BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Wani mugun kallo na watsa masa na kwanta akan gadon dan na dawo gida kenan,tunda abinda yakeso kenan na bar gidan

Ganin na share shi yasa ya fice daga d’akin a daidai lokacin da mahaifiyata ta kirani Ina dagawa na bata labarin duk abinda ya faru na kara da “tunda har dan.bana gidan take kawo Masa abinci har gida gwara na dawo gidana mummy Nagaji yarinya Nan so take ta zautar dani”

“Ke dai ba bazaki bi komai a hankali ba Zaki kuwa dorawa kanki hawan jini yanzu ke da kika je kinganta da idonki,a gaskiya kishin naki ya Miki yawa dole ki daura aure da hawan jini kuwa, nace kiringa bin komai a hankali,idan har namiji ya fara kulle kullen nan, wlh baki Isa ki Hana shi ba ko dafa kanki Zaki ringayi kina bashi Yana ci,wanan haukar kishin da kike sai dai yasa ma kifita a ransa kuyita fada dashi,yaji ya daina ma Jin dadin Zama dake a karshe ma ya fara Shirin auren amma tunda kin k’i bin shawara ta shikenan Anjima zan turo miki zainab ta zauna dake har ki haihun Allah dai ya kyauta”

Daga haka ta kashe wayar

Mahaifiyata bazata Gane halin da nake ciki ba ni nasan wanan yarinya da ta likewa mahfuz idan har banyi dagaske ba idan ni ban hanata shigowa ba fitar dani zatayi.

Badan babu kyau zubar da abinci ba naso na zubar da abincin a karshe na bawa almajirai narasa Ina Iyayenta suke suka barta take aikin dafawa saurayi lafiyayyen abinci haka,waya sani ma ko zaman kanta take Yar iskar.

Idan ferfesun mahfuz keso nima ya ringa siyowa yaga idan ban masa ba,duk bakin ciki da takaici ya cikani.

Koda na Shiga gidan mmn Iman masifa ta hau yi tana “da nasan Zaki Kira mijinki wlh Tallahi da ban kiraki ba,Haka kawai kin zubar min da mutuncina yanzu zai ringa mun kallon munafika,ke sam baki iya ba da so kike ki tabbatar ko ki kamashi,ai da baki kirashi a waya ba da muka gama waya dake sai kizo ki ritsa shi gajen hakurinki ya Miki yawa”

“Hmm mm Iman bazaki gane ba,kisa kaina a matsayin kece na kiraki nace ga budurwa ta shigar Miki gida baban iman na Nan wlh abinda nayi zakiyi”

“Hmmm ai shikenan Allah dai ya kyauta”

“Dan Allah baki ga fitowarta daga gidana ba Naga dai kayan abinci bansameta ba”

“Ya zaayi ma kisameta kiringa da kin kirashi tab a gaisheki ni banga kowa ba dan gida nayi shigowa ta da mijinki ya rufeni da masifa na hada Masa munafirci”
“Na Shiga uku mmn Iman ki kawomin agaji wlh yarinya Nan so take ta kwacemin miji ta k’arfi da yaji”

Shawarwari mmn Iman ta hau bani akan na ringa daurewa Ina danne kishina zuwan zainab kanwata yasa nayi Mata sallama muka koma gida ta dora Mana abincin dare Ina ta tunanin Inda mahfuz yayi.

Mahfuz kuwa Yana barin gidan, gidansu Hadeeza yaje.

Da isar sa ta fito fuskarta a hade

Mahfuz kuwa Sam bai lura da fuskarta ba shigar da tayi ne ya d’auke masa hankali dan indai lafiyayen namiji yaga a yanda yaga Hadeeza dole yaji ya harba

Farar doguwar riga ta sa dayaje mata har kasa kana iya hango duk undies dinta har kalarsu.

Yawu ya hadiye ya daure ya d’auke idonsa daga kirjinta Yana k’ok’arin Magana tace “Mahfuz idan har kasan kana Sona ka tura manya gidan mu ka daina b’ata mun lokaci a gaskiya Nagaji dan bazan zauna na ringa wahalar da kaina akanka alhalin ba Aurena zakayi ba,dan a yau na Kara tabbatar wa da cewar tsoron matarka kake ji bazaka ma iya Kara auren ba Ina kuwa dalili wlh indai dagaske kake.kana sona kazo ka samu babanmu idan Kuma kasan matarka tsoron ta kakeji bazata barka ka Kara aure ba tom sai mu hakura da juna dan a yau ka tsoratani”…….

mg’s skincare

Shin Ina matan suke????️????️????️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi????????
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg’s organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum????hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg’s b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki????
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi’iznillah sister’s duk Wanda yayi using mg’s sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy ????ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg’s skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg’s babushi akasuwa????
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go????
Then @mgs skincare gat you covered ????
Now is time to glow????
Pamper ur skin????
Shine like bride????????♀
Glow????♀️

???? tested nd trusted????
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
BUDURWAR MIJINA

         *NA SADNAF*

E.W.F.

PAID BOOK

PAGE 7

      Wlh idan Kika ce Ina tsoron matata mamaki kike bani,haba Hadeeza karki manta fa gidan ta kikaje Taya zan bari tazo ta Sameki ai sai tayi mana wani fassarar,kamar ace ke yanzu muyi aure bakya nan kizo ki tarar na kawo mace gidan ya zakiji?ai ba batun tsoro bane,sanan zancen na turo  mubi komai a hankali na samu na shirya a tsanake ,tunda kinsan ba yaudararki zanyi ba, idan har gurin manyan naki kikeso naje zanje na same su su san kina da tsayayye Nan da shekara mai zuwa sai a saka mana rana"

“Tabdijam Nan da wani shekarar fa kace wane shiri zakayi haka,haba Mahfuz ka duba maganar nan taka,har sai wata shekara zamuyi aure,a gaskiya yayi nisa ni kaga idan har tunanin kashe kudi zakayi wajen yimin lefe ni na yafe lefen kayimin daga baya,wlh mahaifina kullum sai ya bugowa Abba waya akan na fito da mijin Aure,ni banga dalilin da baza muyi auren ba yanzu,dalili daya kawai zaka cemin zai saka kace min bazaka iya Kara aure ba tsoron matarka kakeji mahfuz a gaskiya lokaci yayi da zaka daina mata b’oye boye ka fito ka fada mata matsayina a wajenka,ni ka fara so kafin ka sota,ni ka fara sani kafin ka santa banda dai kaddara wlh da bata Isa ta sameka ba”

“Ban da dai san zuciya irin naki Zaki ce koma Mai yafaru ai ke Kika jawo Hadeeza Kinga koma mene bai dace kiringa ganin laifina ba,a lokacin da na so aurenki ai k’i kikayi Kika ringa wulakantani wlh ba dan Ina kaunarki ba kinsan ko saurararki bazanyi ba a lokacin da naso muyi aure k’i kikayi sai yanzu ni Kuma da na riga da nayi auren zaki sakoni a gaba”

“Kayi min gori mahfuz kayimin gori dan nace kazo muyi Aure”

Hadeeza tace idonta cike da kwalla

“Nifa ba gori nayi miki ba Wai inaso ki daina ganin Kamar k’in fitowa nayi na aureki zan aureki idan Allah ya yarda ki dan bani lokacin yanzu dududu shekara daya da wata takwas Aurena Kinga ya Kamata ace na bari na shekara biyu kafin na koma musu da zancen Karin aure”

“Hmm”

Kawai Hadeeza tace tana share hawayen daya zubo Mata

“Haba Sweetyna kiyi hakuri dan Allah nifa bana san haka”

“Yanzu dai yaushe zaka zo ka samu Abban mu yasan da maganar taka,zaka iya turowa fa inya so sai a saka shekara guda Kamar yanda ka bukatan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button