BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Karfinsa da nawa ba daya bane duk yanda naso na hanashi kasa wa nayi,haka ya hau jagwal gwalani,Yana dab da cimma burinsa na hau tuno abinda yamin da yanda ya binne kansa a kirjin Hadeeza “idan kasan Kai dan halak ne ka kyalleni idan Kuma ba dan halak bane Kai sai kayi amma inaso kasan ba abinda zakayi naji Dadi a raina bakin ka nake gani har yanzu Ina hango ka a kirjin Hadeeza

Tunda na fara magana ya tsaya cak Ina idda magana ya dagani idonsa yayi jajjur Kamar jini yace “Lubna ni dan halak ne Kuma Zan nuna Miki nidin dan halak ne”

Ya dauke gajeran wandonsa da sauri yayi hanyar d’aki….
Mg’s cakes nd more
For the lovers of cake,Ina masu biki ko suna ko wani shagali na musamman ko dan jin dadinku da morewar ku ko kuma akwati kuke Shirin ansa zaku bayar matsayi tukwaici,tofa nesa tazo kusa domin kuwa zamu tabbatar mun fidda ku kunya mun kuma gamsar daku da hadaddun abubuwa kamar su,cake nd cupcakes,meat pie,fish roll da kuma egg rolls,to me ya rage muku ai kawai ku tuntube mu ta number nmu kamar haka 07067210195,08062991549 cika alkawari shine taken mu,adade anayi sai gaskiya

WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi

Page 20

      Lubna

Koda na Kira Mummy na fada mata fitar da mahfuz yayi da girkin da na masa yaki ci cikin kuka na Kara da “mummy wlh mahfuz a yanzu baya sona hankalinsa ba’a kaina yake ba, shiyasa nace miki bazan dawo ba wlh dan biyan bukatarsa ya dawo dani, yau kwana biyu da dawowa gidansa har ya fara fita wajen budurwarsa wlh abinda na dauka a baya bazan iya dauka ba yanzu, tun daga lokacin da na kamashi da budurwarsa ya fice min a rai mai kaunarka bazai tab’a maka haka ba dan haka wlh mummy bazan iya zama ba zan hakura da aurensa yafimin alheri”

“Shikenan Lubna mijinki bazai fita ba sai kice zance yaje?wai wanan wane irin abune kinfi so tun kina karamarki a ringa kirga miki aure? Kin isa ki canja abinda ya faru ne? Idan kina haka zai goge abinda ya riga da ya farune?,shikenan dan kin kama shi da laifin cin amanarki duk wani motsi ko fita da zaiyi cin amanarki yake”? Lubna bazaki ki kwantar da hankalinki ba ko?bakya Jin magana ko?kinaso ki nuna ban Isa dake ba ko?to ki kashe auren naki tunda bazaki iya zama ba “

Kit naji ta kashe wayar.

Nabi wayar da kallo hawaye na zubo min mummy ta kasa fahimta ta ta kasa gane halin da nake ciki,duk abinan da mahfuz yamin taya zan iya mantawa da wuri,har na iya sakin jikina dashi,ko zan saki jikina dashi sai na tabbatar da rabuwarsa da Yar iskar budurwar sa da ni nasan bazai iya rabuwa da ita ba idan har yasan bazai iya rabuwa da ita ba ya aurota ya sakeni,dan bazan tab’a zama da Hadeeza da Sunan kishiyata ba,ko fitar da yayi ban yarda abinci yaje nema ba nasan wajen Hadeeza ya tafi,idan har Yana Sona dan nayi fushi akan abinda yamin,bai Kamata yayi fushi ba har yak’i cin abincina.

Haka bakin ciki ya cikemin zuciya Ina kallon agogo har tara ta wuce ko uwar abinci yaje ci yaci ace ya gama ci ya dawo idan ba wulakanci ba da Rana ai da yayi zuciya da abincin zuwa yayi ya dafa bai fita nema ba.

Tara da rabi na wucewa na mik’e naje na kulle k’ofar ba inda yaje sama da wajen Hadeeza dan me ya matsamin na dawo bayan Yana tare da ita.

Na dauki Mimi muka Shige daki muka kwanta ni kadai nasan bakin cikin da nake ciki,mahfuz ya Raina min hankali.

Ina kallon agogon har goma ta wuce da minti goma anan na yanke sai dai ya koma wajen Hadeeza ya kwana amma ko ya dawo bazan bude masa kofa ba Kuma sai ya bani takardar sakina ko yanaso ko bayaso gwara ya sakeni yaje ya karata,idan ya ga dama ya auri Hadeeza idan yaga dama ya kawota gidan ta zauna na dindin din wanan matsalarsa ce amma matsawar Ina amsa sunan matarsa ina zaune a gidanan wlh sai dai ya zabi Hadeeza ko zama dani tuna duk abinda nayiwa mahfuz daga lokacin da muka hadu zuwa na aure shi nayi hawaye ya hau zubomin,na tuna akwatin Aurena da ba kayan arziki ya zuba min ba haka kawayena sukayi tayi dani,ko damuwa banyi ba dan Ina kaunarsa,duk wani abu Kuma da nayi da mukayi Aure rabin hidimar mummy ke bani kudin dan duk wata inta dauki albashi haka take binmu da kudi ba iya ni kadai ba dani da Zainab dan tana d’aukar albashin da yawa gashi dagani sai zainab da yayata da nake bi.

haduwata da mahfuz yasa ban cigaba da karatu ba dan yace kishine dashi,haka nake zaune sai mummy ce ma take cemin na bari idan na haihu zata bani jari na kama Sana’a,ban tab’a b’atawa mahfuz rai da gangan ba,duk wani abu da nasan Mahfuz naso Ina iya k’ok’arina na Masa koda ni banaso amma sakayyar da mahfuz zaimin shine ya kawomin budurwarsa har gida ya munafirceni,ya fifitani akanta ya Kuma Sakani hidima da ita,dan Nagano shi nayi fushi shine zaiyi fushi shima,Mai amfanin zama da mahfuz, mutumin da hankalinsa ya koma kan budurwarsa da taki aurensa sabida bashida abin duniya,banma san Yana da rufin asiri ba sai da budurwarsa tazo gidan har ya iya bata Dubu ashirin kudin kitso da kunshi,har a yanzu dubu ashirin a dunkulle bai tab’a bani ba.

Na kara kallon agogon naga goma da minti talatin da biyar adaidai lokacin da naji bugun kofa na maida idona na rufe dan dagaske so nake ya kwana a waje idan gari ya waye yayi zuciya ya bani takardar saki na.

Duk bugun da yake Ina jinsa har Kiran da yake min a wayata da nasaka a silent.

Idona biyu bai fasa buga kofar da Kiran waya ba har daya na dare yayi.

Haushin karnuka kawai nake jiyowa a waje burina ma su cije shi buga kofar da naji ya daina na tsawon mintuna yasa na bud’e idona,wayata dake ta kawo haske na leka naga mummy ce take kirana,da sauri na mike zaune na daga wayar

“Lubna yanzu mijin naki Kika kulle a waje innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dama haka kike a yanzu na tabbatar da kina da matsala a yanzu na yarda akwai mugayen Abubuwan da kikeyi dayasa yarinya nan ta d’auke masa hankali wlh idan baki so naci ubanki kije ki bud’e Masa kofar nan”

Kuka nasaka Ina k’ok’arin Magana ta kashe wayar.

Na duro daga kan gadon nayi waje a fusace na bud’e k’ofar na ja da baya Ina jiran ya shigo.

Sai daya dade kafin naji Yana kokawar shigowa da machine dinsa.

Ina tsaye har ya shigo fuskarsa a balain had’e,kamar yanda nima nawa yake a had’en.

Yana saukowa na fara shakar kamshin turaren Hadeeza daya saka kirjina wani irin bugawa na tabbata ko hauka nake ba’a hayyacina nake ba idan naji kamshin turaren Hadeeza nasani.
Dagaske mahfuz wajen Hadeeza yaje daga dawowa ta bai ma iya daga kafa na kwana biyu ba tunda na hanashi kaina gwara yaje wajenta ta bashi,nama bashi yaje wajenta ballantana yanzu da na hanashi.

Wani irin zafi naji kirjina namin daya kusanto wajen da nake tsaye a fusace ban bari ya karaso ba na daka tsalle na isa wajensa na cakumo wuyan rigarsa sosai yake kamshin turaren hadeeza

“Bani takardar sakina mahfuz na balain tsanarka cutar da kayimin Allah ya Isa ban yafe maka ba bani takarda sakina mahfuz”

Wani irin fincike hannuna yayi daga rukon da nayi masa cikin hucci yace “Ni kikayi wa laifi amma zaki zo ki cakumi wuyan riga na kice na sakeki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button