BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

“Ki bari next week zanzo na same shi amma batun turowa ki dan bani lokaci Hadeeza wai ko dai yarinya auren take so hakane”
Yace yana kanne mata Ido daya
Ta sunkuyar da Kai tana “toh laifi ne dan naso auren masoyina”
Murmushi Mahfuz yayi suka cigaba da hira a bai bar gidan ba sai da ya take cikinsa da tuwon shinkafa miyan kuka dayaji nama.
Ba laifi kanin mahaifin Hadeeza nada rufin asiri Yan boko ne shiyasa basu damu da yanda Hadeeza ke aikin girki ba akwai komai a gidan enough,shi kansa mahfuz din da kwadayin yanda take zuba girki da namomi kaza kifi da sauransu yake, har ya Kai ma ko Lubnar tayi abinci sai yaji Kamar girkin nata bai Kai na Hadeeza dadi ba,bai sani ba ko dan ba kasafai yake Kai naman ayi girki dashi bane, Lubna ce ma ke dan k’ok’arin dafa abinci da Naman.
Wajen karfe goma ya iso gida tun kan ya shiga gidan ya had’e rai dan Yana so ya nuna wa Lubna yaji Haushin zargin da ta masa dazu ya hada Mata da borin kunya,har ga Allah ya kanji Kamar baya kyauta Mata toh ya zaiyi shima zuciyarsa batayi shawara dashi ba ya fara san Hadeeza duka su biyun gani yake bazai iya rayuwa batare dasu ba.
A Palo ya tarar da Lubnar da tsinin ciki ta baje a kasan kafet Zainab kanwarta na dadana mata kafa da ya kumbura,take yaji tausayin ta ya Kuma ji dagaske bai kyauta mata ba ko Yaya dai cikinsa take dauke dashi kulawarsa tafi bukata yanzu.
Gaisuwar zainab din da ta mik’e da sauri ya amsa,ta nufi d’akin bakin
Ya zauna shima a tsakiyar kafet Yana neman kwayar idon lubnar da ta sunkuyar dakai tunda ya shigo bata daga kanta ta kallesa ba.
“Uwar biyu fushin kike dani kenan”?
Ko kallonsa banyi ba na janye kafata daya fara k’ok’arin d’anna min, ko ganinsa bana san yi dan na riga da nasan wajen dai budurwarsa yaje da ta fini mahimmanci,a yau ma da na dawo gidana sati biyu rabona dashi,ba dokin zuwana yake ba,ba nice a gabansa ba budurwarsa ce a gabansa,wlh a baya ko fita nayi haka zai ta jera min Kira Yana tambayar na dawo,bazai daina kirana ba har sai na dawo gida hankalinsa zai kwanta,ni nake tilasta masa ya fita ma,yayi ta mitar korarsa nake, soyayya muke yiwa juna mai wahalar fassaruwa,mahfuz yaji dani ya soni,sai gashi lokaci guda ya canza min duk wanan soyayyar Yana neman rushewa a gaban idona, tunanin da nayi yasa hawaye zubomin na share hawayen naji saukar hannunsa a kumatuna ya dago fuskata
“Lubna dan Allah ki daina sawa kanki damuwa wlh tallahi Ina kaunarki kina nan da matsayin ki a zuciyata,ki cire komai a ranki ni mahfuz nakine ke kadai”
“Mahfuz wlh idan har kana kaunata Kamar yanda kace bazaka so bacin raina ba mai na rage ka dashi dan Allah,dududu yaushe mukayi Aure da zaka fara kula wata mahfuz Ina alkawarikan da kayi min,ko shekara biyu mahfuz har yanzu bamu yi da Aure ba har wata ta d’auke maka hankali akaina baka iya bacci idan baka ji muryarta daddare ba,har abincinta yafi maka nawa dadi, haba Mahfuz a haka kace kana kaunata,sati biyu rabona dakai amma na dawo ko a jikinka ka fice sai yanzu zaka dawo?Mai na maka dana cancanci haka daga wajenka dan Allah”?
Na karashe tare da fashewa da kuka ya jawoni da sauri ya rungumeni tunda na fara magana Naga ya kyab’e fuska da alama maganganu na sun shige shi sai bubuga bayana yake Yana bani hakuri na janye jikina daga nasa Ina”Mahfuz Dan Allah wacce ita?
“Dan Allah kibar zancen nan”
“Dan Allah ka fadamin wacce ita yaushe kuka hadu”?
“Tsohuwar budurwa ta ce lubna mun dade da haduwa da ita,Allah ne yayi bantab’a baki labarinta ba dan har ga Allah a lokacin da na had’u dake na shafe babinta a rayuwata”
“Mai yasa baka aureta ba Mai ya rabaku”?
“Wai Dan Allah Mai ya kawo tambayoyin Nan lubna”?
“So nake na san matsayinta a wajenka Mahfuz”
“Allah baiyi munyi Aure ba lubna sai a yanzu kaddara ta sake hada mu”
Shiru nayi ina jin wani irin abu ya tokare min makoshi bana jin ma zan iya maganar so nake na auna maganganun sa
“Wlh Lubna ita ta dawo rayuwata ta nace min na rasa yanda Zan yakice ta”
“Kana santa Mahfuz ni ba mahaukaciya bace wlh nacewa juna kukayi,ba itace ta nace maka ba,yanzu aurenta zakayi kenan”?
Na zuba masa Ido gabana na faduwa
“Lubna mu bar zancen nan kema ko yanzu aka ce miki zanyi Aure ai zaki karyata kin isheni rayuwa”
“Na isheka rayuwa kake kula wata yaudarar ta kake ko watsewa kuke idan har ba aurenta zakayi ba Mai amfanin kulata ka b’ata mata lokaci mahfuz”?
Lubna dan Allah ki bar zancen nan haba kiji da cikin Nan dake jikinki muyi addua Allah ya saukeki lafiya haba Ina ta kwantar Miki da hankali kin kara dagawa kanki hankali”
Yace a d’an tsawace tare da mik’ewa tsaye
“Ga abincin ka nan ko kaje wajenta kaci”?
“Lubna dan Allah kidaina min maganar wata idan har kina san mu daidaita dake wai wane irin dabia Kika samo haka mara kyau ni nace miki naci abinci”
‘toh zauna kaci abincin”
Tsaki yayi ya zauna duk da a koshe yake ya bude flasks din ganin faten doya ne yasa ya zuba kad’an ya fara ci yanda ya had’e rai yasa ban sake magana ba har ya gama cin abincin ya kwashe komai ya Kai kitchen.
Ya dawo ya taimaka min na Mik’e muka Shige d’akin mu.
Koda ba kallonsa nake ba idona na kansa Yana fitowa daga wanka ya kashe wayarsa ya jefa a side drawer ya Kwanta.
Nima nayi Shirin kwanciya da maganganu a bakina amma akan dole na hakura na kwanta a gefensa.
Ya mirgino kusa dani,muka faranta wa juna bana iya kwanciya ba tare da nayi wanka ba a dadafe nayi wanka sabida baccin daya cika idona Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani.
A zababben ciwon Mara ne ya tasheni daga baccin daya daukeni
Damko mahfuz nayi Ina sallati
Dan ciwon maran haihu daban yake kamar yanda ake bamu labari nasan haihuwa zanyi
A gigice ya mik’e Yana tambaya ta lafiya
Dak’yar na hada Masa kalmar haihuwa zanyi.
Wani irin dirowa yyi daga Kan gado ya kunna fitilar d’akin ya kalli agogo karfe uku da minti ashirin
“Bari na leka gidan Hamisu ya taimaka min da aron motarsa Ina kayan naki yake”
“Mummy ta riga da hade min shi waje daya kayiwa Zainab magana na karashe Ina Kara sallati dan ciwon gadan gadan ba kaukautawa ga wani abu Mai dumi danaji Yana bin kafata.
Mahfuz shi ya taimaka min na saka Riga da zani hannunsa sakale a kuguna kamar Mai koyan tafiya mukayi wajen da Hamisu mijin mmn iman ke jiranmu dan cewa yayi shi zai kaimu daga shi har matarsa suna da balain kirki sun san Kuma darajar makota.
Bansan sanda ma aka iso asibiti ba ban iya tafiya ba sai gado suka kawo da taimakon mahfuz suka dorani sukayi d’akin haihuwa dani zainab na biye dani Mahfuz sai sannu yake min hankalinsa duk a tashe.
Da shigar mu d’akin da haihuwata baifi minti ashirin ba.
Duk Wanda bai haihu ba ba lailai yasan darajar mahaifiyarsa ba Allah ya saka wa iyayenmu da Aljannatul firdausi banyi doguwar nakuda ba amma naci ubana bayana Kamar baa jikina yake ba.
Sai da suka gyarani Suka gyara yarinya da ta d’auko kamani na ba Inda ta baroni amma bata kaini haske ba da alama hasken babanta ta d’auko ido kawai na zuba Mata Ina Jin kaunarta har a cikin raina.
Muryar mahfuz danaji akaina yasa na d’auke idona daga kanta
“Sannu Lubna sannu da k’ok’ari wanan diyar tawa ta baki wahala”
Yace tare da daukarta yana murmushi.
Nima murmushin na sakar masa.
Bakinsa ya kafa a kunnenta Ina kallonsa ya gama ya kwantar da ita a gefena Yana “Sunanki na saka mata Allah ya Raya mana ita sai ki zab’a mata sunan da zamu ringa kiranta dashi”