ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

  Ai gabadaya goggo da Baba Ade da Ummah Suka saki baki Suna bin Azeema da kallo,madina ta mike tana fadin”Azeema tashi ki juya musu su kara ganinki da kyau..”cikin kunya Azeema ta mike tana juyawa,ai bata gama ba Ummah ta mike ta Rumgumeta Tana fadin”Job weldon makka da madina wlh kin yi aiki mai kyau Allah ya biyaki..”goggo ko fadi take”Azeema tace tadawo haka? lalle yanzu bani da shakka akanki diyata,Madina Allah yayi miki albarka kin cece aure Allah yayima Rayuwa albarka.”Haka Baba ade keta kwararama Madina da Ummah addu”a Ummah ce ta mike tace”ya kamata muyi harama kafin dare yayi ko? Madina tace”Ummah Ni da nace nida mardiya mufarayin gaba saboda gyare gyare da goge Tunda dai mace bata taba zama agidan ba,dole gidan yana bukatar gyara,in mun kammallah sai mu kiraku awaya sai ku taho da Azeemar..”Jinjina kai Ummah tayi kafin tace”Eh kuma fa kinyi mgana,to ku hanzarta sai mu mu taho daga baya..”Jin Haka yasa Madina da mardiya suka mike kowacce Ta dauki jakarta,tare da yar aikin Madina suka tafi yara kuma suka makalema Azeema sai ummah tace abarsu,direba ya kwashesu tare da akwatunan Azeema da Sauran kayanta,Koda suka isa barikin Sojojin dake babban get basu barsu sun Shiga ba,sai da madina ta kira yaya captain tace gasu abakin barrak dinsu,an hanasu Shiga,cikin lokaci Captain ya yi musu waya sai gasu madina abakin apartment din Aliyu nan suka tarar da Aliyun da jabir suna tsaye,dukkansu sanye da Fararen kaya riga da wando masu tambarin Army daga gani suna wani Training ne,da hanzari Aliyu ya isa garesu sukuma suka firfito suna gaisheshi ya amsa yana tambayansu ya yaransu,bai tsaya wani mgana ba,ya mika musu makullin gidan yana fadin”Ga key din nan,already koda kuka kirani muna kan wani aiki ne..”karba Madina Tayi cikin girmamawa,wucewa yayi Shiko Jabir ya tsaya yana gaisawa dasu yana mamakin mai ya kawosu,nan take Shaidamishi Azeema ce zata tare anan barikin,baki Jabir ya saki yana mamakin Aliyu don ko alama bai taba Fadamai ba,koda ya tambayeshi mai su Madina zasu zo suyi cewa yayi bai sani ba,Shi yakarasu har kofar gidan kafin ya juyo yabi bayan Aliyu da gudu har ya cimmai yana fadin”Sannu uban yan Sirri ko nace bakin munafiki boyen mai ake mana,toh naji Ashe zaka samu wajen hutu ne ba lbri.? ko kallonsa Aliyu bai ba harma ya cire rai da zai yi mgana sai chan yaji yace!eh taya zan gayamaka Tunda kai yaro ne,haryanzu baka girma ba,ka bari in ka kara kwari mayi wannan mganar..”baki jabir yakama yana fadin”kutumar ubanchan Ammh fa ka raina min wayau,kalli Mazantakana dakyau yasin tafi taka kwari da juriyan wahala..”Kallonsa Aliyu yayi kafin yace”Allah ko,kenan ka jaraba ka gani,”Eh na jaraba mana,..”yar dariya Aliyu yayi kafin yace”eh lalle ka lalace kenan  kana Shigo da wata ciki kenan da daddare…? kallonsa Jabir yayi yana fadin”ina kenan..? ciki gidan ka mana,kana jarabawa…? baya Jabir yaja yana Fadin”Allah ya isa da sharrin daka kullamin,ni ko Rumgume mace bantabayi ba.”kai tsaye Aliyu yace!”Toh kagani haryanzu da Sauranka yaro,Kabari ka girma ma tattauna mganar..”daga haka ya wuce yabarshi nan yana Duramai zagi harda Allah ya isanshi Abun yamai zafi,duk kwanan karfin halin dayakeyi ammh gayen chan yacemai yaro Tabdijam dole ya mike tsaye.

  Su madina Sunyi Abun da himmah,basu dauki wani lokaci ba suka tsaftace gidan gabadaya,duka bedroom din guda biyu sun lailayesu da zannuwan gado masu kyau da ban Sha”awaa,Falon kuma sun gyare komai duk da gidan bai yi kura ba Sosai,sai kichen shima suka gyarashi Suka tsaftace ko”ina suka kunna Turaren wuta nan da nan gida ya kaure da kamshi,suna gamawa suka kira Ummah sukace su taho,daman Suma Ashirye suke hijabi kadai suka bama Azeema ta sanya suka Fito suka tafi Direba ya kwashesu sai cikin barraks,Suma din sai da aka tsaidasu aka kira Aliyun da kanshi kafin su samu Shiga cikin barikin,Sai gasu har kofar apartment din Aliyu Wani soja ya kawosu,Su madina suka Fito suka taresu zuwa cikin gidan,Da kafar dama Goggo ta umarci Azeema data Shiga gidan,basu direta ko”ina ba sai bisa makeken gadon gadanga Domin ga alamu nan ya nuna dakin yake kwana,saboda wardrope din dakin cike da kayan sawanshi,yawata gidan Su goggo suka fara suna saka albarka,Itako Azeema Tuni Madina ta sakata ta hince ta fada wanka,kafin ta fito sun Fito mata da kayan da zata sanya Wani Fefa less Orange ammh light dinshi,dinkin Riga da zani,rigar half jamfa ce,ammh fa yayi kyau sosai bata Daura Dankwali ba,Sai gashinta data Daureshi da band,sai wani babban Orange din vail mai duwatsu ammh yana da Sansti sosai bisa gadon daya sha Zanin gadon alfarma,suka zaunar da ita bayan Sun Fesheta da Turaruka masu kamshi,tuni ko”ina na gidan na tashin kamshi,Madina da mardiya suna ciki suko su goggo suna Falo,Ummah takira Aliyu tace sun gama zasu tafi,ba a dau wani lokaci ba Sai gashi sun Shigo shida Jabir,wanda duk wulakancin da gadanga kemai bai hakura ba sai da ya biyoshi.

Am Srry For d Typing errors bansamu lokacin Editing ba.

         

        #Comment,share,and vote…#

       #Janafty,Aka Shakira…#

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*Wannan Shafin nakune, AISHA SULAIMAN????,Dake da AMEENA ISAH..Abokan Aiki????????Allah kara hazaka malaman mkranta,????Endless of Love Habibaties*

       *Chapter 19*

    “””Dukawa har kasa sukayi dukkansu suna gaishedasu goggo da Ummah da baba Ade,sukuma Suna amsawa cikin sakin Fuska da Annushuwa Jabir ne yace”Ashe goggo kuma Azeema zata tare,? toh Allah yabasu zaman lafiya..”Goggo ta karba da “Amin Amin Jabiru saura kai,yakamata kaima ka fito da matar aure hakanan zaman gaurancin ya kare ko..”Dariya yayi yahau Sosa kai Aliyu ne yayi caraf yace”Goggo wannan yaron kikema mganar Aure,tab ai bai isa ba tukunnah..”kafa Jabir ya sa ya tokari Aliyu yana Hararansa kafin yace kasa kasa”Sannu wanda ya isa..”dariyan mugunta Aliyu yayimai kafin yace ahankali yadda da Bawanda zaiji”Gashi kaga alamar isar tawa..”ya fada yana nunamai Dakin da yaji Surutun su madina ciki da ido,tsungulinsa Jabir yayi har sai da yasa kara yana sosa wajen,Suko Su goggo basu gabe zun zata wata mganar arziki sukeyi.

  Ummah ce tace”Toh gadanga mufa zamu yi harama..”sadda kai yayi yana fadin”Tun yanzu Ummah baku bari sai anjuma..”baki Ummah ta rike tana fadin”wane mu Rufamin Asiri yanzu ma bakajin Fadan da kawunka yake tayi ba wai meya zaunar damu haryanzu bamu dawo ba.”goggo ta karbe da cewa”Atoh da gaskiyansa muma jibi jibin nan zamu koma inda mukafi wayau..”kai tsaye Aliyu yace “Goggo ai ke kinzo kenan bazaki koma ba..”Kada kai tayi kafin tace”Toh ubana Shehu..”gabadaya dariya suka kwashe jin kalaman goggo,shiko gadanga murmusawa yayi kawai,Ummah da kanta ta Shiga ciki ta tararro Su madina tare da Azeemar suka Fito falon gabadayansu goggo ta hada tayi musu nasiha mai kashe jiki daga karshe tayima Aliyu jan hankali mai hade da gargardi akan ga Azeema nan Amanace agaresa in yaci Amanarta toh ya sani Amanar Allah zata cisa,bata da kowa sai shi sai Allah sai kuma su Ummah,wanda goggo ta dankamata amanar Azeema,ita kuma ta saka hannun bibbiyu ta amsa,Aliyu yayi alqawarin rike Azeema bisa Amana da gaskiya,koda akabama Baba Ade damar mgana kasawa tayi saboda kuka godiya taitayima goggo da gadanga kafin takoma tana sanyama Ummah albarka,Azeema ko tafadamata in ta kuskura ta sabama mijinta da gangan Allah bazai kyaleta ba,Azeema tana ta kuka,kukan Farinciki da kewan rabuwa da goggo,bata kara tsinkewa da al”amarinsu sai da suka mike zasu Tafi,nan fa Azeema tace batasan wannan zencen ba tamakale goggo tana kuka,wanda duk dauriyar goggo sai ta koka da gudu ta fito daga gidan Tana Share kwallah,Ummah ce ta umarci Aliyu daya rike Azeemar wacce ta ki sakin hannun Baba Ade,ta bayanta yaje ya Rumgumota dakyar ya bambare Hannunta ana Baba Ade,Jabir ne yatafi rakasu zuwa bakin motocinsu Sukansu su hidaya kuka suke wai sai sun zauna wajen Anty Azeema,madina na dariya ta iza keyarsu tana fadin”Kajimun yara da ballo Ruwa oya ku wuce muje gida gobe sai na saka direba yadawo daku..”kowanne amotar dayazo yakoma Mardiya daganan bata koma gida ba direban madina ya Sauketa gida ita kuma ya karisa da ita gida su kuwa su goggo suka koma gidan kawu cike da Murna tare da kewar Azeema dashi kanshi gadangan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button