BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

MAHFUZ

Tunda suka dawo gida yake gwada lambar Hadeeza yake jinta a kashe,ya dubata ta WhatsApp nan ma Bata hau ba ya rasa duk Mai ke mai dadi,yasan fushi tayi sam bai so yau baije wajenta ba,dan shima ji yayi Kamar ya dade bai ganta ba,burinsa bacci ya dauki lubna ya fita waje ya kirata a waya idan yaji a kashe ya kira Ameera kanwarta,muryrta da zaiji kawai zai saka ya samu nutsuwa sai dai lubna kankame shi tayi taki barin jikinsa abu kadan sai yaga ta bud’e idonta a haka ya kwanta kamar yayi kuka baccin Kuma yak’i daukarsa.

Allah Allah yake gari ya waye idan ya fita massallaci ya kirata a waya.

Wajen tara yaje gidan nasu.

Kiran sallahr asuba a kunnensa hakane yasa ya mik’e da sauri ya fada bandaki ya daura alwala a daidai lokacin da Lubna ta mik’e zaune itama tana yamutsa fuska

“sannu ya jikin naki”?

“Wlh har yanzu ciwo yake min ga kaina Kamar ya rabe gida biyu dan Allah ka zauna kaja mu sallah ba sai kaje massallaci ba”

“Haba Lubna jiya ma fa banje massallaci ba ai ana iddar wa zan dawo bari naje”

Yace da sauri tare da yin waje ya jefa wayarsa a aljihunsa.

Na tabe baki dan nasan Kiranta zaiyi a waya,yau ma bazan bari yaje ko’ina ba

Sai dai mayyar taci kanta,na tsaya ma Ina neman dorawa kaina hawan jini bayan ga hanyoyi nan da Zan bi wajen rabasu,yanzu wayarsa ta kara zuwa hannuna lambarta zan d’auka

Bai dawo gidan ba sai wajen shidda da rabi.

Daga yanda naga fuskarsa ba walwala nasan ko bai samu yin waya da ita ba ko Kuma ta zazzage shi Kamar yanda nake fata da Addu’a.

Ban koma bacci ba na dafe marata na fara wash wash,ya dafe kansa Yana “Lubna wanan wane irin ciwon Mara ne”

Ban bashi amsa ba na hau matsar kwalla.

Mahfuz kamar ya sa kuka dan bakin ciki,dan Yana ta Kiran Hadeeza a waya bata d’auka ba,karshe sai text tayi Masa da Allah ya hada kowa da rabonsa bazata iya ba tunda matarsa ke controlling dinsa.

Ya Kira dan ya bata hakuri Sam taki dagawa,bashida burin daya wuce tara yayi yaje gidan nasu.

Sam bazai iya hakura da Hadeeza ba Yana jinta a ransa ba abinda yake Balain so da ita sama da shagwabarta ko ba’a fada ba yasan idan ya mallaketa zai Sha soyayya sai gashi yau ma Lubna na neman hana shi fita.

magungunan ta ya d’auko mata ya siyo kayan shayi ya hada mata.

Sai dai Koda ta Sha bata fasa ihun ciwo mara ba,Yana ji Yana gani Lubna ta dabaibaye shi bai samu ya fita ba a ranar.

Hadeeza kuwa ta Kara cika tayi fam tana ganin wulakanci mahfuz din ke san yi Mata ta dauka da ta Masa text din zai zo gidansu da sassafe sai dai ko keyarsa bata gani ba.

Sam ba walwala a fuskar mahfuz har wani tsawa tsawa yake min idan zaiyi magana hannunsa manne da wayarsa nima bakin cikin duk wanan abun akan wata can a waje ya keyi dan kawai bai samu fita wajenta ba,har mamaki yake bani wlh bantab’a zaton haka daga wajen sa ba,
banga ta Zama ba ko Ina so ko bana so dole gobe zai fita Kuma yaje gidan nasu sai dai Allah ya kawomin mafita.

Daddaren ma ban bashi space ba haka.na manne Masa banga Kuma alamar zai fita waje waya ba sai tsaki da nakeji yanayi akai akai.

Washegari kuwa da sassafe ya fice daga gidan kamar akan Kaya yake mahfuz da ni nake tilasta.masa fita sabida kar ya makara sai gashi yau wata ta d’auke masa hankali koma wacce yarinya nan ban yafe mata ba na share hawayen daya zubomin na dauki wayata dan na Kira Mahaifiyata ita kawai zan Kira na samu kwanciyar hankali dan nasan zata bani shawarwari masu kyau.

Mahfuz

Dak’yar ya samu Hadeeza ta fito dan sai da yayi ta turawa gidansu Tama k’i d’aukar wayarsa.

Koda ta fito shi kadai ya hau maganar sa Yana bata hakurin dalilin dayasa bata ganshi ba Lubna ce bata da lafiya kwanan su biyu a asibiti bada gangan yak’i zuwa ba

Sai a lokacin Hadeeza ta kalleshi idonta cike da kwalla tana “Mahfuz Ina kaunarka amma ya zama dole na hakura da Kai dan na riga da nasan b’atamin lokaci kake,wlh bazaka iya Aurena ba,bazaka iya rik’e Mata biyu ba,dan kana balain tsoron matarka mahfuz zagi da cin mutunci haka ta zuba min sau uku kenan tana zagina da iyayena har karuwa tace min idan har bata da lafiya zata zageni ne”?

“Wlh da gaske Lubna bata da lafiya ko dai wata ce ta kiraki ta zageki matar da bata da lafiya taya har zata kiraki ta zageki”?

“Hmm Mahfuz kenan karya Zan Mata kenan wlh Azeem bamu dade da waya da kai ba na sake kiranka ta d’auka ta hau zazzagina har da cemin Kai ba sona kake ba,na like ma Ina ta dafa maka abinci Kamar wata matarka”

“Ikon Allah Mahfuz yace tare da d’auko wayarsa ta Shiga call log na ranar asabar din sai dai Sam bai ga Kiran Hadeeza ba dan suna waya yake goge lambar yanzu ya haddace lambar baiyi saving a wayarsa ba har wane lokaci Lubna ta daga wayar tayi zagin bayan yazo fita ta fara ciwon maran

“Wlh Kinga banga Kiran naki ba”

“To na mata karya Mahfuz”

“Ba haka bane bance kinyi karya ba amma kiyi hakuri dan Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu”

Dak’yar dak’yar ya samu Hadeeza ta hakura Inda yace Mata ta daina kiransa ta bari ya ringa kiranta da kansa gudun sake faruwan hakan da haka Suka rabu akan zata aika Masa abincin Rana,dan ba karya Yana Jin dadin abincin ta sosai.

Yana isa office Kiran lubna na shigo wa wayarsa sai daya zauna ya daga wayar yana tunanin ko wani matsalar ne ya taso,ga mamakinsa Yana dauka lubna tambayar sa tayi ko yaje office lafiya dalilin dayasa ta Kira kenan.

Murmushi ya saki Suka dan tab’a hira da ita kafin ta Masa sallama.

Yana kashewa ta turo Masa kalamai masu balain Dadi ya hau mamakin Kira da text din da ta masa bata Saba da Masa hakan ba.

LUBNA

Shawarwarin mahaifiyata na dauka,na zage damara wajen San na dawo da hankalin mijina kaina,hakane yasa muna gama waya da ita na kirashi a waya naji ya Isa office d’insa kalau.na Kara da Masa text dan mahaifiyata tace na dage da haka,da rana ma sai da na kirashi na sake Masa text Inda ya hau tsokana ta Wai ko dai soyayayar ce yau ta motsa min.

Murmushi kawai nayi nace Masa ee.

Tunda ga lokacin ban Kara ganin tsinaniyar na kiransa ba,har wayarsa na bincika daya shiga bandaki dan naga ko zan samu lambarta,sai dai na gama dube dubena banga lambarta ba.

Ba karamin danne zuciyata nake ba dan Yana yawan fita wayar daren Koda kuwa a kirjinsa nake zai kwantar dani ya fita.

Na rasa mai yake nema a wajen wata,nasan da kunya yanzu ya ce zai Aure ko shekara biyu ban rufa ba.

A cikin wanan yanayin cikina ya Shiga wata na tara dama mun riga da munyi dashi Ina shiga watan haihuwa na zan koma gida har sai na haihu,dan sai na fi samun kulawa a wajen mahaifiyata tunda haihuwa farine,ji nayi Kamar na fasa tafiya gida dan nasan yanzu mahfuz zai baje kolinsa wajen waya da budurwarsa a baya yakan ce jina kawai yake bazan je gida wanka ba,sai gashi shine Kan gaba wajen hada min kayana.

Ko da nayiwa mahaifiyata magana fada ta rufeni dashi akan na fiye kishi na watsar da komai na ringa kyautata wa mijina zato.

Da haka na tattara na koma gidan mu amma hankalina na wajen mahfuz,haka zuciyata zata tayimin sake sake akan Yana can Yana waya ko ya tafi zance take Zan kirashi a waya tunda bana nan dani.ya Kamata ya ringa hirar.

Muna cikin wayar ba dadewa zaice min zai kwanta bacci yake ji.

Bayan Yan mintina idan na kirashi zanji alamar Yana waya haka.zan cika fam.idan ya biyo Kiran sai yacemin da Wani yake waya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button