BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Haka kacemin a gida jiya Kuma ka koma wajenta mahfuz da aurenka kake aikata zina,ban rage ka da komai ba sabida rashin godiyar Allah, ka bar matarka ta suna ka tafi wajen da zaka kwasowa kanka zunubi inaso na yarda shaidan ne ya rinjayeka daka kawota har gida jiya Kuma fa”?

“Wlh ban yi komai ba jiya lubna wlh bacin rai ma yasa na kirata muka hadu turarenta nada k’arfi shiyasa kikaji kamshinsa a jikina”

Mik’ewa nayi fadar ma ya hadu da ita bai san.mai hakan ke haddasa min bane.

Na shige kitchen sai gashi shima ya shigo kitchen din,bai bar kitchen din ba har na dafa farar taliya na yanka cabbage dan mai da yaji nakeso naci.

Koda na zubo haka ya saka hannu ya fara ci,so yake ya ringa abinda Zan tanka shi hakane yasa ko kulashin banyi ba Ina gama cin abincin na dauki Mimi nayi daki da ita na mata wanka.

Zamansa a palon yasa nayi kwanciyata a d’aki.

Ban Kara Jin motsinsa ba har bacci ya saceni bansan tsawon lokacin da na dauka Ina bacci ba sai ji nayi ana hura min iska a kunne na bud’e idona a hankali sai da na wartsake na kalli gefena da alama wanka yayi sai kamshin turare yake

D’auke kaina nayi daga kallonsa na matsa sabida Rabin jikinsa ya kwantar a jikina.

“Lokacin sallah yayi ki tashi kiyi sallah ga abinci nan na siyo mana yau ba sai kin wahalar da kanki wajen girki ba daddare sai mu fita”

Da a baya yace zamu fita inaga sabida doki bazan ma iya cin abincin ba dan a rayuwata Ina balain san naga mun fita,irin rayuwar nan na matukar burgeni,ban ce masa komai ba na sauka daga kan gadon na shige bandaki na dauro alwala na fito.

Kafin na iddar da Sallah ya fita daga d’akin ya dauko plate da cokali

Ina sane nayi zamana akan sallaya bazan cutar da kaina ba zanci dashi nake fushi bada cikina ba.

Ina satar kallonsa har ya zuba Miya akan sakwaran dake a mulmule yasan Ina balain San sakwara inaga hakane yasa ya siyo,duk abinan fa da yake yi da wata a zuciyarsa na girgiza Kaina Ina danne zuciyata dake san bijiromin da tunanin Hadeeza.

Yana gama zuba miyan ya kawo sakwaran ya ajiye a gabana ya dauko ruwan wanke hannu da ruwan roba ya zauna tare da tankwashe kafarsa Yana “Bismillah”

“Na koshi”

“Lubna dan Allah ki bari, fushi da zuciya bazai canza abinda ya riga da ya faru ba dan Allah ki sauke fushin nan haka haba lubna”

Ya yanko sakwaran ya kawo bakina na kau da kai

K’arfi da yaji ya dage sai ya bani a baki hakane yasa na wanke hannuna na fara cin sakwarar Kamar ana min dole,har ga Allah Kuma yamin dadi,fuskata a hade har na gama cin Wanda Zan iya ci Yana Jana da hira nidai ban tanka masa ba har na wanke hannuna na Mik’e na dauki mimi nayi Palo na zauna.

Shi ya kwaso kwanukan ba jimawa yazo palon shima ya zauna shi kadai ya ringa hirarsa da eee Aa kawai na ringa binsa bana san fushin mummy ya tabbata a kaina.

A haka har aka Kira sallah la’asar yayi alwala ya fita massallaci nima nayi sallah na sake wanka tare da canja kayan jikina nayi zamana daki na dauko wayata na kunna data na hau WhatsApp.

Grps na Shiga nake dan bin hirar mutane har ya Kuma shigowa d’akin ya zauna Yana yiwa Mimi Wasa Ina latsa wayata Ina satar kallonsa idonsa na kaina sai sauke numfashi yake, na riga da nasan duk abinda yake yiwa bana san na cigaba da dorawa.kaina zunubi Addu’a nake Allah ya bani ikon daurewa idan ya sake nemana.

Bai bar dakin ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah magriba da ya fita bai sake dawowa ba sai da aka yi sallah Isha.

A Palo ya tarar dani a zaune idan ta nice a koshe nake,sai dai ya nemowa kansa abinda zaici.

Yana shigowa yace na tashi mu dan fita baa machine zamu fita ba a machine Mai kafa uku zamu fita ya hada da na tayashi da Addu’a akwai kudin da yake sa rai idan ya shigo zai siyi mota.

“Idan ma aure zakayi wanan damuwarka ce ba inda zani sai ka dawo”

Ya dawo gefena da sauri ya zauna Yana “Lubna ba dan halina ba dan Allah ki tashi mu tafi”

Banza na bawa ajiyarsa ya cigaba da magiya yanda ya dagemin yasa na shige daki na canza kayan jikina zuwa doguwar Riga na yane mayafin akaina.

Shi ya goya mimi da jakar goyo ta gaba sai kallona yake ni kuwa na hade rai nasan so yake yace mayafin dana yafa yayi kadan ban saurare shi ba nayi gaba har muka fita titi ya tsayar Mana da abin hawa ya fada mishi inda zai kaimu.

Wayata nake latsawa har muka iso wajen da ake Shan ice cream yasan ni mayyar ice cream ce rabon ma daya siyomin tun Ina amarya.

Nidai binsa nake kawai a baya har muka iso wajen zama na zauna, ya miko min Mimi yaje ya fada musu kalar ice cream din daya keso a kawo daga Inda nake zaunen na ringa Kare Masa kallo.

Shigar kananan Kaya na balain yi Masa kyau so nake naga muninsa,amma na shagala da kallonsa Yana k’ok’arin jiyowa na d’auke kaina da sauri ya dawo ya zauna.

Muka hada ido ya sakar min murmushi na d’auke kaina aka kawo Mana ice cream din.

Ya mik’o hannu Yana na bashi Mimi naji dadin Shan ice cream din

Ban musa masa ba na mika masa Mimi na fara Shan ice cream din a hankali,har ga Allah naji dadi a raina, amma ban nuna hakan a fuskata ba sai ma Sha da nake a hankali kamar yamin dole,da alama masoya Nan suke zuwa har nawa namiji zai kashe ya kawo matarsa nan ya faranta Mata,mazan mu basa Mana adalci haka suke ajiyemu a gida su fito nan da Yan matan su waya sani ma ko ya kakawo Hadeeza nan take na hade rai naji ice cream din na neman fita a raina.

A hankali na saci kallonsa naga yana kallon wani waje hakane yasa na juya dan naga mai yake kallo,mace da namiji ne zaune macen ta bani baya yanayin jikinta Kamar na Hadeeza take naji gabana ya Fadi,na maido da kallona Kan Mahfuz da har lokacin yake kallonsu na Kara juyawa na kallesu,a daidai lokacin da namijin yake bawa yarinya ice cream a baki hannu daya mika yasa nagane a baki yake Bata amma banga fuskar macen ba,na Kara dawo da kallona Kan Mahfuz daa yanzu yake juya cokalin ice cream din ba Kuma Sha yake ba ni kuwa na zuba masa Ido Ina karantarsa hada Ido da mukayi yasa ya sakar min murmushi da a idona na yak’e ne yace “Kiyi ki gama mu tafi dare yanayi ko Kar Mimi ta kamu da mura”

Juyawa nayi na kara kallon wajen da dazu yake kallo sai dai har lokacin namijin kawai nake gani,macen bata jiyo ba,bansani ba ko hancina ne sai naji kamar kamshin turaren Hadeeza.

Kishi wata mahfuz keyi a gabana kenan take naji raina ya b’aci Yana k’ok’arin Magana nace “Sabida kaga Hadeeza da wani shine ka hade rai Mahfuz”

Ya gwallo Ido waje Yana “Kamarya lubna akwai wacce zanyi kishinta bayan ke ne ai babu dan Allah ki daina kiramin sunan ta ki gama Sha mu tafi”

“Na Gama”

Na juya na Kara kallon bayan yarinyar da Zan so ta juyo ba ma ja Hadeeza ce kamar na kwalla Mata Kira ta juyo Wanda kake kauna kake kishi,mahfuz ganin ta da wani ne yasa ya kasa Shan ice cream din,take naji zuciyata na min zafi daya barin Kuma sai naji dadin ganin daya Mata da wani duk abinan dai ban tabbatar da itace ko ba ita bace.

“Kaje wajenta Mana mahfuz Zan jiraka a waje”

“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun haba lubna”

Ya dan fada da karfi idona na Kan yarinya dan burina ta juyo na ganta aikuwa muryar mahfuz da taji yasaka ta juyo, gabana yayi wani irin faduwa.

Bana Jin tagani ganin mahfuz yasaka ta mik’ewa tare da gwallo ido tana mahfuz gadan gadan tayo wajen mu har lokacin bata gani ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button