BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Kafin ta karaso mahfuz ya daka mata wani uban tsawan daya saka ta tsayawa cak

“Karki sake ki matso kusa dani,ki fita daga rayuwata Hadeeza daga yau bani bake, matata ta isheni rayuwa ki rabu dani Hadeeza idan Kuma kika k’i duk abinda na miki ke kika jawowa kanki”

Bansan Mai yasa naji sanyi da Dadi na ratsani ba,Koda baa har zuciya MahfuZ ya fadi haka ba ya faranta min dan ya disgata a gaban katon Alhajin da tazo dashi haka ma a gaban mutane.

Ido muka hada da ita idonta ya ciciko da hawaye na sakar mata murmushi na tsinci kaina da karasawa wajen da take tsaye Ina “Idan ke din ba jaka bace Kuma karuwa mai bin mazajen mutane sai ki hakura ki daina bibiyar mijina haka banza balagaza karuwa”

So nake tayi magana na d’auke ta da mari batayi magana ba har Mahfuz yazo ya janyeni

Muka bar wajen muna fita na fusge hannuna Ina “Wlh duk kishi yasaka kayi maganar da kayi,mahfuz ni ba yarinya bace wlh kana san yarinya nan ka sakeni kawai ka aurota”

“Lubna bansan Kuma Mai kikeso na miki bayan wanan ba agaban idonki dai kina ganin kashedin dana mata duk sabida na faranta miki rai haba lubna”

Ya kuwa faranta min din banaso na nuna masa ne ban Kara ce masa komai ba har muka Isa gida.

Da isarmu gida ya ajiye ledojin da ya dan yi siyayyarsa a ciki har dasu balangu a palo ni kuwa daki na shige na canjawa Mimi Pampers na bata abincinta ta Sha ta koshi

Kafin na Shiga bandaki nayi wanka na saka kayan bacci na haye gado raina fes dan na fara yarda mahfuz dagaske yake zai rabu da Hadeeza.

Shigowarsa yasa nayi saurin lumshe idona yace “bazaki ci balangun ba”?

” A koshe.nake”

Bai Kara cemin komai ba ya fice daga d’akin ba dadewa ya dawo d’akin Ina jinsa ya rufe kofa yazo ya kwanta a gefena a hankali ya matso kusa dani yamin rada a kunne “Ina bukatar ki pls kimin wanan taimakon dan Allah”

Ban motsa ba ya juyo dani,jiki da jini Ina karbar sakonsa amma haka na kwanta kamar ruwa na d’auka yi zaiyi sai ji nayi ya dagoni idona a rufe yake Ina k’ok’arin bude Idona naji jikinsa a bakina Yana shafa kaina.

Har ga Allah abinan amai yake Sakani nayita tofe tofen yawu har garin Allah ya waye janye kaina nayi na koma na kwanta,hakane yasa ya hakura jikinsa sai rawa yake kamar Wanda tab’a sanin mace ba har ya samu nutsuwarsa naji bacci ya d’auke shi nima Ina rufe Ido bacci yayi awon gaba dani…
MG’S SKINCARE

In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,

Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?

To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,

Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,

Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,

Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg’s bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu

WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi

Page 22

        Dagani har shi makara mukayi sallah asuba sai a gida yayi sallah asuba.

Sanin zaije aiki tunda ranar Monday ne yasa ban koma bacci ba na fara k’ok’arin zuwa kitchen na sama Masa abinda zaici.

Sai dai Ina zuwa na gansa a kitchen Yana soya kwai Ido da muka hada dashi yasa ya kanne min Ido Yana “Na hutasheki farin cikina jekiyi kwanciyarki kiyi baccinki”

Ina karya Zan wuce na Kulle Miki gidan idan bazaki iya girkin rana ba Zan siya na Aiko miki dashi”

Hmm kawai nace tare da barin Kitchen din nasan duk Yana hakane dan na manta abinda yamin,nima zanso na manta din amma bansan Mai yasa nakeji kamar bazan iya sakin jikina dashi kamar a baya ba,ban koma d’aki ba na zauna a palo,ya fito daga kitchen din da plate din kwai da kofin shayi.

Ya zauna a gefena yana ci Yana min hira nidai biyesa kawai nake har ya gama ya jawoni ya Kara jagwalgwalani san ransa banda ma naki nasan karawa zaiyi ya shige daki ba dadewa ya fito a shirye Yana kamshin turare ya ajiyemin Dubu biyu a gefena Yana “bari naje kar na makara”

“A dawo lafiya”

Ya sunkuyo yamin kiss zai juya nace “Idan har ka sake cin amanata Allah ya isa ban yafe maka ba idan bana kallonka Allah na kallonka”

Murmushi yayi Yana “Mahfuz bazai ci amanarki ba mahfuz nakine ke kadai ki kwantar da hankalinki a gabanki dai jiya kina kallon irin gargadin da nayi mata”

Yarda daya ce amma ba abinda mahfuz zai cemin yanzu na yarda da Ido na bishi har ya fice daga gidan.

Na Mik’e na koma daki na kwanta bacci ya Kara awon gaba dani.

Mahfuz

      Sosai yaji shi cikin farinciki dan a yanzu yasan ya samu ya shawo Kan lubna zaiyi iya kokarinsa wajen gujewa duk wani abu da zai saka su samu sabani.

Take yaji shi cikin b’acin rai daya tuno ganin da yayiwa Hadeeza da wani jiya,tunda yake da ita bai tab’a ganinta da wani ba baisani ba ko hakane yasa jiya yaji ransa ya b’acin da ganinta da wani,Ashe karya take da tace masa bata kula kowa Ashe karya take da tace shi kadai ne saurayinta,a yanzu ya Kara tabbatar da zarginsa akan fuska biyu gareta,dama hanya yake nema da zai yakiceta,dama hanya yake nema da zai ce Mata bazai iya aurenta ba, a yanzu Kuma ya samu hanyar tunda ya ganta da wani jiya.

Sai da ya isa office ya dan kammalla wasu ayyukan kafin ya Nemo lambar Ammi ya kirata dan su gaisa,dan ba mai wanan sabon layin nasa.

Sai dai Ammi na Jin muryarsa ta rufeshi da fada tana “Wulakanci ne yasa ka kashe wayarka tun jiya nake neman layinka a kashe”

‘canja layi nayi Ammi shiyasa na kiraki da sabuwar Dan na daina amfani da wancan”

“Sabida me ka canja layin da tun kana Saurayi kake amfani dashi”?

“Haka kawai na canja layin Ammi”

“Karya kake yi kace min matarka ce ta saka ka canja layi sabida Kar mu ringa samun ka a waya mahfuz kasan dai ba ita ta haifamin Kai ba ko”Anya yarinya nan ba asirice ka tayi ba naga alama so take ta rabaka da kowa ta hanaka muamalla da kowa to wlh wanan ne bata Isa ba dan ko dawo da ita da kayi bada yawuna ba,amma tunda ka dage wlh sai ka Kara aure Ina nan akan bakana Kuma kafin na Saba maka ka mayar da layin nan da kowa yasanka dashi,ba ruwana da wanan sabon layin jibi kazo Ina san ganinka”

Kit ta kashe wayar yabi wayar da kallo,ya riga da yasan halin Ammi idan baiyi abinda tace ba kadan da aikinta tace zata maka baki, mayar da layin nan da tace yayi zai iya haddasa Masa matsala da Lubna yasan halin Hadeeza da azababben naci ko yayi blocking dinta sai ta kirashi da wani layin ba Kuma lalai duk bayanin da zai yiwa Lubna akan ita take nace Masa ba ta yarda,zancen Karin Aure Kuma da ta dage sai yayi sam bai shiryawa wani aure ba,Koda zaiyi ba yanzu ba Hadeeza ce dama ta matsa Masa yaji Yana San ya Kara auren,a yanzu Kuma bazai tab’a iya aurenta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button