BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Ciki ciki na gaida shi ya amsa da murmushi a fuskar sa Mahfuz kuwa yayi rau rau da fuska Kamar zaiyi kuka

“Lubna kiyi hakuri Mahfuz bai kyauta ba duk Wanda aka bashi hakuri ansan an cutar dashi,ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki yafe Masa wlh yayi nadama ya Kuma gane kuransa ko dan yarinyar dake tsakanin ku kiyi hakuri ba Wanda baya kuskure tunda baki tab’a kamashi da irin wanan laifin ba insha Allahu wanan shine Karo na farko Kuma shine na karshe da Zaki Kama shi da laifi irin wanan”

A dake na dago na fara magana ba tare da naji wani nauyinsa ba

“Ya Usman wlh ko mahfuz shine autan maza na gama aurensa bazan tab’a komawa gidansa ba inaga karyar da ya Saba yi mutane ya ma shiyasa baka san ainihin abinda ya faru ba bari na baka labarin abinda ya aikata kasa kanka a matsayin yayana idan kanwarka ce ni wane mataki zaka ce na d’auka.

Tiryan tiryan na kwashe komai na fada masa game da duk abinda Hadeeza ta fada min har yanda ta shawo kansa kafin ya kawota gidan da duk abinda sukayi na zayyane masa

“Idan har Mahfuz zai min haka ya zuba min magani a lemo na Sha dan yaje d’akin budurwarsa karshen cin mutunci yamin wlh Mai kaunarka bazai tab’a maka haka ba tsananin Santa da yake yasa ya kawota gidansa dan ya ringa ganinta bama zai iya Hakuri har sai an daura musu aure ba taya zan komawa Mahfuz da idona nagansa kwance a jikin ta da wane idon zai kalleni na kalleshi har ya samu matsayi a zuciyata da Sunan mijina wane irin Zama zanyi dashi, mutuncinsa ya Riga da ya zube a idona,bazan tab’a girmama shi har na iya Masa biyayyan Aure ba har yaji dadin Zama dani dan haka yaje ya auri hadeezar sa ya kawomin takarda sakina idan na yaye mimi yazo ya d’auketa”

Daga yanda Ya Usman ya kasa motsi nasan ya rasa Mai zai cemin ne hakane yasa na fara k’ok’arin mik’ewa mahfuz yayi sauri ya Sha gabana ya zube akan gwiwar sa idonsa ya Kada yayi jajjur kiriss yake jira ya saka kuka”Lubna dan Allah badan halina ba kiyi hakuri,wlh tallahi sharrin shaidan ne kema kinsan Ina balain kaunarki wlh na hadu da shaidaniyar mace ne,banyi niyyar kaita gida ba wlh Allah haka ta dagemin har ta shawo kaina”

Bayan ta maka kiss kaji tudun kirjinta a bayanka sabida kwarto ne Kai dole ta shawo kanka nifa Mahfuz da kasan irin tsanar da na maka wlh Tallahi da baka tsaya a gabana da Sunan bani hakuri ba idan har baka San tonan asirinka ka aikomin da takardata ko ka bani yanzu idan ba haka ba wlh tallahi hisba Zan Kai ka Kuma kasan naje can dole na fada musu abinda kamin dayasa nake neman takardar saki,wlh bama kada kunya mahfuz,har gidanku ka Kai Hadeeza da baka Santa zaka kaita gidanku dan ta gaida Ammi ne,duk siyayyan nan da ka ringayi Ashe duk sabida ita ne Allah ya Isa tsakanina da Kai mahfuz ka rubutamin takarda sakina idan ba Haka ba wlh jibin nan Zan Kai ka hisba suma Dole ka bani takarda ta domin bazan Kara Zama da mazinaci ba”

Na fara k’ok’arin kewaye shi na wuce dan yayansa har ya fice daga palon

Mahfuz ya rike kafata gam dan duk abinan da ake Yana tsugunne akan gwiwarsa

“Wlh bani na Kai Hadeeza gidanmu ba,ita ta Kai kanta ki yarda dani,Wlh wasu Abubuwan da ta fada Miki karyane so take ta rabamu lubna ki dubi soyayyar dake tsakanina dake ki yafemin”

Ba abinda nake sai k’ok’arin fusge kafata amma ya rik’e gam har sai da na hada Masa da duka Ina ya sakeni.

Karar bugun da nake Masa ne ya fito da mummy daga d’aki da sauri tayo wajena tana ke Mai haka ka cika ta mahfuz.

Sai a lokacin ya cika ni na kewaye shi na shige dakinmu ya hau rokon mummy akan ta bani hakuri yayi nadamar abinda yayi na Masa kowane irin hukuncine,mummy ce masa tayi yaje gida zata min magana godiya ha hau yi Mata yace mata Yana San ganin Mimi,Mummy tace Masa bacci take.

Ina Jin Yana Mata sallama akan zai dawo daddare,mummy tace ba sai yazo ba ya bari a kwana biyu har yanzu Ina Kan zuciya ne.

Koda na Shiga d’akin Ina Kara tuna abinda mahfuz yamin ne ina Kara Jin zafi a zuciyata.

Mummy kuwa data shigo rarrashina ta hau yi tana nayi hakuri,mijina na sona kila ma asiri Hadeeza ta Masa baa hayyacinsa ya kaita gida ba”

Murmushin takaici nayi dan nasan an Sha rainawa Mata wayo da Sunan asiri aka yiwa mazajensu bayan karyane ba wani asiri zalar iskanci ne ko asirine ma asiri na tada hali.

Wayata ta mikomin akan shi ya kawomin

Na kuwa karba nayi blocking lambarsa.

Miscall din Abdul nagani rututu har dasu text Koda na bud’e text dinsa hakuri yaringa bani da rantsuwar baisan abinda Mahfuz yayi ba kenan da bai kawota ba.

Ban Masa reply ba dan ba amfanin hakan ban Kuma wani ji haushinsa ba dan ada na dauka da hadin bakinsa amma tunda ga lokacin da nasan ba ruwansa naji ban rik’e sa a raina ba.

Har a raina so nake bayan sallah idan har Mahfuz bai kawomin takarda ta ba hisba Zan Kai sa.

Wasa Wasa sai gashi kullum mahfuz sai yazo gidanmu duk da bana fita,haka ya ringa kawomin mutane iri iri akan su bani hakuri ciki kuwa har da mijin mmn Iman da yace mahfuz Yana neman zarewa na yafe Masa yayi nadama.

Sam bana Jin mahfuz a Raina dan Mummy ma yanzu tausayinsa takeji,ita ta ringa hanani zuwa hisba.

Daidai da zainab kanwata sai da ta fara tausayinsa amma niko Ina nan Ina Jin haushinsa har yanzu Ina kwanta bacci Ina tuno yanda na gansa da Hadeeza.

A irin wanan lokacin Ina da wata daya da sati daya a gida Abdul yazo bayan dogon nasihar da yamin da waazi da roko akan na komawa Mahfuz na dage Masa na gama auren mahfuz,dan ko na koma wlh bazai ji dadin Zama dani ba dan mutuncinsa ya zube a idona na har abada ba Kuma na jinsa a zuciyata balle har na iya kyautata Masa.

A takaice dak’yar da nasiha da rarrashi dan mahaifiyata da ta sakoni agaba da mmn Iman na yarda Zan koma baa san Raina ba Ina jimanta irin zaman da zamuyi da mahfuz da ko kad’an bana kaunarsa, indai Zan gansa sai na tuna abinda yamin zuciyata tayi ciwon abinda yamin,sabida na bashi wahala nace Masa bazan zauna a gidanmu ba dan indai Zan kalli d’akin da Hadeeza ta zauna sai na tuna ta.

Take ya nemo gidan haya ya Kama mana sai rawar jiki yake yabi ya rame Kamar bashi ba,bana ma jinsa a Raina nasan bazaiji dadin Zama dani ba,dan.bazan tab’a yarda ya kusanceni ba dan bazai zo ya shafamin cuta ba……

Duk wayanda suke min sharing na barsu da Allah
MG’S SKINCARE

In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,

Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?

To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,

Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,

Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,

Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg’s bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button