BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

“Dama kinsan gidanmu ne”?

“Tunda har nasan gidanka sanin gidanku bazai min wahala ba Mama nada kirki wlh tayi min tarb’a Mai kyau da dukan alamu na samu karbuwa a wajenta ba nida wani fargaba”

“Hmmm ai da kinn fada min zakije kila akwai shirin da zanyi kafin kije din amma tunda kin riga da kinje shikenan tace na miki godiya”

“Ba wani damuwa ai nima mahaifiyata ce”

“Hadeeza”

“Naam”

“Magana nakeso muyi mai mahimmanci Ina fatan Kuma Zaki fahimceni”

Gaban Hadeeza yanke wa yayi ya fadi duk tunani take mahfuz cewa zaiyi tayi hakuri bazai iya aurenta ba bata iya cewa komai ba ta zuba Masa Ido

“Kinsan dai Ina sanki Ina Kuma kaunarki,fatana Allah ya mallaka min ke Babu yaudara a tsakanina dake,da ace bana kaunarki bana Jin zan tsaya na ringa b’ata Miki lokaci ina b’atawa kaina,saura wata hud’u na samu shekara biyu da aurena,kafin ki dawo rayuwata wlh banida wani plan din auren Mata biyu a nawa tsarin mace daya ta isheni rayuwa sai dai idan Yana cikin kaddara ta sai na Kara Aure,Hadeeza Kamar yanda Kika sani a baya ni ba wani shahararren Mai kudi bane da na tada kai,rufin asiri gareni rayuwa ta a saukake nake yinta,kina kallo ko mota har yanzu bani dashi,dama burina bai wuce idan lubna ta haihu na fara tunanin yanda Zan samu motar ba,banida wani gida daya wuce Wanda Lubna ke ciki sai wani fili da na siya nida wani abokina Abdul komai a rayuwa sai kana tsarawa yanda bazaka yi abinda zai takura ka a yanzu nauyi ya Kara hawa kaina.tunda na fara tara iyali,Hadeeza abinda yasa nake Miki wanan maganar naga kin matsu kina so ko a yayane na turo muyi aure, inaso kisan komai sai da plan bana so muyi gaggawa ko garaje,inaso mubi komai a hankali a yanzu da Allah ya kaddara Zan aureki Zan fara shirye shiryen yanda Zan zauna da Mata biyu,dan haka zanzo na samu Abban naku yasan da maganar auren a bani lokaci na samu mu tsara komai,na biyu ba zancen Ina tsoron matata bane ko wani abu,inaso mu canza taku yanda ba zaa ringa saurin dago mu ba,wayar daren nan da mukeyi inaso mu hakura da wanan wayar,
Idan na fito daga gida Zan Kira ki da kaina.

kema kinsan Ina samun sarari Ina baki lokaci sosai a wajen chatting wanan shine maganar kawai dafatan Kuma zaki fahimceni”

Ba karamin dauriya tayi ba wajen danne zuciyarta cikin yak’e tace “Na fahimceka wlh ba wani damuwa zan daina kiranka idan kana gidan kamar yanda ka bukata amma inaso kasan cewa wlh ba sharri a zuciyata bansani ba ko matarka wani abu tace maka kazo kake min maganganun nan”

“Aaa wlh ba abinda tace min kawia naga ya dace yanda nake baki lokaci itama na ringa bata lokacinta Kinga bai dace na ringa shiga hakkinta ba ko”

“Eee hakane kuma”

Tace cikin yak’e tana “yaushe zanzo barka ne kaga ya Kamata naje naga ‘yata”

“Kai aaa Zan kawo Miki ita idan ta fara wayo”

“Kasan kuwa next week su Abba zasu tafi umara wlh dukansu har da yaran ni Kuma wai na koma gida idan sun dawo sai na dawo”

“Allah sarki kice zanyi missing dinki”

“Tab ai ba Inda zani bazan iya kwana biyu banganka ba wlh”

Dariya mahfuz yasa Yana “toh ya zaayi kenan”?

“A jaka zan saka ka mu tafi can”

Hira kawai suke mahfuz Sam baima San lokaci ya ja ba sai da aka fara Kiran sallah magriba yaso daga massallaci ya wuce gida Hadeeza ta hana shi har sai daya ci abincin dare a gidan.

A lokacin daya isa gida har Lubna tayi bacci.

Zainab da Aunty Sa’a kanwar mahaifiyar lubna kuwa Suna daya d’akin Yana jiyo hirarsu.

Wanka kawai yayi yazo ya kwanta ganin Lubna na bacci yasa ya kunna data Suka hau chatting da Hadeeza da ta ajiye masa message rututu na irin kaunar da take Masa ta hada da ya turo mata hotunan baby.

Sai da ya fara Jin bacci yayi Mata sallama ya kashe wayarsa.

LUBNA

Ba laifi naga canji daga wajen mahfuz tunda na haihu,ban sake ganin yayi wayar dare ba,idan ya dawo gida baya sake fita har a raina naji dadi Inda na ringa addua Allah yasa ya dore a haka Allah yasa ya rabu da wanan tsinaniyar budurwar tasa,har bincike nayi a wayarsa na shiga message dinsa da watsapp banga alamar lambarta ba a wayanda yake Hira dasu yafi hira da Abdul na Kuma ji dadi sosai.

Ba laifi ya min dinki masu dan kyau da tsada daidai karfinsa duk da mummy ta riga da tamin dinkin fitar suna haka ma ta kusa cikowa mimi akwati da kaya.

Hankalina kwance muka Sha Suna a ranar sunar ba inda Mahfuz yaje Yana nanike dani,Muna ta hotuna.

Ko kunyar mutane bayaji da suka cika gidan,har anko mukayi dashi na wani blue shadda munyi kyau sosai Koda ba’a fada ba.

Zuwan mahaifiyarsa Hajiya Ammi da ta had’e rai tana dan harararsa yasa ya bar wajena yayi waje.

Koda na gaisheta Mimi kawai ta karba daga hannuna ta amsa gaisuwar ciki ciki nakan yi mamakin yanda take min,Banda matan yayyen mahfuz nace min haka halinta yake da nace sona ne batayi.

Yan uwana sai da suka tayani kintsa koina Kamar ba’ayi taro a gidan ba kafin suka tafi Aunty Sa’a Dai sai ta Kara kwana biyu kafin ta tafi.

Mahfuz

Yaji dadin hadin Kan da Hadeeza ta bashi wajen daina damunsa a waya suna gama chatting yake gogewa gudun kar Lubna ta masa bincike a waya ta gani yafiso ta dauka sun rabu da Hadeeza Sam bayasan ta ringa zarginsa tana dagawa kanta hankali.

Ranar suna da Mai kwalliya tazo ta rangada wa Lubnarsa kwalliya ba karamin kyau ta masa ba hakane yasa yayi ta zuba musu hotuna a wayarsa da mimi.

Hotunan dayafi kyau ya zab’a ya Dora akan status da rubutun “Allah ya Raya mana Mimi ya baki lafiyar shayarwa Rabin Raina

Ko minti biyar baiyi da sawa ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.

Bai kawo komai ba ya daga wayar

Kukanta ne ya karade wayar

Sam baisan Mai yasa ta kuka.ba hakane yasa a rude ya hau tambayarta lafiya mai ya faru bata ce masa komai ba ta cigaba da rusa kuka.

Katse wayar yayi ya haye machine dinsa yayi gidansu dan bata tab’a kiransa tana rusa uban kuka haka ba.

A lokacin daya iso gidansu sai daya dade Yana jiranta kafin ta fito idonta ya kada yayi jajjur.

Mik’ewa yayi da sauri dan ya d’auka ko wani ne ya mutu da sallati yace “Lafiya kuwa Hadeeza Mai faru

A wajen kafarsa ta zauna ta Kara fashewa da kukan

Ya zauna da sauri.yana “Hadeeza wai Mai yake faruwane”

Dagowa tayi kafin ya ankara ta jawo hannunsa ta manna a kirjinta “kaji zuciyata Mahfuz kaji yanda yake bugawa,Ina da kishi mahfuz hotunan nan daka dora ya daga min hankali mahfuz anya kana Sona kuwa”?
Tunda muke da Kai baka tab’a dora hotona ba”

“Wai wane hotone ya daga Miki hankali hoton nida Lubna ko me”?

“Gyada Masa Kai tayi har lokacin Tana kankame da hannunsa ba hotunan da sukayi tare da mahfuz ne ya daga Mata hankali ba bata kawo Lubnar ta kai haka kyau da haduwa ba,bata ga abinda zata Gaya wa Lubnar ba,sai taga ma kamar ta girmi Lubnar Sam ta kasa danne kishinta har sai data Kira mahfuz din,gani take mahfuz na iya kubce Mata kowane lokaci,tundaga lokacin daya kafa mata sharadin kiransa a waya,ta tsorata dashi,dan taga dagaske Lubna nada wani irin matsayi a wajensa abu.kadan na iya sawa mahfuz yace ya fasa aurenta.

Tsananin mamakin Hadeeza yasa ya saki baki Yana kallonta kallon Anya ma tana da hankali kuwa hoton lubna ne bataso ya dora ko me

“Yanzu ke kishin lubna kikeyi har dasu kukan ki yanzu laifi ne dan nayi hoto da matata matata ce fa ba wata ba”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button