BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

“Mahfuz bazaka gane ba nidai dan Allah kayimin alkawari bazaka rabu dani ba duk runtsi duk wuya”
“Wai duk hoton namune ya rudaki haka,lailai kinma fi lubna kishi to bakya so muyi hoton ne ko me”
“Ni ba haka nake nufi ba”
“Toh Mai kike nufi”
“Nidai kayimin alkawari bazaka rabu dani ba”
Girgiza Kai mahfuz yayi Ya hau dariya dan dariyar ma ta bashi biye mata yayi yace yayi alkawari kafin ta yarda ta cika Masa hannu tace Masa tana zuwa.
Bayan minti goma sai gata ta dawo cikin kwalliya ta Sha shadda pink mai duhu ta kashe dauri,
Da ido yake binta har ta zauna a gefensa kafadarta na guga nashi ga kamshin turarenta nan ya bade ko’ina.
Bai san mai take nufi ba sai da ta d’auki wayar ta tana “nima hotunan zamuyi naji dadi dama bamu tab’a hoto ba tace tare da daga wayar murmushi kawai yayi ta hau yi musu hotuna har tana dadafa shi kamar irin couples dinan da basu Dade da Aure ba.
Shi dai biye mata yayi sukayi tayi har da su videos sai daya gaji ya kwace wayar daga hannunta yana ya isa haka.
Jera hotunan ta hau yi status sai duk yaji hankalinsa bai kwanta da dorawa da tayi ba duk da yasan Lubna ba saninta tayi ba yanzu idan ya ce ta cire sai ta masa wani fassarar.
Yanda take wani nanarke Masa tana neman daga Masa hankali a banza yasa ya mik’e yace Mata zai tafi.
Sai da ta raka shi har waje ta Kara komawa ciki ta d’auko leda mai dan girma ta bashi tana ya kaiwa yarta.
Yakan yi.mamakin Inda take yawan samun kudin da take kashewa haka,duk da yasan shima Yana tura Mata kudi Dan Yana da acct number dinta sai dai kudin daya ke tura Mata bai Kai yawan hidimar da take dashi ba har dinkin shadda ta Masa da agogo da turare mai tsada lubna duk ta d’auka shi ya siyo da kudinsa.
Godiya yayi Mata bayan ya roketa da daina dorawa kanta wahala haka.
Koda ya isa gida a zaune ya tarar da Lubna tana shayar da Mimi yanda ta zubo Masa Ido yasa yaji duk ya tsargu sai yake ganin kamar zata gane wajen Hadeeza yaje.
“Ina ta gwada wayarka tundazu Ina ka shiga ne”?
Nace Ina Kare Masa kallo nidai duk da ban Kara Kama shi Yana waya ba idan har ya dan Dade a waje sai naji kamar zance yaje.
“Ina can gida mun hadu da Yaya Mustapha”
Ya mik’o min ledar hannunsa “ga Kaya nan inji wani abokina”
Karba nayi na bud’e na fara fito da kayan ciki,kayane masu kyau da tsada wajen kala biyar sun balain yimin kyau
“Wane abokin naka ne ya Mana abin arziki haka”?
“Baki San shi ba a wajen aikinmu yake”
“Aikuwa ya kyauta sosai kayi Mana godiya”
Kai kawai ya gyada min ya hau Wasa da mimi.
A yanzu dai Zan iya cewa banida wani matsala Ina samun kulawa sosai a wajen mahfuz, tuni hankalina ya fara kwanciya dan da alama yanzu baya tare da yarinya data so saka min hawan jini sau tari na Sha Masa bincike ban ga alamar bakon lambar da bansani ba.
A yau da nasamu sati biyu da haihuwa baifi saura kwana shidda ayi babbar sallah ba bayan fitar mahfuz wajen aiki ya kirani a waya akan Abdul Yana hanya zai zo ya shigo garin na tanade shi.
Nasan yanda Abdul yake a wajen Mahfuz aminan juna ne Yana da balain kirki Nima Ina matukar ganin mutuncinsa,baya Wasa da duk wani abu daya shafi Mahfuz duk da baya garin na haihu sai da ya hada kayan barka ya aiko Mana dashi.
Kitchen na Shiga da kaina na fara k’ok’arin dafa fried rice a cikin awa daya na kamalla komai na gyara gidan zainab bata Nan taje gida ta dawo.
Wajen karfe biyu naji sallamarsa tare da bugun k’ofar gidan.
Hijabina na saka har kasa,naje na bud’e k’ofar fuskata d’auke da murmushi.
Tsokanata ya fara yi Yana “Uwargida sarautar mata”
“Dagani ba kari insha Allahu na karashe Ina “toh ashe da amaryarka kake tafe aa lalle marhaban shigo shigo.
Nace Ina bawa macen dake biye dashi a baya fuskata washe ita kuwa sai wani sunkuyar da Kai take hannunta janye da dan madaidaicin trolley.
Suna Zama na dauko musu ruwa da lemo Ina satar kallon budurwar Abdul din bana iya ganin komai na jikinta dan hijabi tasa har kasa fuskarta ce kawai a waje kyakyawa ce ba laifi.
Mimi kuwa na hannun Abdul Yana ta mata Wasa “wato ka gaji da gorin auren da muke ma kenan”
Nace ina tsokanar Abdul daya gyarawa Mimi Zama a jikinsa Yana “Tukunna dai wlh har yanzu ban samu wacce ta kwanta min ba wanan ai ‘yar babar yayar mu ce da suke zaune a Lagos inaga mahfuz ya tab’a baki labarinta lokacin dayaje can Lagos din ko”?
“Kwarai kuwa ya tab’a bani labarin yayarka ta Lagos”
“Toh wanan yarta ce ta fari.
Ta shigo garin nan ne zatayi wani training na kwana goma,shine nace bari na kawota nan ta zauna idan ba damuwa”
“Haba haba ba wani damuwa wlh ai an Zama daya fatana dai ta saki jikinta Nan ma gidane ai”
Muka hada ido da ita ta sakar min murmushi tare da sake sunkuyar da Kai,nikam yanayin ta ya burgeni da alama tana da nutsuwa da kamun Kai.
Sai da suka ci abinci na Kai mata akwatin ta daya dakin.
Muka dan tab’a hira da Abdul kafin yamin sallama.akan goben nan zai koma ya ajiye min kudi Mai yawa na hau yi mishi godiya har bakin k’ofa muka raka shi nida ummi bakuwar da mukayi sabida tsiya irin na Abdul Ashe bai fadawa mahfuz zai kawota ba Wai Idan ya dawo na fada Masa…..
Wanan novel din na kudine a page 10 zamu gama free pages biya 500 dan ki samu kicigaba da karatunki cikin sallama tura 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko ta wanan 0000551222 Taj bank nafisa Nuhu turo da shaidar ta wanan lambar 08033719070 ko katin mtn ta wanan layin 08033719070 karku bari a barku abaya.
KAYAN MATA
Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?
Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?
Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?
Shin minene matsalar?
Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?
Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,
Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,
Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, ???? kikerewa sa’o’i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,
Munada tsumi nau’i nau’i
Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu
Akway ruwan jaraba
Ruwan Dadi
Hadin minannas
Hadin dafa kaza(manta uwa)
Hadin yar gaban goshi,
Turarukan mallaka.
Duk a farashi mesauqi.
Serious buyers call, WhatsApp 07046881166
Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagode
BUDURWAR MIJINA
*NA SADNAF*
E.W.F.
PAID BOOK
PAGE 9
Koda muka koma ciki,a kasan kafet ta zauna ta miko min hannu tana na bata mimi.
Mik’a mata Mimi nayi Ina “Mai Kika zauna a kasa ki koma ki zauna mana akan kujerar”
“Nan ma yyi Aunty ngd”
“Kai Kai sunana Lubna ba Aunty ba”
Murmushi kawai tayi ta cigaba da Wasa da mimi tana ta zuba mata kiss a fuska ni.kuwa take ta sake burgeni ni nasan Zainab gajiya tayi ta gudu toh tayi a banza tunda na samu Yar tayin hira.
Hira na fara janta dashi Ina dan jefa Mata tambayoyi duk dan ta saki jikinta,anan take fadamin ta kamalla degree dinta tana neman aiki, shine kafin su dauketa suka turota nan ta danyi wani programme a shiyarsu ta nan.