ALIYU GADANGA Page 21 to 30

*Chapter 18*
“””Koda garin Allah ya waye,Kafin Anty madina tagama Shirya yara zuwa mkranta Tuni Azeema hartayi wanka,takumayi Turaren Tsugunnonta,takuma sha mganungunanta wanda Anty madina ta nunnuna mata,koda Anty madina ta Shigo Azeema ta cakare,cikin Wata Atamfa mai blue da ja,cikin wanda goggo ta dinkamatane,simple make up ne Afuskarta,ta taje gashinta tayi baya dashi ta saka band ta daure,tsaye take gaban madubi tana cikiniyar Daura dan kwallin Anty madina ta Shigo kallonta tayi tana rike baki kafin tace
“Matar yaya,Allah kinyi kyau kinganki kuwa chanchadi..”Tafada tana dariya Rufe Fuska Azeema tayi kafin tace”Ina kwana Anty madina..”Ta amsa da lafiya kalau matar yaya,yakika tashi..? tafada tana karisawa kusa da ita ta karbi dankwalin tana fadin”Laccan Mu ta farko zata Fara daga Dauran dankwaline,Tunda Shi na tarar kinayi..”Gyada kai Azeema tayi tana kallon yadda ta dankwasa dankwalinta,Kafin ta Dauramata bisa kai,Daurin Maryam babangida tana yi tana mata bayanin yadda zatayi bayan tagama sai tace ta kwance ta daura da kanta,nan da nan kuwa ta aza abinta yayi kyau sosai Tafi Anty madina tayi mata tana fadin!Good matar yaya da alamun, dai zaki Saurin dauke komai,yanzu taho muje mufara dora karatunmu lokaci na kurewa..”Tafada tana jan hannunta zuwa kan gadon,tsakiyar gadon madina ta hau tana fadin”Hayo nan matar yaya..!Hayowa Azeema tayi suka zauna Suna Fuskantar juna bayan Dukkansu sun tankwashe kafafunsu Riko hannunta Madina tayi kafin tafara da cewa.
“”Abu na farko kafin mufara dora karatunmu yakamata kifara sanin menene Aure,Aure dai wani Nau”i ne na bauta,gabadayanshi bauta ne na ubangiji,kuma duk Abunda akace Bautane na ubangiji toh sai fa mutum ya dage kuma ya zage damtse,Abubuwa guda biyu da suka kasance ginshikin bauta ma Aure sune LADABI DA BIYAYYAH..Matukar kinaso,kiyi bautar Aure,sai kin kasance,kina da ladabi da biyayyag,kibi mijinki Sau da kafa,yi nayi bari na bari,kiyi amfani da Umarninsa kiyi hani da Abunda yahanki,karki tsallake Umarninsa ko alama,ki kuma bisa don yana gaba dake,tsakaninki dashi tamkar tazaran kasa da Sama ne,Aljannarki,tana karkashin digadigin sane,sai yalamuncemiki zaki Shiga Aljannah,Abubuwa masu muhimmancin dayakamata kisani bayan Ladabi da biyayyah wanda suka kasance ginshikin,ki kasance mai HAKURI.. Hakuri wani babban Tsani ne,Azeema matukar babu hakuri Da juna Da Auren mutane dadama ya mutu acikin Duniyan nan,domin ko harshe da hakori,suna sabawa balle zaman mutum da mutum,Namiji yana son agirmamasa sosai balle ke mijinki yana da son abashi girma bayason Raini ko kadan,kuma yana da isa da takama,toh dole sai kin zama mai hakuri domin zaki dinga ganin yana yi miki komai cikin isa,duk da ya isan ne,domin Shi Shugabane gareki,ki ka sance mai kauda kai,banda yawan korafi kigani kikigani kiji kuma kikiji,Toh in kikayi haka Aurenki zai zauna lafiya kuma zaku Fahimci juna Sosai,abu nagaba danikeson fadamiki,Shine Kisance mace Tagari wacce take maida damuwar mijinta nata,Farincikinshi shima naki ne,ki kasance kina kokarin rike Sirrrinki dana mijinki,domin bayyanar da Sirrinki ga kowa,koda ga goggo ne,ko kakarki ke ko ni kaina,in bawani abu bane wanda yazama dole sai iyaye sun Shiga ba,Shima din ki bari sai dai in Shi yafara furtawa,yin hakan ba karamin karama mace daraja yakeyi ba,kinga duk sanda Namijin yasan baki da Sirri shikenan ya ranmiki Daga ranar zai Fara kokarin Rike Sirrinshi bazai taba bari ki sani ba,Ki sance mai yawan Fara”a ga mijinki Azeema,karki bari ko alama ya zauna cikin Damuwa kiyi amfani da baiwarki ta diya mace ki hillaceshi har ya manta damuwarshi,ki sance mai ba mijinki shawara,ta wajen aiki ne,na game da yan”uwanshi ne,ke nakomai ma,ki zama mace jaruma wacce zata dinga karafafama mijinta gwiwa aharkan komai,kinga in kika cika wadan nan sharudan kin gama cika Sharudan zama MACE TAGARI..”Fatan kina Saurarena da kunnen basira.
Jikin Azeema daya gama yin sanyi tagyada kai tana fadin”Eh ina Sauraranki Anty madina..”gyara zama madina tayi kafin tace”good to kinga duk wannan karatun danayi miki toh matukar baki cika Wadandan Fa”idojin da zan gayamiki ba,toh duk abanza ne,domin kamar kayi wanka ne kayi kwalliyah ka koma kayi ma kanka wanka da Kasa ne,”Kallonta Azeema tayi tana Sauraren mai zata cemata Madina ta cigaba da Fadin”Fa”idojin Sune, *KWALLIYAH,GIRKI,IYA SALON MGANA,SALON KWANCIYA.*Kinga duk wanda kika saki acikin hudun nan Toh ina mai tabbatar miki kin samu nakasu”Zaro ido Azeema tayi madina tace”Yes..Matukar baki iya girki toh yakamata ki daina amsa sunanki na mace,ko baki iya kwalliyah ba,da yadda zaki dau dressing din da zaki dau hankalin megida ba,kema Sunanki Sauna,kana matukar baki iya Salon mgana ba,da yadda zaki Rikita mai gida da salon mgana na jan hankali ba,kema Sunanki sakara,uwa uba baki iya salon kwanciya balle sanin yadda zaki sarrafa maigida ta hanyar rikitashi da salolin kwanciya toh wannan Sunanki Dussa,duk matakan baya,kin gama zubar dasu,don sai wadannan sunyi kyau hasken wadanchan ke bayyana”
gyada kai Azeema tayi kafin tace”Toh Anty kimin bayaninsu daya bayan zan Fi ganewa..”Anty madina tace “Yanzu kuwa matar yaya.bari mufara da kwalliyah, girki wannan sai anjuma zamu Shiga kichen Shi pratical zamuyu kingane..”gyada kai Azeema tayi kafin Anty madina ta Furta..
*KWALLIYAH..* ita kalmar kwalliya ko ahausance sai da aka kawatata kafin Afurta,Ita mace kuma dama asanta yar kawa da kwalliyace,kwalliya kala kalace,akwai wacce akeyin wanka kawai asaka kaya Shikenan,anyi kwalliya toh ni ba ita nake Nufi ba Azeema Firstly Ki lakanci kayan da in kika saka Suna amsanki,riga da Sikat ne,ko kuwa Riga da zani ne? Doguwar rigane? ko kuwa kayan Rumgumar darling ne,ma”ana kananan kaya na zaman Falo,da inda kika karanci Kayan da sukafi fitar miki da Sirrin kyau sai ki lazimci dinka ira irensu,bayan nan kada ki dauka ance kwalliya ki zata wannan kwalliyan ta zamani ne data Fito ta hauka,ki saka Foundation ki zamo aljannah garin gyaran ido ki Rasa gira,No ba ita ba Simple make up,wacce da an kalli mace asan ta san Abunda take,kuma kallon Fuskarta zai sa agane kedin classic ce,ki shafa hodarki sai jambakinki wanda yayi daidai da kalan kayanki Shima kada ki cika,ki laziminci sanya kwalli domin Farin idon mace bai da kyan gani,ki koyi kashe dauri kala kala domin burge mijinki koyi salon Tafiya mai daukan hankali duk zan koya miki wannan,Ki sanya dan kunne da sarka ki sanya awarwaro,da Sauran kawan mata kada kibari mijinki yadinga shakan wari ajinki basai kin zama kwado wajen wanka ba,kiyi koda sau biyu Arana da wankan gaisuwan Safe da waankan barka da dawowa megida,wankan safe ta Kayanmu na hausawane Atamfa ko leshi,ko wht ever dai,da yammah kuwa english wear ne,mai wando ne mai sikat ne,sai dai wanda kika zaba duk dayane ya kasance dai koya kika gilma kamshi ke binki shiyasa duk Rinti duk wuya kada ki Rasa humra ko kiyima Turare yaji sam kada ki Fara Azeema domin kamshin na jan Hankalin Namiji zuwa gareki tare da Kara dankon kauna,sai Abu na gaba
*IYA SALON MAGANA.* Kefasan akwai dayawa matan da basu iya mgana da miji ba,wata in tana mgana da mijinta kamar tana mgana da wani kaninta ko tsaranta ba karya harshe ba Tautausawa ba girmamawa bawani karkwasa balle wani Shagwaba a”a sai dai kawai damkam dinkin kamar wata Sauna ko sakarya yakamata mata su gane harshenki yazamanto kala kala ne,ma”ana harshen da zakiyi mgana da mijinki dabam,wanda zaki amfani dashi wajen mgana da kawarki dabam,wanda zakiyi da makotanki dabam,kai kowa kinsan yadda zaki karya harshe ki iya salon mgana dashi Sai kiga kin zama mace mai aji da kima a idon Jama”a,mganar yadda zaki karya harshe wajen Miji Shine First look at me Azeema kamar ace kene Abban Hidaya muna zaune haka kamar zanyi mai wata mgana mai muhimmanci abu na Farko sai na Fara jan Hankalinsa zuwa gareni,bayan na kuramai ido na langwabe wuya gefe daya na marairaice To indai yaga kinsamai ido haka zai bar dukkan Abunda yake ya tambayeki”Noor meya faru ne?Zaki Fara rigimarki ko? ke kuma dagajin haka sai ki shagwabe Fuskarki da muryanki kice”Abban hidaya ya mganarmu Ta Ranar naji haryanzu bakace komai ba..”Ki karishe kinamai Fari da ido,toh lokaci daya zaki ga ya Rude yana tambayanki wata mgana,ke kuma sai ki kalailayeshi bisa jikinsa,domin yin nesa da Jikin miji na rage Shakuwa Shawarata gareki Jikin yaya captain yazama wajen zamanki matukar yana gida ta hakane body contact dinku zai Shaku da juna,kuma shi Namiji yanason adinga mannemai ana lafemai bisa jiki,kin Fahimta..? ajiyar Zuciya Azeema ta Sauke kafin tace”Na gane Anty madina..”ta gyda kai tana fadin”Naji dadin jin hakan yanzu bari muje gaba lokaci na Tafiya,Abu na karshe kuma wanda yafi muhimmanci Shine