BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare

what are you guys waiting for hurry nd grab urs???? now is the time to glow????♀️
Pamper ur skin????
Shine like a bride ????
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders????

Do not forget to follow us????
Like nd comment pls dearies????
Patronize us????
mg’s always serve you the best✅❤️

WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min sharing idan bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi

Bm

 *Na Sadnaf*

Page 16

Hadeeza ji tayi wani zazzabi na Neman rufeta dama da zazzabin ma, matsawar mahfuz bai aureta ba taga ta kanta dan shi kadai ne option dinta yanzu bata da wani na aure dukan samarinta Yan bariki ne, lubna kuwa Dole ne ma ta rama abinda ta mata ko yan dabba sai ta haya sun rama mata.

Sai da taje gidansu ta tuna mukullin na cikin akwatinta wayarta ma na gidan,sai makota ta Shiga dan ta Kira mahfuz ta gaya masa ya kawo Mata akwatinta da mukullinta a ciki da ace tasan Lubna zata mata irin wanan dukan da bata soma zuwa gidan ba,bata san Mai ya hana ta rama dukan da ta mata ba har ta bari ta Mata irin wanan dukan,Koda ta Shiga gidan makotan mamn khairat sallati tayi ta sanar da ubangiji tana tambayarta hatsari tayi, gyada Mata Kai kawai tayi akan hatsarin tayi dan shine karyar kawai da zatayi,dan ba mai yarda dukan ta Sha haka a wajen siririya da bata kai.ta kauri ba,wayar mmn khairat ta karba ta saka lambar mahfuz sai da ta Masa miscal uku kafin ya d’auka Yana Jin muryarta ya kashe wayar,take ta sake kiransa amma haka yayi ta ringing bai dauka ba sai text ta masa akan kayanta da mukuli.

Bata san Mai yasa mahfuz yake neman wulakanta ta ba,bayan uban dukan da ta sha awajen lubna a yanzu ya Kamata yafi kula da ita ya turo kudin aurenta gidansu,sai gashi a madadin kulawar nema yake ya juya Mata baya,haka ta rike wayar tana tunanin zai Kira,bayan minti goma sai ga sallamar almajiri da akwatin ta tayi sauri ta mik’e ta leka waje ko zata ganshi dan tasan dole shine ya kawo Mata kayanta.

Sai dai babu shi babu dalilinsa jiki a sanyaye ta ja akwatin ta bayan ta bawa mmn khairat wayarta ta bude gidansu ta shige dole ta zauna a gidan ita kadai har sai sun dawo daga aikin Hajjin.

Mahfuz

Ji yayi Kamar ya rabu da K’aya a lokacin da Hadeeza ta ta tafi,a lokacin da ta kirashi dama Yana gida sabida ya kwashe kayanta ya Kai Mata sai gashi ta kirashi duk abinan da ya faru gani yake ita ta jawo Masa,balain haushinta Yake ji,duk kayanta ya tattara mata nesa da gidan ya tsaya ya samu almajiri ya bashi akan ya Kai gidan dake jikin gidansu dan yasan Dole tana can, bashida burin daya wuce ya samu ya shawo Kan lubna,indai Lubnar daya sani ne yasan wuyanta su keb’e ya marairaice Mata,da kwarin gwiwarsa ya Kara wanka ya saka sabon kayan daya dinka na sallah,ya nufi gidan ya Usman ya riga da yasan Mai ya kawo shi hakane yasa basu wani b’ata lokaci ba suka nufi gidansu Lubna,a k’ofar gida Suka tarar da zainab na zance kanwar lubna,bata ko kalli mahfuz ba iya ya Usman din ta gaisar yace mata ta musu iso wajen mahaifiyar su Suka zo dan mahaifinsu ya dade da rasuwa,kuma bata sake aure ba.

Mahfuz kuwa ganinsa a k’ofar gidansu lubna Kuma sai duk yaji hankalinsa ya tashi dan baisan Mai zai tarar ba.

Gabansa ne ya hau faduwa a lokacin da suka shiga gidan har palon mahaifiyar lubna da aka fi Kira da Aunty nurse ita kadai suka samu a palon da alama da baki a gidan sabida ranar take sallah suna Kuma jiyo hirar mutane a dakunan palon.

Mahfuz sai wurga Ido yake yaga ko zai ga lubna daga yanda Aunty nurse ta amsa gaisuwar shi sai yaji jikinsa ya Kara sanyi ya sunkuyar da kansa Yana Jan ya Usman na mata bayanin basu dadin abinda ya faru ba,ya hau bada hakuri yana a dubi zuriar dake tsakani.

Aunty nurse bata katse shi ba har ya gama kafin itama tayi gyaran murya tana “Abinda Mahfuz yayi ya munana,ba uwar da zaa yiwa yarta haka bata ji zafin abinda aka mata ba,kafin ya Kai budurwarsa gidan ta sha dan min korafin wayar da yake yi da budurwa a cikin gidanta,har barota yake yi a daki ya fita dan kawai yaji muryar budurwarsa wlh idan ta fadamin hakuri nake bata, tana ta Kai zuciyarta nesa,a iya sanina basu wani Dade da Aure ba da har ta cancanci haka daga wajensa iya nan bai ishe shi ba sai gashi ya dauko budurwar ya kawota har cikin gidansa ya zuba karyar Yar uwar abokinsa ce tsakani da Allah yayiwa yarinya nan adalci duk macen da mijinta zai iya Mata haka wlh ba kaunarta yake ba,dan haka a ganina kuyi hakuri yaje ya auri wancan din dan yafi kaunarta,ita Kuma Lubna Allah ya mata zabin daya fi alheri”

Mahfuz nasan baiyi daidai ba,abinda yayi ba abinda zaa yi saurin mantawa bane ko a yafe,amma idan kuka tuna Allah ma muna mishi laifi ya yafe Mana Ina ga mu Yan Adam,dan Allah dan annabi kuyi hakuri”

Mahfuz baki ya sa ya hau bada hakuri shima

Aunty nurse ajiyar zuciya ta sauke tana “ba fa nice lubna ba idan lubna taga zata koma bazan hanata ba dan haka bari na turo muku ita”

Ta mik’e ta bar palon ta shige daya daga dakunan dake cikin palon.

Lubna

   Nayi kukan fili nayi na zuciya har na gaji,nasan daga jiya zuwa yau sai da jinina ya hau, duk abinda ya faru dawo min yake kawai a kaina daga lokacin da Hadeeza ta taka kafarta zuwa gidana har jiya da ya kasance min bak'ar Rana, mahfuz yaci mutuncina ya wulakanta ni da yanzu asirinsu bai tonu ba har ta samu ta tafi,da ahaka Zan saki baki ya aurota bayan ta gama sanin komai nawa sai a yanzu na tsani halina na saurin sabo da mutum Koda a ranar na fara haduwa da mutum,Banda mmn Iman ta kwabeni da komai nawa Zan kwasa na fadawa Hadeeza,Ina Jin Haushin mamn Iman har a cikin zuciyata da ace ta fadamin tun wuri da Hadeeza bata Dade a gidanan haka ba,tsabar munafirci mahfuz ko kallonta baya yi Ina murna ba ruwansa ashe yaudarata suke har abin ya Kai ya sakamin magani a lemo,a yanda nakejin zuciyata bana Jin akwai Wanda na tsana kamar mahfuz domin ya ci amanata,Ina matarsa ya hadani da dubu biyar ya bawa budurwarsa Dubu ashirin,wlh ko zaa na rantse min mahfuz zai iya kusanta kansa ga zina karyatawa zanyi,sai gashi a cikin gidana yaje ya kwanta da Hadeeza Ina can dakina ya bugar dani Ina bacci.

Mummy gajiya tayi da rarrashina ta hau ni da fada akan Kar naja wa kaina wani matsalar akan abinda ya riga da ya faru ya Kuma wuce dan kuka da saka damuwa a zuciya bashi zai canza komai ba.

Hakane yasa na koma kukan zuci,da ciwo Wanda ka aminta dashi ka bashi Amana ya maka irin Wanan cin amanar.

Shigowar Mummy data zauna a gefena da Sam bansan da shigowar ta ba sai da ta zauna a gefena na dawo daga tunanin dana tafi.

Ido ta zubamin har sai da na sunkuyar da kaina
“Haba Lubna wai bazaki sasautawa kanki bane Kinga yanda Kika rame daga jiya zuwa yau haba dan Allah dan annabi so kike ki mutu da bakin ciki ko abinda ya faru ya Riga da ya faru ba abinda zai iya canza hakan nasan da ciwo amma haka zakiyi hakuri ki fuskanci kuma gaba Aure gabad’ayansa dan hakuri ne,duk wata macen da Zaki gani a gidan mijinta da nata kalar jarrabawa da take fuskanta ke naki jarrabawar kenan,dan haka kiyi addua Allah ya baki ikon cinye wanan jarrabawa”

Jinta kawai nake dan gani nake ba Wanda ya Kai nawa zafi

“Kije Palo yayan mahfuz na kiranki”

“Mummy wlh bazan koma wa mahfuz ba na gama Zama dashi idan ma hakuri yazo bani gwara kar ya wahalar da kansa dan na Gama auren mahfuz yaje can ya karata da Hadeeza data fiye Masa ni ya Aiko min da takadar da ta cikin ruwan sanyi idan ba haka ba wlh hisba Zan Kai shi Kuma na Kai shi Kara kowa sai yasan mai ya aikata”

“Ki tashi ki saka hijabinki duk sai ki fada masa nidai bazan miki dole ba amma inaso kisan indan Zama bai Kare a tsakanin ku ba haka Zaki hakura ki koma ana abinda yafi wanan ma a koma a cigaba da Zama”

Zuciyata tafasa take har nasa ka hijabina bana san ganin Wanda ya danganci mahfuz amma gwara naje idan Yana tunanin dan ya turo yayansa zan hakura toh yayi a banza ba abinda zai taba mayar dani gidansa.

Sai dai ga mamakina Ina fita naga ashe har da mahfuz yazo,hada idon da mukayi dashi yasa na watsa mishi wani mugun kallo Ina Munafiki kawai ni nasan yajini haka ma yayansa da isana wajensu na samu waje na zauna banso ma gaida yayansa ba amma sam sai naji bazan iya k’in gaishe shi ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button