BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Dukansu sunyi aure da matansu kannensu Mata uku suma sunyi Aure,Yar autarsu shemau kadai ce ta rage batayi Aure ba.

“Mahfuz ashe abinda ka aikata kenan kanka daya kuwa taya zaka dauki budurwarka ka kaita har gidanka”?

Mahfuz najin haka yasan Ammi ce ta fada musu,fada Suka rufe shi dashi Kamar zasu dake shi sai Ammi ce ta tsawatar musu tana “kuka san dalilin dayasa ya kaita gidansa ni abinda yasa na fada muku sabida kuji irin dibar albarkar da yarinya nan tayi mana idan haka ta kasance sau tari mace tagari rufawa mijinta asiri take,amma.yarinya nan haka ta Tara Mana jamaa a yanzu nasan kowa yasan mai ya faru yarinya nan Sam ba matar rufin asiri bace sai kunga yanda ta canzawa yarinyar kamani”

“Haba Ammi ya zakice haka wlh duk Wanda akayi wa haka dole ya dau matakin da ta d’auka har gida fa ya Kai budurwarsa dan bashida mutunci ,a madadin ki Masa fada shine kike k’ok’arin fito da laifinta bansan Mai yasa bakya san laifin yayanki ba yanzu da shemau ko Amina akayi wa haka wlh nasan kece gaba wajen cewa Baki yarda ba”

“Fito kawai fili ka dura min ashar Aliyu Kai dama ai bakada mutunci tunda kayi aure kunnuwaka Suka Kara fadi kamar na matarka,nama manta Kai waye na tsaya Ina fada muku na manta bazaku bi bayan dan uwanku ba ai bance muku yayi daidai ba abinda yayi Amma abinda ita lubnar tayi yayi yawa yanzu da auren sukayi da yarinya nan halan haka kishi zai saka ta zuba Mana hauka”?

Duk sun Riga da sun San halin Ammi dan yanzu nan ma sai laifiin Kuma ya koma Kan matansu da suka San hakuri suke da ita hakane yasa Suka ja bakinsu suka tsuke har ta gama ta fice kafin suma suyi waje gabad’aya dan su tafi massallaci mahfuz na dab da fita Ammi ta tsayar dashi tana “Ka tabbata daga massallaci ka jeka ka gano yar mutane idan an sallameta a yau ta dawo nan din ta zauna kafin Iyayenta su dawo”

“Aaa Ammi dan Allah idan an sallameta na bata kudin mota ta tafi wajen danginta ba dai a gidan nan ba yanzu dan Allah idan lubna taji labarin tana gidanmu wlh bazata ji dadi ba zan Kara jawowa kaina matsala ne a wajenta.

Mahfuz Anya haka.yarinyar nan ta barka kuwa”?

“Mun tafi massallaci Kar mu makara yafice daga gidan da sauri yabi bayan yayyensa.

Suna fitowa daga massallaci,Mahfuz cikin kwantar da murya da biyyaya ya hau neman taimakon su ya Alin akan su shige Masa gaba wajen zuwa bawa lubna hakuri,Ya Ali tsaki yaja yayi tafiyarsa Yana ba inda zaije.

Sai Ya Usman ne yayi ta Masa fadan abinda yayi a karshe yace “yarinya nan daka Kai gidanka Sam Bata da tarbiyya karka soma aurenta domin ka aureta wlh sai kayi matukar nadama Taya mace zata biyo namiji har gidan aurensa wanan yarinya sam bata da kamun kai, idan ma so kake ka aureta ka gaggauta fasawa Ina laifin matarka yarinya Mai hankali dududu yaushe ma kayi auren dan masifa.

Sharrin shaidan ne Yaya tsaki Ya Usman din yayi Yana “Ka fara zuwa asibitin ka dubota karfe uku kazo ka sameni a gida sai mu tafi Allah ya kyauta”

Mahfuz machine dinsa ya hau ya nufi asibitin Ya Usman Kuma yaje ya hau motar ya Aliyu suka tafi.

Hadeeza.

Bakin ciki kamar ya kasheta data ga mahfuz baizo ba,Koda ta ce shemau ta Kira mahfuz taji Yana Ina ce mata tayi ta kirasa bai d'auka ba.

Ko baccin bata koma ba har gari ya waye tunani kawai take Yana can kila ma Yana rarrashin Lubnar da ta kusa kasheta ko’ina na jikinta kuwa ciwo yake mata, idan kanin mahaifinta ya dawo sai dai tace Masa hatsari tayi,lubna bata daki banza ba insha Allahu sai ta rama dukan da ta Mata idan ta auri mahfuz sai ta fitar da ita daga gidan,cikin kirsa zata saka Mahfuz ya saketa,dan ta gano logon Mahfuz.

Wajen sha daya taga mahfuz ya shigo fuskarsa a daure.

Shemau na gaishe shi ta mik’e tana “Wlh dama na gaji Yaya ko sallah idi yau bansamu zuwa ba bari naje gida”

Yana Jin idon Hadeeza daya balain kankancewa sabida kumburin da yayi a kansa,ko kallonta baiyi ba dan haushinta Yake ji bashida burin daya wuce ya yakice ta ta barshi ya sarara “Nima ai ba dadewa zanyi ba ai inaga ba wani matsala sallamarta kawai za’ayi yanzu dan na biya ta wajen likita yace ba wani matsala”

“Toh nidai na tafi Yaya sai kun fito”

Tayi waje da sauri sai a lokacin ya kalli ya Hadeeza da take zubar hawaye fuska a had’e yace “Ya jikin naki”?

“Mahfuz sai a yanzu zaka zo wajena”?tun jiya da kuka kawoni mahfuz baka Kara waiwayata ba, kaga yanda matarka ta min lahani kaga fuskata mahfuz duk halin nan da nake ciki matarka ce jefani a ciki amma shine baka zauna dani a asibiti ba sai a yanzu kazo”

“Kinsan halin da Kika jefani a ciki ko Hadeeza kin zubar min da mutunci Hadeeza wanan wane irin rashin hankaline taya zaki saki baki ki fadawa lubna komai har dasu Ina zuba mata magani a lemo dan nazo dakinki Kika ce mata kin bawa Ammi atamfa wane irin rashin hankaline wanan”?

“Mahfuz mutuwa na gani Kai yanzu damuwarka abinda na fada ba lafiya ta ba haba mahfuz matarka kiris ya rage ta kasheni da ban fada mata ba ba abinda zai hana ta kasheni fada ya Kamata kazo kana min Ina cikin wanan halin tsakani da Allah Mahfuz”

“Komai zata miki bai Kamata ki fada mata komai ba kinzo kinsani nayi Abu mutuncina ya zube lubna tayi fushi ta koma gidansu,kin jefani cikin tashin hankali Hadeeza nifa Ina kaunar matata bance Miki bana Santa ba,badan kin dawo rayuwata ba ni ta isheni rayuwa bana bukatar wani Karin Aure Kuma na fada Miki”

“A yanzu Kuma fa”?
Tace tana zubar da hawaye

Mahfuz ya d’auke kansa Yana

Hadeeza bari na karbo takardar sallamarki idan an sallameki sai na raka ki tasha na biya Miki kudin mota zan nemeki idan komai ya daidaita”

“Taya zanje gida a haka bayan na fada maka ba kowa,can gombe ma ba kowa sai dai naje gidanku”

“Hadeeza baza kije gidanmu ba wanan wane irin masifa ne Taya zakije gidanmu da wane Ido kikeso dangina su kalleki a kin gama zuwa gidan aurena kin zauna kin zauna Kuma a gidanmu Zan aureki,sai kace a kudu,a kudu nasan ake haka,mace zata je ta zauna a gidansu saurayi,wannan ba al’adar bahaushe bane Sam,dan haka bazaki zauna a gidanmu ba gidanku Zaki tafi”

Yayi waje a fusace Hadeeza tabi shi da kallo baki a sake,sam bata tab’a tunanin zai Mata haka ba,lailai idan batayi dagaske ba Mahfuz bazai aureta ba,da alama duk Haushin tona musu asiri da tayi yake ji anya Haka lubna ta barsa ba asirice shi tayi ba.

Mintuna da fitarsa sai gashi ya dawo da likita.

Likitan ya duduba ta ya tambayeta inda ke Mata ciwo ta fada Masa kanta ne har yanzu yake balain ciwo.
Yayi rubuce rubuce a takarda ya bawa mahfuz akan a siya Mata magunguna Yana karba yace tazo su wuce su tafi

A wajen tashin haka tayi ta cicije lebbe tana faduwa da gangan taga ko zai taimaka Mata amma ko kallonta baiyi ba har ta saka takalminta ta fara tafiya a hankali tana binsa a baya.

Ta d’auka gidansa zai kaita ta kwaso kayanta tana so taje taga ko Lubnar na nan, sai dai suna zuwa ya tsayar da abin hawa akan ya kaita gidansu zai aiko Mata da kayanta yaki bari ma ya kalleta ganin Yana k’ok’arin tafiya yasa ta ruko hannunsa tana “Ya zancen Aurenmu mahfuz”?

“Allah ya Mana zabin daya fi alheri”

Yace tare da fusge hannunsa daga nata……

Kuringa hakuri dani wajen posting din Daren da nake a lokacin nake da time

Don’t share my novels plc
Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg’s skincare is the best plug for you????
Do you wish to have that flawless skin that’s free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go????
Try mg’s product nd I assure you you’ll never use any other product except mg’s product✅
Mg’s will gv you the best out of all
With mg’s product ur skin is ???? clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day????
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it????
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
07046881166
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button