko? gyada mata kai Azeema tayi tana ansam doguwar rigar abayar da Anty madina ke mikamata,ficewa tayi da hanzari Dakinta takoma ta dauki waya ta kira Ummah.

Ummah na tare da kawu bala,kiran Madina ya Shigo mata cike da zumudi ta dauka tana Fadin”Makka da madina ya akayi ne? Tura baki Madina tayi kafin tace”Toh ku Ummah kuna nufin haka zaku kai diyar taku babu kayan kirki,yanzu na bude akwatinta wlh babu kayan kwalliya na mata ko kadan..”Ummah tace”Topha to yanzu yaza’ayi Hajiya madina..”Madina tace”Kudi muke bukata Ummah,da zan Shiga kasuwa nayi mata siyayyah,sai sauran kayan gyaran da zan Hada mata,da wanda zatayi amfani dashi anan harda wanda zata tafi dashi”Ummah ta jinjina kai tace”Ok tom ba damuwa bari nayi miki Transfer din 2 hundred Thousand yanzu ai zasu isa ko? Madina tace”In ma basu isa ba,Ummah zan yi ciko,ai Matar yaya ne,so antytin for him aie..”Tafada tana dariya,kashe wayar Ummah tayi tana fadin'”Allah ya Shiryeki Madina..”Kawu na gefe yace”Harda uwar Madinar itama Allah ya Shiryata..”Dariya Ummah ta kece dashi batayi mgana ba.

  Kawu yace”Naji ana mganar kudi ne,babu bukatar taimako na..”girgiza kai Ummah tayi tana Fadin”Babu bukatar Taimakon yallabai anan,kai kagama naka,Tunda ka biya sadaki kuma ka karbo Auren,barmu da Sauran mu makarisa Abunmu..”Gyada kai yayi yana fadin’Hakane..”Tace”Eh mana..”Maida kansa yayi kan kujera yayi yana fadin”Allah bada sa”a ammh a sassautama Dana don Allah..”Wani kallo Ummah tayi kafin tace”Toh yallabai…”Tafada tana dariya Shima yar dariya yakeyi,nan take tama Madina Tranafer din kudin datace,kawu bai damu ba domin yasan halin Umaima indai tana dashi toh babu Abunda bazata iyayimai ba,balle ma ita Aliyu tamkar uwa da Danta ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button