BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA

        *NA SADNAF*

E.W.F

Bismillahi Rahamanir Raheem

Page 1

    Wai saurin me kake yi ne haka"?

Wayar sa ya Kara duba wa tare da Kara sauri Yana “Jirana ake fa karki damu yanzu zan dawo bazan dade ba yace tare da yin waje da sauri.

Da ido na bishi har ya fice daga gidan naji karar tashin lifan dinsa.

Tagumi nayi tare da bin kulolin da na ajiye a tsakiyar kafet din palon da ido,abincin daren dana dau tsawon lokaci ina yinsa duk sabida na faranta Masa duk da cikin dake jikina ina jin yunwa haka na hakura da cin abincin sabida idan ya dawo muci tare kamar yanda Muka Saba sai gashi daga dawowar sa ya sake wanka ya fice daga gidan da Sunan kawunsa na neman sa.

Kwana biyu kenan Yana min haka.

Haka na zauna raina a b’ace Ina tsaki kasa kasa ganin idan na cigaba da zama a haka batare da naci abincin ba zan cutar da kaina da abinda ke cikina yasa na zuba abincin na fara ci.

Ban wani ci da yawa ba na rufe sauran na jawo wayata na fara chatting abinda kawai zai rage min kadaici da takaicin fitar da mahfuz yayi ya barni ni kadai a gida kamar Mayya.

Mahfuz bai dawo ba sai wajen goma na dare zuwa wanan lokacin Raina ya Kai kololuwa wajen b’aci kafa kawai nake girgiza wa Koda ya shigo da sallama ciki ciki na amsa mishi,ya saki murmushi Yana “Afuwan tawan wlh wani waje na raka kawu bansan zamu dade haka ba kiyi hakuri kinji matata”

Bansan Mai yasa bana iya dogon fushi da mahfuz ba Yana min murmushi da yar murya zanji na sauko.

Ledar daya shigo da ita ya bud’e Yana “Kinga kayan kwadayin dana taho Miki dashi

A binka da mai ciki da sauri na wafci ledar ganin alewar Madara da gulisuwa yasa na washe baki dan duk wani Abu Mai Madara da siga Ina so.

Sai da na fara Shan alewar Madarar na kalli mahfuz da ya zauna a kasan kafet Yana Danna wayarsa

“Baza ka ci abincin bane?”

“Wlh kawu ya tilasta min cin abinci a gidansa sai dai gobe ki dumama min kafin na fita”

“Yanzu ko cokali daya bazaka yi ba sabida Kai na girka fa”

“Ai nace Miki gobe sai kimin dumame wlh yanzu a koshe nake”

Badan raina naso ba na cigaba da Shan alewar Madarata shi kuma ya mike kafarsa da hannu bibiyu Yana latsa wayarsa har da dan murmushinsa.

Ido na zuba Masa Ina tunanin canjawar da yayi a kwanakin nan,Mahfuz mutum ne da bai wani damu da chatting ba dan sau tari ni nake tilasta Masa yin chatting sabida Ina tura Masa sakwanin ta watsapp,ada idan ya dawo gida ko waiwayar wayarsa baya Kara yi sai dai yayi ta jana da hira Yana bani labarai idan yaga na dauko wayata sai ya kwace yace a hakura da danna wayar nan azo a ji da ni amma a kwanakin nan har da asuba Zan ga Yana latsa wayarsa ban taba zarginsa ba bana Jin Zan Kuma zarge idan na tuna San da muke yiwa juna,ba Kuma mu dade da yin auren ba tunda yanzu shekara biyu da auren mu a yanzu Allah ya azurtani da samun ciki

“Wai Mai kake yi a wayar kake ta murmushi haka”?

Dagowa yayi da sauri Yana “Da Abdul muke hira fa sai dariya yake bani kinsan halinsa da barkwanci”

Murmushi nayi nima Ina “Gwauro ba har yanzu sai ruwan ido yake ya kasa tsayar da budurwar balle mu sha biki”

Yana chatting muna hira har zuwa sha daya da rabi na dare kafin mu tafi daki mu kwanta.

Fitsarin da nake ji ne ya farkar dani sai da na wartsake na mike zaune ga mamakina mahfuz baya d’akin har Kara shafawa nayi Naga ko dai lumewa yayi a bargon da muka lulluba sai dai bargone kawai baya d’akin.

Kasa kunnena nayi naji ko dai Yana bandakin a daidai lokacin da na daga kaina Ina kallon agogo d’akin karfe biyu da minti goma Sha biyar na dare.

Mik’ewa nayi a hankali Ina mamakin Inda Mahmud yayi dan nasan baya bandaki tunda banji motsi ba.

Sai dana kunna fitilar d’akin na nufi wajen k’ofar dakin da aka dan bud’e idan har zan tab’a k’ofar ba abinda zai hana yayi Kara daga d’akin Ina Jin maganarsa hakane yasa nake so naji mai yake cewa zuciyata fal da mamaki da wa Mahfuz yake magana a tsakar daren nan ya baroni a daki ni kadai.

A hankali na samu na fito daga d’akin batare da na bari kofar tayi Kara ba, cikin sand’a na fito na nufi palon da yake akwai siririn corridor kafin a iso palon.

Hasken wayarsa kawai nake hango wa yayi rub da ciki fitilar palon a kashe.

“Nifa bana ganinki sosai wai me hakane”?

Abinda ya sauka a kunnena kenan daya bala’in fadar min da gaba har sai dana dafe cikin jikina sabida motsawar da yayi.

Ban motsa ba na tsaya Ina cigaba da Jin hirarsa da macen da nake Jin saukar muryarta a kunnena.

“Bana so na kunna haske na tashi Ameera fa Wai yanzu baka ganina”

“Rowa kawai zaki min Kisani mafarki a banza”

Dariya macen ta kyalkyale dashi Yana shirin magana bansan rike numfashina nayi ba Ina sakin numfashin yayi jifa da wayar da sauri Yana “Lubna”

Duk da jikina balain rawa yake Ina hada gumi bansan ya akayi nayi jarumtaka wajen daidaita kaina Ina “Farkawa nayi zanyi fitsari da ban ganka a d’aki ba shine na fito”

“Ooo e’e’e motsi naji a waje shine na fito naga waye har waje na fita ma”

Yace Yana in’ina ya sunkuya dan ya dauki wayarsa na juya jikina na cigaba da rawa nabi bango na koma d’akin Yana daga bayana Yana fadin Yana tunanin barayi sun adabi unguwar bance Masa komai ba na kwanta tare da Jan bargo dan har wani zazzabi naji Yana neman rufeni.

Yana kwanciya a gefena ya fara k’ok’arin jawoni idan har na hana shi rungumeni zai zargi naji maganar da yake yi da mace.

Halin da nake ciki yasa ban iya jure rungumar da yamin ba dan gani nake kamar ya manna min garwashin wuta na janye jikina banaso nayi magana sabida Zan iya fallasa halin da nake ciki bana so nayi abinda zanzo Ina nadama inaso na samu nutsuwa nayi tunani Mai kyau.

Koda na janye jikina bai Kara jawo ni ba yace tom yau bbyn bayaso a tabaki kenan ya juyamin baya tare da Jan bargo saman kansa.

Ido na zubawa bayansa Ina Jin tashin maganarsa a kunnena nifa bana ganinki sosai wai me hakane
Rowa kawai zakimin kisani mafarki a banza.

Da wa Mahfuz ke video call da tsakar daren nan har ya barni a daki ya tafi palo wacce ce ita,har yaushe Muka yi Aure da mahfuz zai fara kula Yan Mata,Anya ma mahfuz dina ne wanan ko dai mafarki nake yi na mitsini kaina wai dan na tabbatar da ba mafarki nake ba.

Zuciyata wani irin zafi yake min na tsananin kishi mahfuz dama Yana da budurwa duk soyayyar Nan da yake min dama zai iya kula wata, mahfuz makota ma sun shaida irin kaunar da yake min.

Soyayya mai tsafta muka yi a shekara uku da muka hadu dashi,naje banki zan bude acct shi kuma anan yake aiki,tun ban dauki soyayyarsa da wani mahimmanci ba har sai da ya samu matsuguni a zuciyata,ba Wanda baisani dashi ba a cikin dangina haka ma danginsa,kawayena Kan roki Allah ya basu irin Mahfuz sabida yanda baya iya b’oye san da yake min a gaban kowa, nida kawayena mun Sha hada Kai mu siyi layi dan mu gwada shi,Yana Jin muryar mace zai kashe dan kafin muyi aure Ina balain saka kaina a matan da suka yi sa’a da dace samun nagartace kamar mahfuz ban fuskanci wani matsala ba har mukayi aure zan Kuma iya shaidarsa dan ba abinda yake boye min,a gurin mahaifiyarsa Hajiya Ammi kawai nake ganin ban wani samu karbuwa ba duk da da yawa ance haka take bata fiye sakarwa sirikanta fuska ba,da na auri Mahfuz sai na fuskanci idan kina so ta sakar Miki fuska ki bata abin duniya a ranar zata sakar Miki fuska na Kuma ji halayenta a wajen matar yayyen mahfuz Inda Suka ce Kar na sake duk wani abu da zai hadani da Mahfuz nace Zan Kai kararsa wajen mahaifiyarsa tsana zan janyowa kaina dan bata san laifin yayanta ko kad’an.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button