BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Tab’e baki yayi bai ce min komai ba Nima ban Kara magana ba har ya gama cin abincinsa
Ya Mike zai tafi na tafi dan na raka shi munje bakin k’ofa ya juyo Yana “Na manta ban fada Miki ba Abdul jiya yace na fada Miki wanan yarinyar ba komai ta iya ci ba ya roki arzikin a ringa tambayarta abinda zata ci ko a barta ta dafa abinda takeso dakanta wlh badan kin dage ba da sai na Masa rashin mutunci nida gidana azo ana min iko”
“Allah sarki wlh ba damuwa ai kana ganinta kasan Yar hutu ce ba irinmu da duk abinda muka samu ci zamuyi ba Tom ba damuwa ai tunda ba laifi muna da Abubuwan Yan gayu yanzu a gidan idan ma cornflask take so ta ringa Sha gashi nan”
“Ku kuka sani”
Yace a daidai lokacin da ya ida fitar da machine dinsa ya tayar ya tafi Ina daga masa hannu.
Ina komawa ciki na karasa mopping din na turara koina kafin na koma d’akin Ummi dan na tambayeta mai zata ci.
Kwalliya na tarar tanayi a lokacin da na Shiga tana ganina ta saki murmushi tana “so nake na shirya kar nayi latti”
“Kina nufin bazaki karya ba Zaki tafi nidai na soya dankali da kwai sai kayan shayi bansani ba kinaci ko bakya ci idan bakya ci sai a sama Miki wani abu dan Abdul yace Wai ba komai kike ci ba”
“Eee wlh aunty duk wani abu Mai maiko ban fiye ci ba da safe nafiso nasha corn flask haka ko bakin tea”
“Toh shikenan ki gama shiryawan akwai cornflask sai ki hada ki Sha”
Godiya tamin na sakar mata murmushi na fito.
Ban Dade da fitowa ba sai gata ta shigo da dogon hijabinta har kasa da farin glass.
Tana Zama na dauko mata kofi da cokali da tuni na ajiye Mata Madara da cornflask din
Cikin nutsuwa ta hada ta Sha sai satar kallona take narasa Mai yasa take San satar kallona.
Tana gama Sha ta mik’e da Yar Jakarta tana “Bari naje kar makara sai na dawo”
A dawo lafiya” ta fice daga gidan ni Kuma na koma daki.
Ina kwanciya mamn Iman ta hau bugun kofa tana kwallamin Kira
Ko mai take nema a wajena da sassafe haka oho na mike nayi hanyar waje……..
Karku manta a gobe zamu gama free pages insha Allahu ku biya 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko ta Nan 0000551222 taj bank nafisa Nuhu ko katin mtn a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 yanzu zamu shiga cikin labarin budurwar mijina karki sake a barki a baya
KAYAN MATA
Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?
Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?
Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?
Shin minene matsalar?
Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?
Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,
Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,
Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, ???? kikerewa sa’o’i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,
Munada tsumi nau’i nau’i
Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu
Akway ruwan jaraba
Ruwan Dadi
Hadin minannas
Hadin dafa kaza(manta uwa)
Hadin yar gaban goshi,
Turarukan mallaka.
Duk a farashi mesauqi.
Serious buyers call, WhatsApp 07046881166
Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagode
BUDURWAR MIJINA
*NA SADNAF*
E.W.F.
PAID BOOK
LAST FREE PAGE
PAGE 10
Ina bud’e kofa na yamutsa fuska Ina “Shi bawa bazaa barsa ya huta ba”
“Eee baza’a barki ki huta ba wuce muje”
Dariya nasa dan muna Yar Wasa da mmn Iman sosai muna Shiga ciki ta zauna a dogon kujera tana kalle kalle nima na zauna a kujera mai kallonta Ina “kefa wani zubin kanki ba dadi Mai kike dubawa ne”
“Mai nake dubawa kuwa so nake na tabbatar da ba kowa a gidan kafin nayi magana duk da Naga fitar mahfuz da bakuwarki”
” Ba kowa dagani sai Mimi kin samo mai zafi kenan”?
Nace Ina maida hankalina gabadaya kanta dan Naga alamar da magana tazo Mai mahimmanci
“Eee da magana nazo Kam amma nariga da nasan halinki gajen hakuri baki iya bin komai a hankali ba”
Mik’ewa nayi da sauri na koma gefenta na zauna Ina “Mai ya faru mmn Iman bani labari”
“Wai ya kuke da bakuwar nan da tazo jiya”?
Yamutsa fuska nayi Ina “Wai Ummi”?
“Eee”
“Ba dangi iya babu na baba Ina Abokin Mahfuz Abdul da nake dan baki labarinsa Yana yawan yi Mana aike har kike cewa idan kina da kanwa da kin bashi”
“Eee na tuna shi”
“Toh yarinyar yayarsa ce suna zaune a Lagos tazo nan wani program ne na sati daya ko kwana goma yace ne jiya dai da kansa ya kawota,lafiya kuwa kike tambayeni”?
Ajiyar zuciya ta sauke tana “Ni yarinya Sam ban yarda da ita bane naga tana ta Abu kamar mara gaskiya,kinsan jiya nan Ina zaune wlh satar kallonta kawai nake ni a idona ma sai naga kamar kallon banza take miki kasa kasa”
Dariya na kwashe dashi Ina “Kai mmn Iman abin naki har da sharri yarinya da ko kallona bata iya yi ga kunya”
“Kefa dadina dake hauka wlh Ina miki maganar serious shi Abdul din duk wayanda ya sani anan ga gidansu mahfuz Mai yasa bazai kaita can ba sai nan, Taya zaa kawo Miki tsalleliyar budurwa irin wanan haba mana”
“Wani kusancin ai yafi wani mmn Iman shiyasa ya kawota nan Allah sarki kawata tsoro kike zaa kwace mun miji ko”
Na kyalkyale da dariya mmn Iman ta zuba tagumi tana kallona
“Kwantar da hankalinki ba Mai kwace min miji mahfuz Zan iya rantse Miki ba lailai yasan kamaninta ba dan ko kallonta bayayi,itama ba lailai tasan kamaninsa ba dan tana ganinsa take sunkuyar da Kai”
“Tom ai shikenan amma nidai ban yarda da ita ba wlh masu shiru shiru da saka hijabin nan wlh munafikai ne,a idona jiya ta Miki kallon banza ke Kuma ga saurin sakin jikin balai name kike wani janta da hira”
“Kai mmn Iman bakonka annabinka so kike na hade rai,nifa kinsan ban iya wulakanci ba”
Mmn Iman shiru tayi dan ba iya maganar da ya shigo da ita kenan ba,jiya taji mahfuz nata waya a k’ofar gidan ta har makalewa tayi a jikin kofa dan taji Mai yake cewa soyayya yake zubawa a waya da wata taso ta fadawa lubna ta saka mishi ido amma tuna haukar data Mata kwanaki yasa ta hakura”
Maganar lubna ya katse Mata tunanin da take
“Mmn Iman mun zama yan gayu fa jiya Kinga siyayyar da Mahfuz yayo Mana kuwa zomuje kitchen kigani”
Na jawo hannunta mukayi kitchen din Ina bata labarin abubuwan da mahfuz ya siyo Mana jiya.
A bakin kitchen ta tsaya na hau nuna Mata ta ringa gyada Kai dan ita dama mijinta na siyo mata nice dai bakuwa da aka siyomin a Karon farko.
“Aaa lailai kam kun zama Yan gayu kin huta da siyan kanana Yan sachet nidai ko dan bakuwar aka muku siyayya haka sabida Kar ta Raina ku”?
“Ko daya fa tazo dai a daidai ne wani kudi suka samu yayi Mana siyayyan,dazun Nan yake cemin ya bada kudin ragon layya,yau saura kwana biyar fa Mai da me ya Kamata muyi?
“Mai kuwa zamuyi daya wuce ayi yanka mu soya ban karya ba mallama zubo Mana dankalin muci”
Ta koma Palon na juyo dankalin a plate da kwai flask din tea din na Palo da bredi Muka fara ci
“Kiringa Jan class dinki lubna ki daina sakar wa wanan bakuwar taki fuska kina zuba a gabanta haba jiya kin bani haushi wlh banda kin dage da a shawarce kin yiwa mahfuz magana ta koma gidansu wlh tunda akwai Yan mata acan itama sai tafi sakewa”