BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Daga aurena da mahfuz zuwa yanzu ban wani fuskanci matsala ba duk da kyautata min da yake Yi a waje da bambanci a yanzu da muka yi aure, dama can ba soyayar kudi muka yi ba shiyasa Koda muka yi aure ba wani kudi yake bani ba nima ban damu ba bansani ba ko dan ban Dade bane Zan bukaci kudi a gaba kayan abinci dan abinda bazaa rasa ba ban Kuma damu ba.
Zuciyata suya kawai take bacci ya kauracewa idona zuciyata nata sak’a min na tashe shi na tambaye shi da wa yake waya,wata zuciya.kuma na hanani akan nabi komai a hankali.
Kiran sallah asuba a kunnena dama Ina rigashi tashi sallah ni nake tashinsa.Haushinsa da nakeji yasa ban tashe shi ba naje.na daura alwala inaga motsin rufe k’ofar bandakin ne ya tashe shi.Koda ya mike Yana Hamma yace “Da ban tashi ba,bazaki tasheni ba kenan”?Ban ma iya bashi amsa ba bama naso nayi magana dan wani abu ne ya tokareni a mak’oshi.
Banida burin daya wuce ya tafi massallaci na dan bincike wayarsa dan na tabbatar da zargina.Sai dai yana fitowa daga bandaki ya zura wayarsa a jallabiyarsa yayi ficewarsa.Zuwa yanzu zargin mahfuz nada budurwa ya tabbata dan a kwanakin nan yafara haka,amma baya fita da wayarsa har password dinsa nasani dan sunana ne.Ina zaune ne kawai akan sallaya zuciyata fal da tunanin da mamakin mahfuz dana d’auko so da yarda na dora masa.
Mahfuz ba mutum bane da idan yaje massallaci Yake dadewa sai gashi har gari ya fara haske bai dawo gidan ba.Tuni wani irin kishi ya turnike ni jikina har rawa Yake.Har zan fita waje na koma dakina na dauki wayata tare da bin umarnin zuciya ta akan na gwada Kiran wayarsa naji ko dai wayar yake.Ina kuwa kira ya nuna call waiting Wanda hakan ya kara saka kirjina nauyi sabida kishi ban hakura ba na cigaba da kira dan idan har ya daukeni da mahimmaci ya Kamata ace ya dauki wayata tunda nasan dole zai ga kirana sai dai bai dauka ba nima ban fasa Kira ba nasan bazai wuce layin unguwar ba dan gida uku ne tsakanin mu da massallaci da hijabin jikina na fita waje wayata Kare a kunne na a dakalin gidan makociyata na hangoshi a zaune.Yana ganina ya katse wayar tare da mik’ewa tsananin bacin rai yasa tun kafin ya iso nace “Mahfuz da wa kake waya”?Murmushi ya sakar min Yana da Abdul nake waya ManaKatse shi nayi a dan tsawace Ina “Wlh karyane Mahfuz da mace kake waya bada Abdul kake waya ba””Ni nake miki karyar”?Yace Yana nuna kirjinsa fuskarsa ta sauya daga murmushi zuwa bacin rai”Ai nasan karyar ne mahfuz dan idan da Abdul zaka yi waya bazaka fito waje kayi wayar ba, jiya ai naji duk hirar da kake yi da budurwar ko zaka rantse ba da budurwa kake wayar ba,Mahfuz wacece ita?dudu yaushe muka yi aure da har wata zata fara d’auke maka hankali jiya har ka barni a daki ka fito Palo Kuna video call har kana ce wa zata saka kayi mafarki a banza”?Dogon tsaki yaja ya ratsa ta gefena ya Shige ciki na juya da sauri raina na balain suya daki ya nufa nabi bayansa Ina cigaba da tambayar sa da wa yake waya amma ko kallona baiyi.Takaici yasa na fashe da kuka Ina “Mahfuz wacece ita mai na maka da zaka sakamin da cin Amana”?Banza ya bawa ajiya ta abinda bai tab’a min ba ya d’auko wayarsa ya fara lalatsawa kamar ba dashi nake magana ba,tun auren mu bamu taba hayaniya dashi ba,bamu taba dogon fada dashi ba,Mahfuz da nasani Ina d’an b’ata rai zai hau rarrashina Yana bani hakuri sai gashi yanzu kuka nake a gabansa amma ko kulani baiyi baYanda ya watsar dani ya bawa banza ajiyata yasa na fusge wayar daga hannunsa a zuciye ya dago da idonsa da suka dan rine sabida b’acin rai ya mik’omin hannu Yana “Bani wayata Lubna kafin na sassab’a miki””Bazan bayar ba Mahfuz har sai ka Gaya min da wacce Yar iskar kake waya”Mik’ewa yayi Yana k’ok’arin Magana naji wayar sa na vibrating a hannuna da alama ya cire ringing tone din a vibrating yasa.Da sauri na juyo da wayar naga SR ke kira a waya a cikin Sakani na dauki wayar na Kara a kunnena yayo kaina da balain sauri a daidai lokacin dana ji muryar budurwar da bazan tab’a mantawa ba a rayuwata wacce ta watsa min farincikina ta kusa zautar dani.”Sugar lafiya kuwa naji ka katse wayar”Maganar daya fito a bakinta kenan “Allah ya tsine Miki shegiya kwartuwa”
Ihu na saka sakamakon murd’emin hannu da yayi ya fusge wayar a hannuna Yana “Ke wacce irin wawiya ce mara hankali kinsan wacce kike zaginta”?”Nice wawiya mara hankali sabida na zagi budurwar ka mahfuz”?Nace Ina nuna kaina hawaye mai zafi ya hau zubomin yaja dogon tsaki ya nufi wajen wadrobe din kayansa ya fito da kanan kaya hawaye kawai nake Ina kallonsa har ya gama canza kayan jikinsa ko kallona baiyi ba ya fice daga d’akin.Rawar da jikina keyi yasa na zube akan gwiwa ta na cigaba da kuka Ina tunanin ko dai mahfuz ba’a hayyacinsa yake ba har wani dumm na ringa ji a kunnena dana tuna sunan da Yar iskar ta Kira mahfuz dashi Sugar….

mg’s skincare

Shin Ina matan suke????️????️????️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi????????
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg’s organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum????hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg’s b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki????
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi’iznillah sister’s duk Wanda yayi using mg’s sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy ????ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg’s skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg’s babushi akasuwa????
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go????
Then @mgs skincare gat you covered ????
Now is time to glow????
Pamper ur skin????
Shine like bride????????♀
Glow????♀️

???? tested nd trusted????
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
BUDURWAR MIJINA

         *NA SADNAF*

E.W.F.

PAID BOOK

PAGE 2

Bansan tsawon lokacin dana d’auka a durk’ushe a kasa ba,zuciyata Kamar an cinna Mata wuta ban tab’a sanin haka nake da tsananin kishi ba kawai Ina hararo irin so da kaunar da mahfuz yake gwadamin ya fara gwada wa wata,har ta d’auke Masa hankali a kaina akanta ya cemin wawiya Mara hankali waya sani ma ko zance yake zuwa wajen tsininiyar yarinya da ta Kira mahfuz da sugar,har san da yake Mata ya Kai Muna kwance ya baroni a daki ya fito Palo dan kawai yayi waya da ita.
Ko dan na samu ciki hallitar jikina ya canza yasa mahfuz ya fara ganin munina
Tunanin daya darsu a raina yasa na m’ike a hankali na nufi wajen da mudubi yake na fara karewa kaina kallo tunda ga saman goshina tare da shafa fuskata.
Tunda na samu ciki wani irin kananan pimples suka feso a fuska ta suka Sakani Muni,siririn lebbena yayi kauri.Haka hancina da bai fiye tsini ba ya doke nasan cikin nan yasani muni ba kadan ba fari dai na Kara tunda ni fara ce.Baza’a sakani a sahun masu tsayi da kyau sosai ba akan dai mahfuz za’a sakani a sahun masu kyau duk da mace sai ta dan yi kwalliya kyaunta ke Kara fitowa.Kwalliya da nake yi yasa ake ganin kyauna sosai. mutum tara yake bai cika goma ba abinda na rasa shine nono banida cikar kirji Sam idan na ga mace mai kirji sai naji Kamar na sace ko dan mahfuz da sai da muka yi aure na fahimci Yana balain san no-no,kafin na samu ciki indai Muna zaune hannunsa na saman kirjina Yana shafawa wai idan ana yawan shafa shi Yana fitowa.Bansan Yana san nono ba sai da naga ya fara siyomin duk wani cream ko supplement akan na ringa Sha zai taimaka wajen fitomin da nono.Ba abinda banyi amfani dashi dan nono ya girma ko dan na farantawa mahfuz rai amma abin ya gagara daya ga na fara matsawa kaina ya ce min na daina takura kaina duk da haka burina na samu nono na ya girma idan na d’auke nonon ba wani abu a jikina da baya burge mahfuz.Idan ya dawo bashida wajen kwanciya sai a jikina ya gwadamin kaunar daya narkar dani a kogin Sansa burina bai wuce nayi abinda zan faranta Masa ba Koda bana so har na samu ciki banga canji a wajensa ba duk da mitar da nake akan cikin ya sani muni hakan na iya sawa mahfuz ya rage ji dani.Idan na ce masa nayi muni dariya yakemin yace shi bai gani ba ai cikin nan yasa kirjina ya ciciko,bamu tab’a fushi da juna ba,bamu taba sa’insa ba,bai tab’a gaya min bak’ar magana ba sai gashi wata Yar iska tana neman juyar min da kwakwalwar miji bansan adadin tsinuwar da nayiwa macen da ta Kira shi ba.Gajiya nayi da tsayuwa agaban mudubin na koma Kan gado na kwanta Ina sak’e sak’en yanda zan biyowa mahfuz ni nasan idan ya dawo dole ya bani hakuri dan baya iya dogon fushi dani dole na nuna Masa bacin raina na Kuma jawo shi jikina na binciki wayarsa nayi blocking din Yar iskar yarinya da take kiransa,da Wanan tunanin na samu nayi wanka abincin ma da kyar naci sabida b’acin rai,sai duba wayata nake naga ko zai kirani ko zaimin text,har watsapp na hau naga ko ya ajiyemin sako duk shiru,hakan kuwa ya Kara saka min Jin haushinsa na tanadi masifar da zan Masa idan ya dawo.Kamar bazan yi girkin dare ba na daure na dafa jollof din shinkafa na hada Masa zobo.Nayi kwalliya kamar yanda na Saba na zauna zaman jiransa raina a had’e.Mahfuz bai dawo gidan ba sai goma da rabi na dare Ina Jin sa ya shigo da machine dinsa.Ciki ciki yayi sallamar ya hade rai da leda a hannunsa bai Kuma Kalli inda nake ba.Baki sake nabi shi da kallo har ya shige daki mamaki da bakin cikin halin ko inkular da ya nuna min ya rufeni,Mai mahfuz yake nufi dani yamin laifi ya nade tabarma da kunya a zuciye na tashi zan bishi har d’akin.
Kafin na isa d’akin na tsaya Ina bin umarnin zuciyata dana watsar dashi zai nemeni da kansa.
Da wanan tunanin na nufi daya d’akin da idan ba baki muka yi ba ba Mai kwana a ciki.Nan na shige zuciyata na balain tafasa
Duk abinda nayi dan na samu zuciyata tayi sanyi duk a banza kofa kawai nake kallo ko zanga shigowarsa yazo bani hakuri ga yunwa da nakeji amma bana jin cin abincin.
Watsapp na hau sabida na samu nayi hira da Yan uwana da muke grp daya ko zan samu na rage bakin ciki dake Raina sai dai Ina hawa na duba mahfuz naga Yana online,wato ba abinda ya dame shi ni nasan da Yar iskar yarinya yake hira.Ban iya hakuri ba na rubuta “Mahfuz yanzu nice abar wulakantawa a wajenka ko,”?
Bai bud’e sakon da wuri ba na fara k’ok’arin Kara rubutu naga ya bude ya turo “hmmmmm”
Bakin cikin bazai iya bani hakuri ko ya biyoni daki ba yasa na kashe data na wurgar da wayar,Idona akan agogo har karfe daya na dare sai juyi nake ba alamar bacci zai daukeni sai tunani daya cike min zuciya tunda mukayi Aure bamu taba raba shimfida da mahfuz ba sai gashi a sanadin haduwa da wata nayi fushi dashi bai ma kalleni ba.
Hawaye kawai ke zubomin Ina tsinewa macen da ke san Shiga tsakanina da mahfuz har ta samu matsayi haka a wajen mahfuz da zai k’i nemana a kanta sai da cikina ya tsufa mahfuz ya fara daga min kafa amma ko yayane sai ya nemeni ko period nake sai na Masa dabaru har hirar na tab’a yi da wata aminiyata take cemin namijin da baya iya daga ma kafa ba karamin gamsar dashi ake ba.Amma mahfuz yamin laifi akan Ina kishinsa bai iya bani hakuri ba,nifa yayi wa laifin nan amma shine ya kasa bani hakuri.Har tunani na Kara yi a tsanake dan naga ko dai zaginsa nayi cikin fushi batare da nasani ba sai dai banda karya tashi da nayi na zagi tsinaniyar da ta kira ban Masa komai ba.Zuciyata raya min kawai yake akan naje d’akin na sameshi wani b’ari na zuciyata na hanani akan shi yamin laifi shi ya Kamata ya nemeni.Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga dan bakin ciki sai biyu da wajen rabi na dare bacci yayi awon gaba dani. Ban tashi bude Idona ba sai wajen bakwai da minti goma Sha biyar.Na Mik’e da sauri Ina sallati na tsani naga sallah asuba ta kubcemin.Da balain sauri na fada bandakin na daura alwala na fito.Sai dai banida hijabi a dakin bana san zuwa dakina naga mahfuz sai dai ya zama dole tunda ba hijabi a d’akin.Fuskata a had’e na nufi dakina a hankali na tura k’ofar na shiga.Bangan shi a dakin ba na dai jiyo motsinsa a bandakin da alama wanka yake.
A madadin na d’auko hijabi na wajen da na hango wayar sa a saman bedside drawer na nufa da sauri na dauki wayarsa na fita daga dakin na koma daya d’akin na saka key na zauna a saman gado hannuna sai rawa yake.Ko da na bud’e wayar ajiyar zuciya na sauke da naga ba password.Message dinsa na fara shiga SR da na gani ta turo message da bai bud’e ba yasa na bud’e message din jikina na balain rawa Message ta turo.masa wajen biyar na asuba da alama reply ta Masa “Kayi hakuri sugar banga kiranka ba sai yanzu kasan jiya ban kwanta da wuri ba how was your night my love zaka biyo d’in I missed you”Hannuna rawa kawai yake kirjina Kamar ya fado ji nake ma dakin na juya min”Lubna ki bud’e min k’ofar nan sabida Mai zaki zo ki dauki wayata?Wai me yake damunki ne”Najiyo mahfuz a bakin k’ofa Yana jijjiga k’ofar.Rawar da jikina keyi yasa ban ma iya mik’ewa ba na nemo lambar SR na fara kiranta a wayarsa bugu daya ta d’auka murya can kasa tace “Sugar ka iso ne”?”Kutumar bura ubanki tsinanniya ya iso wajen ubanki shegiya laananiya”Kit naji ta kashe wayar na Kara kiranta bata d’auka ba,ban hakura ba na cigaba da kiranta Mahfuz kuwa sai jijjiga kofa yake Yana kwalla min Kira akan nazo na bud’e k’ofar na bashi wayarsaGanin tak’i d’aukar wayata yasa na m’ike jikina na rawa naje na bud’e k’ofar mahfuz ya fado dakin da sauri ya fusge wayarsa daga hannuna idonsa ya Kada yayi jajjur cikin k’ak’ausar murya yace “Daga yau karki Kara tab’a min waya lubna wlh Kika Kara sai ranki ya b’aci kinji na fada miki”Ya fara k’ok’arin juyawa ya bar dakin na Sha gabansa da sauri hawaye na zubomin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button