BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Wata matace mai sayarda masa tagani kusa da ita taje ta zauna tambayarta matar tayi na nawa kikeso shiru tayi kadan kafin tace inna kizubamin iya daidai cikina wanda kikasan zan iya cinyewa

Dariya matar tayi tace yoh ni nasan cikinki ne yar nan

Shiru Aneesa tamata ganin Aneesa bata kulata bane yasa ta dauki roba tazuba mata na 200 tamika mata

Aneesa tasa hannu ta karba da bismilla tafara ci har tagama saidai bata iya cinyewa ba nan ta mika mata sauran dariya matar tamata kana tace toh kin gani yanzu ya kk so inyi da sauran kinga ni ba damuwata bane kawai abinda nasani shine ki biyani kudina

Aneesa taciro dari biyar tamika mata matar ta karba tana washe hakora

Aneesa tamike da niyyar barin wurin har tafara tafiya ko me ta tuno kuma oho sai ta juyo tace inna dan Allah ina zan……

Sai kuma tayi shiru matar dai dama batada niyyar kula Aneesar sai tayi kamar batamasan da mutum a wurin ba

Kujera Aneesa tasamu ta zauna jin jikinta na mata wani iri tun safe da tayi wanka har yanzu batayi ba kuma saidai ta canza pad dazu da aka tsaya a lokoja cin abinci

Amma still tana bukatar wanka tsaki taja wanda yasa matar nan kallonta saidai batace da ita komai ba

Har 10pm Aneesa na zaune matar tagama hada kayayyakinta ne tace yar nan niko in tambayeki bazaki wuce gida bane

Aneesa tace bansan kowa a garinnan ba ni bakuwa ce dan girman Allah ki taimakeni

Shiru matar tayi na dan mintoci kafin tace toh yar nan kinsanfa yanzu duniyar nan abar tsoro ce

Kana zama zamanka sai azo a goga maka tsiya abarka wasu cuta nikam ina tsoro saidai bkm Allah zai kareni

Aneesa tace inna wallahi ni ba macuciya bace ki yarda dani

Matar tace toh taso muje yar nan Aneesa tamike tsaye suka kama hanyar gidan matar wani shago matar tatsaya tasayi abinda zata saya itako Aneesa ta sayi Always matar ta kalleta irin na tuhuma saidai batace da ita uffan ba

Wani gidane matar tashiga mai dakuna 3 kacal wani daki suka nufa matar tafara shiga itama aneesar da sallamarta tashiga

Dakine mai dan girma sai bayi da kitchen wato Bed sitter

Matar ce ta zauna a saman 2seater itama aneesar zama tayi amma a kasa tanaima dakin kallo

Akwai katifa a dakin sai tv carpet ke shimfide a dakin

Dukda karamin dakine saidai ba laifi tsaf yake

Aneesa ta kalli matar data jinginar da kanta a saman kujera tace mata inna wanka nakeson yi

Bude ido matar tayi tace shiga cen tayi mata nuni da yatsarta mikewa Aneesa tayi tashige bayi ta rage kayan jikinta dama ta yi omo wanke inners nata tayi bayan tayi wanka

Ji tayi jikinta yadan mata dadi tana gamawa tafito tana smile

Acen gidansu Aneesa kuwa koda gari yawaye Aisha ce tafara neman ta saidai bata ganta ba

Dakin mom tanufa nanma shiru hankalin mom bai ko tashi ba don a tunaninta kila Aneesar ta tafi gun ashraf ne tunda su biyu2 sun kasa hkr

Abu dai kamar wasa karfe 8am mom takira wayar Ashraf take cemai ya turo Ameesar tana son ganinta tunda 9am zasu kama hanya

Saidai Ashraf cemata yayi shi tun jiya bai bayan dinner bai kuma sakata a ido ba

Hakan ba karamin dagama mom hankali yayi ba yan rakiyar Amarya duk sun shirya motoci sunyi convoy ana jiran fitowar Amarya

Sai jin ihun……………….

✍????
By Leemat

Love U All????????????

Kuyi hakuri dani masoya aiyuka ne sukamin yawa amma yau gashinan nacika maku burinku nasan jin murya ta ????????07065676724
Nima ina kaunarku ????????????????
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wannan page din na sadaukar dashine ga dukkan masoyana na nan gida nigeria dana kasashen waje Allah bar kauna ameen

A gaskiya naso na daina typin din wannan littafi bisa rashin mutuncinda wasu sukamin…..
Harga Allah naji zafin abinda akamin wanda hakan yasa na dakatar dayin typing har nake tunanin daina yin novel gabaki daya saidai kash……. Leemat jirgi nake mai masoya dayawa ………❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
masoyana sunce nayi hakuri na bar makiya da mahassada tabbas na hakura kuma inshaa Allahu zanci gaba da yima masoyana typin ina yimasu posting dinshi I care 4 u fans????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                     32

Sai jin ihun mom akayi ai dagudu aka shiga ganin mom akan Aisha sai faman kuka take tana jijjiga Aisha wacce ta fadi sumamma jin Ashraf yace shi tun jiya bai ga Aneesa ba

Yayyafamawa Aisha ruwa akayi dakyar aka samu ta farfado sai faman kiran sunar Aneesa takeyi
Shiko gogan jin shiru gashi karfe 9 saura kwata yasashi fitowa jin gabanshi tayi mummunar faduwa ne yasashi farayin addu’oi

Ai kuwa dashigarshi palo sai ganin mata yayi zazzaune sunyi jikum kamar masu zaman makoki kirjinshine ya tsananta bugawa

Binsu yayitayi da kallo daya bayan daya cen ya hango mom da Aisha a zaune sai faman sharar kuka suketayi

Wurinsu yanufa yana kaiwa nan yace mom lfy?

Mom takasa amsa mashi sai faman kukanta take mamaki yakeyi anyaa mom ce kuwa dayagama waya da ita yanzu shine take kuka kamar ba itaba

Toh ko lfy?
Meya faru kuma kara tambayarta yayi nanma shiru ganin mom batada niyyar amsa mashi ne yasashi mikewa jiki ba kwari sai tsintar muryar Aisha yayi tana fadin Uncle Ashraf Sis Aneesa ……. sis Aa…nees……. a bamu ganta ba …….

Ai salati Ashraf yayi kafin kace me jinsa yayi kafarshi ta kasa daukar shi zufa keta keto mashi tako ina

Nan danan idonshi ta fara kadawa gani yake kamar ko ina juyawa take ai kuwa nan ya zube

Yayanta ne yashigo jin hayaniyar tayi yawa ai a bakin kofar palonne yaci karo da wata mata da take kokarin fitowa dan kiran wani namijin ai dagudu yabi bayanta yana isa wurin ya tsuguna yana fadin mom lfy

Wata matace take yimashi bayanin abinda yake faruwa salati sukajiyo daga bakin kofar juyowarda zasuyi sai ganin dad sukayi shida Abban Ashraf da wasu abokan Ashraf din wanda ganin lokaci na kurewa ne yasasu shigowa dan jin ko lfy

Basu tsaya yin wata wata ba suka kinkimi Ashraf sai asibiti

Aneesa kuwa ranar barcinta tayi hankali kwance koda gari ya waye ita tayi share share da gyare gyare sannan ta taya inna aiki inna kam taji dadi sosai da yanda Aneesa taketa aikace2 ganin abin na Aneesa bana lfy bane yasa inna cewar yar nan jeki huta mana

Aneesa kuwa cewa tayi inna kibarni nakarasa inna kam taki yarda

Ashraf kam koda ya farka da salati ya farka sannan ya fara kiran sunan Aneesa yana hawaye

Rarrashin duniyar nan anyi amma kamar a banza ganin hakanne yasa dr yace saidai ayi mashi allurar barci dan gudun kar yasami matsala a zuciyarshi

Kwanansu 3 aka sallamosu Ashraf kam cewa yayi bazai koma zaria ba

Dakin Aneesa yakoma dazama kamar wani zautacce kullum bashida aikinyi sai kiran sunan Aneesa yana kuka kamar wani small boy

Bada cigiyarta akayi ako ina amma ba lbr shiru akwana atashi bawuya a wurin Allah

Yau watan Aneesa 1 da bata Ashraf kuwa har yanzu babu abinda ya canza gameda halinda yashiga

Aneesa ce zaune tayi tagumi kamar wacce aka aikoma da sakin mutuwa inna ta kalleta tace ………….

✍????by LEEMAT

Love u all masoya????????????
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Ina mai kara godiya ga Allah daya nunamin zagayowar ranar haihuwata ina mika godiya da jinjina agareku kawaye da abokan arziki da kuka tayani celebrating din birthday dina da addu’oinki gareni nagode Allah bar kauna yawane daku bazan iya rubuto sunayenku gaba daya ba nagode nagode nagode ????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button