BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Layin ya mayar a karamar wayarsa dan yasa a babbar wayarsa sai Hadeeza ta kusa cika mishi waya da magana ta watsapp.

Yana sakawa ko minti goma baayi ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa ya riga da ya haddace lambarta a kansa baiyi wata wata ba ya danna Mata blocking sai yake hango ta a idonsa yanda ta dame ko’ina a jikinta wani katon da a haife ya haifeta ya ringa bata ice cream a baki.

Texes ne sukayi ta shigowa da wani lambar zain ko bai bud’e ba yasan itace tayi amfani da wani layin

Duk message din na ban hakuri ne da bayanin ba saurayinta bane wani dan uwansu ne ya bata dama su had’u bata ji dadin wulakanci daya mata ba jiya ko bacci batayi ba,Kar ya manta irin san da take masa,Kar ya manta irin dukan da ta Sha a hannun matarsa bai dace ya Mata haka ba.

Tsaki yayi ya goge duk messages din ya Nemo lambar lubna a waya dan so yake ya goge komai a zuciyarta sai da Kiran ya kusa katsewa kafin yaji ta d’auka hira ya hau janta dashi amma daga yanda take amsa wayar yasan ba so take ba,dariya ma yanzu take bashi ita a lailai fushi take dashi,bayan yasan balain San shi take dannewa kawai take katse wayar yayi ya tutura Mata text ya ajiye wayar.

Kiransa da Hadeeza ke tayi da layin zain din da ta ke ta Masa texes ya danna a block Yana Jan dogon tsaki,har yanzu hangota yake da wanan katon yana bata ice cream ya rasa ma mai yasa yake Jin haushi idan ya tuna.

Wajen karfe daya ya mik’e dan so yake daga massallaci ya biya ta restaurant yayi take away guda biyu ya aikawa lubna daya shima yaci daya.

A bakin k’ofa ya ci Karo da Hadeeza da ta sha bak’ar doguwar Riga har kasa kamshin turare kawai take.

Da sauri yaja da baya cikin mugun hade rai,Yana “Mai ya kawoki office dina ban hanaki zuwa wajen aikina ba Wai Mai yasa bakida hankaline wane kallo kikeso a ringa min ne bana ce miki ki rabu dani ba”

Ba ko alamar fushi a fuskarta ta rufe k’ofar tana “Mahfuz taya zan rabu dakai bayan Ina sanka nasan kaima kana Sona, Mahfuz Ina duk alkawarikan da kayi min,na zaka aureni,duk wahala da na sha da dukan da naci a hannun matarka ya tashi a banza kenan a yanzu zaka ce na rabu da kai,bayan kasan banida kowa Wanda ka gani dashi a jiyan cousin dina ne ba saurayina bane”

“Hadeeza ada ni nace zan aureki a yanzu Kuma na fasa ba Kuma ki isa kimin dole ba,har ni zaki rainawa hankali kicemin wanan katon da na ganki dashi jiya cousin dinki ne?cousin dinki ne yake baki ice cream a baki?wane irin rantsuwa ne bakimin akan bakida saurayi ba ni kadai gareki,nasan irin wayanda kike hulda dasu taya zan aureki kina biye biye wlh Hadeeza Sam ban yarda dake ba na dade Ina zargin badani kawai kike muamalla ba jiya kuwa idona ya gane min dan haka a yanzu ban yarda da ke ba bazan iya aurenki ba ki daina kirana a waya Hadeeza karki hadani fada da lubna inasan matata”

Akan gwiwarta ta zube hawaye na zubo Mata Tana “Wlh mahfuz dakai kawai nake hulda ka yarda dani ba komai tsakanina da wanan da kagani dashi jiya,san da nake ma yasa nake ma duk abinda nakeyi bawai dan halina bane ba Zan iya maka komai dan na faranta maka rai”

Kamar an fusgo maganar daga bakinsa dan ya dade Yana san ya mata tambayar “Hadeeza bani na fara saninki ba wa Kika fara bawa kanki”?

“Fyade aka min a lokacin Ina secondary mahfuz shiyasa kaji haka amma wlh ba na muammalla da kowa”

Tasan ta hanyar da take Kama mahfuz hakan kuwa yasa ta cigaba da kuka cikin kirsa tunda taga yayi shiru ta cigaba da kuka cikin shagwaba taja gwiwar ta zuwa wajen da yake tsaye ta mike tsaye tare da rungumeshi.

Har zai janyeta ta Kara kankame shi.

So take ko Yaya ne ta rinjayeshi tunda ya fara botsare mata hankalinta ya tashi bata da wata hanya da zata samu ya fito ya aureta sai ta wanan hanyar da idan ta samu cikar burinta ya gama zuwa hannunta,so take ta nunawa lubna tayi kad’an bata Isa ta hana aurenta da mahfuz ba,so take ta nunawa lubna iyakarta a jiya ko runtsawa batayi ba burinta kawai mahfuz ya aureta.

Yanda ta fara kunna shi yasa mahfuz janye jikinsa da sauri Yana “Dan Allah ki tafi gida Hadeeza nan karki Manta wajen aikina ne”

“Bazan tafi ba sai ka tabbatar min da zaka zo gidanmu idan ba haka ba wlh haka zan ta zuwa nan”

“Hadeeza Dan Allah ki bari na samu nutsuwa zanzo ki daina kirana a waya bana so ki haddasa min wata fitinar har yanzu ban gama shawo Kan lubna ba Kuma kinsan duk abinda ya faru ke Kika jawo min,kema kinsan bazan samu wani kwanciyar hankali ba har nayi tunanin wani aure idan bana zaman lafiya da lubna”

Kamar ruwan zafi yake watsa mata haka ta ringa ji amma haka ta daure tana “toh idan ban kiraka ba kai zaka kirani”?

“Eee karki sake ki Kara kirana a waya Hadeeza da kaina Zan kiraki Kuma Dan Allah ki daina fesa wanan turaren yanzu lubna tasan kamshin turaren ki idan har kinaso mu cigaba da muamalla ya zama dole ki kiyaye Abubuwan da na fada miki na Kuma gaya Miki gaskiya a yanzu banida halin aure idan har matsuwa kikayi da auren sai dai ki nemi wani idan Kuma Zaki iya jirana toh sai ki bini a hankali”

Murmushi ta sakar Masa tana “Duk yanda kace ayi haka za’ayi Ina kaunarka Mahfuz”

Ta Kara rungumeshi,mahfuz da kyar ya Kai zuciyarsa nesa bai biye mata ba amma har kasan ransa yaji yana san kasancewa da Hadeeza dan wani irin salo take masa dake gigita shi.

A haka ya samu ya Koreta yana maida numfashi sai yake ganin kamar Lubna zata gane ya had’u da Hadeeza wayarsa ya d’auko ya Kira lubna Koda ta d’auka hira ya ringa janta dashi da alama ta fara saukowa dan ta dan biye Masa har take tambayarsa mai zata dafa mishi daddare sosai yake jinsa cikin farinciki saukowar da tayi hira Suka dan tab’a kafin ya kashe wayarsa ya sake alwala a bandakin office d’insa yayi sallah Koda ya iddar cire rigarsa yayi ya wanke a bandakin ya rage daga shi sai vest da dogon wando dan gani yake Yana zuwa gida lubna zata ji kamshin turaren Hadeeza a jikinsa a yanzu tsoro yake lubna ta gano Yana tare da Hadeeza bai san Mai yasa zuciyarsa taki bashi hadin Kan ya rabu da ita ba tana da tsara shi shikenan.

LUBNA

Tunda mahfuz ya kirani a waya ban Kara komawa bacci ba na tashi na nemawa kaina abinci naci na gyara ko’ina nayi wa mimi wanka na dawo Palo na zauna haka kawai nake Jin wani irin kadaici da ace a wancan unguwar muke da yanzu na Shiga gidan mmn Iman mun Sha hira.

Wayata na dauka dan na kirata Ina kuwa kiranta tace min yanzu takeso ta kirani akan ta shigo layin gidana.

Kasa hakura nayi ta shigo na fita waje na tsaya har ta karaso cikin farinciki na rungume ta mmn Iman nada wani irin matsayi a zuciyata Ina kaunarta sabida tana kaunata duk wani abu da ya shafeni tana daukarsa da mahimmanci damuwata damuwarta ce, duk da ta girmeni ko jinina ce ita sai haka.

Hira muka barke dashi ta hau tsokana ta akan nayi fresh anya daga dawowata mahfuz bai yiwa Mimi kanwa ba,nariga da nasan halinta ban biye mata ba
Na Shiga kitchen na dora Mana abincin muna hira Ina girkin har na sauke na zubo Mana muna cikin ci nake bata labarin duk abinda ya faru daga dawowata gidan har ganin da mukayi wa Hadeeza jiya da wani ban b’oye mata komai ba

Cokalin hannunta ta ajiye tana “Lubna ki ajiye duk wani fushi ki cire komai a ranki a yanzu ya Kamata ki zage wajen kyautatawa mahfuz wlh yarinya nan shaidaniya ce,duk da kince ya mata kashedi a gabanki zata yi duk abinda zatayi dan ta dawo rayuwarsa ke Kuma kisan yanda zakiyi ki hana hakan faruwa,yanzu balain da ake ta fama dashi kenan wlh shekaranjiya Abban Iman ya bani lambar wata da ta sako shi a gaba yace na kirata na nace mata ta daina kiransa a waya bakiga zagin da nayiwa yar iska ba,yau ma Yana Kira a wayarsa ya mikomin yace min itace tanajin muryata ta kashe”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button