BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

Yanda yaga raina a had’e yasa murmushi daya shigo dashi ya kau Yana “Lubna lafiya kuwa”?
“Ba komai”
Kawai nace Masa na samu waje na zauna Ina Masa sannu da zuwa ya amsa Yana “Lubna ban Saba ganinki a haka ba lafiya kuwa”?
“Wlh wanan yarinya ce ta bata min Rai kasan na tsani naga an shigar min daki kwatsam sai gata ta shigo min daki ni naga alamar tana da rawar Kai a gaskiya in zata cigaba da min haka bazamu shirya ba”
“Oo keda kanki yau Kuma kika cewa ta bata miki rai, da da Kika kawota wancan d’akin fa”
“Gaskiya badan kusancinka da Abdul ba wlh gobe zata barmin gidanan bana San munafirci kaga kwalliyar da tayi sai kace wata matar gidan”
Daga hannuwansa sama yayi Yana “Ni ba abinda nagani mallama muje ki hada.min ruwan wanka tunda zu ma nake kiranki baki dauka ba”
Mik’ewa nayi na nufi d’akin ya biyoni a baya.
Koda na zuba Mata abincin a bakin k’ofa na ajiye Mata “Ina ummi ga abincin ki ban tsaya jiran ta fito ba na koma Palo mukaci abinci da mahfuz .
Muka tab’a hira lokacin baccina nayi na mike dan nasan sai yayi kallonsa na masifa daya tsiro dashi.
Washegari ban bari ta wani tayani aiki ba kafin ta fito na gama komai yau Kam bata Isa na Mata wani abin karyawar va abinda nayi zata ci.
Doya da kwai da tea.
Har mahfuz ya fita bata fito ba.
Ban Kuma damu na dubata ba bansani ba yau ko ba inda zataje,nidai yau fita zanyi zanje kunshi da kitso.
Mmn Iman tun jiya tana unguwarsu.
Idan ba inda zataje sai ta zauna tayi gadin gida na kulle palona.
Na shirya kenan,na fito Palo sai gata ta shigo palon sanye da hijabinta har kasa a Raina nace munafika
Gaisheni tayi.murya na rawa na amsa Mata Ina k’ok’arin goya mimi tace ” Aunty ko dai akwai abinda na miki ne bansani ba”?
“Mai zakimin kuwa ummi”?
“Wlh sai Naga kamar na Bata Miki Rai bansani ba Dan Allah kiyi hakuri”
Tuni naji ta bani tausayi nace “ba komai wlh ummi jiyan ne raina a bace,ga abincin ki nan fita zanyi kinsan saura kwana biyu sallah zanje kitso da kunshi”
“A koshe nake Aunty bana Jin yunwa yau nima ba inda zanje Dan Allah ko zan iya binki kunshi bana so na zauna ni.kadai”
“Ba damuwa ki zo mu tafi.
Mik’ewa tayi da sauri ta fita waje ba dadewa sai gata ta fito da hijabinta har kasa.
Na kulle ko’ina muka nufi gidan kunshin…..
BUDURWAR MIJINA
*NA SADNAF*
E.W.F.
PAID BOOK
Last free page
Anan na kawo karshen free pages tighten your belt dan labari rikita rikita karamin yak’i a cigaban budurwar mijina biya 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko 0000551222 Taj bank nafisa Nuhu idan katine turo Mtn ko Airtel ta layin nan 08033719070 ku turo da shaidar biya ta nan layin 08033719070 mutanen Niger Kuma katin Airtel zaku turo na dari biyar ta layin mtn din,daa baki labari gwara ki bayar da ki tsaya a sato Wanda ya hucce gwara ki kasance cikin grp ki karanta da duminsa,Yan albarka shekarar Nan hajji nakeso naje maza a harhado na samu na calle????????????
Last free page
Ba mu dade sosai a gidan kunshin ba dan dama Mai kunshin tasan da zuwana na Kuma dade da Kama layi.
Ni aka fara yiwa hannu da kafa ja da baki.
Ita Kuma ummi tace ayi Mata a iya hannu
Sai amsa waya take kamar wata Yar kasuwa waya biyune da ita babba da Karama,anfi kiranta a karamar wayar.
Na riga ta cire kunshin hannuna,zaman da nayi bana komai yasa nace “Ummi dan bani wayarki na kalli hotuna”
zaro Ido tayi tana “Kai Aunty sai dai na baki karamar dan akwa sirrikana a wayar nan kiyi hakuri”
Dariya ma ta bani na Kai hannu zan d’auka dan Yana cinyarta tayi saurin daukewa wayarta ya kawo haske.
Kamar dai hotonta ne da wani.
Girgiza kai nayi Ina “Ai shikenan”
A Raina na fara gasgata zargin da nake Mata da kila Yar duniya ce daga yanda maza rututu ke kiranta Anya ma ba karya tamin akan an sa mata Rana ba kuwa”.
A haka na zauna itama ta cire nata.
Hannu na saka ajaka dan na dauko kudin kunshin tunda iya hannu aka Mata Dubu daya dai zan iya biya Mata Dan Dubu biyar mahfuz ya bani sababin dari bibbiyu.
Kafin na ciro kudin itama ta ciro sababin dari biyun ta kalli hannuna na kalli nata,ta saki murmushi tana “kema ashe dari bibiyun ne dake,jiya na tsaya a banki na cira”
Ta kirga Dubu uku ta bawa Mai kunshin dan nawa Dubu biyune.
Na maida kudina jaka Ina ngd.
Daga nan Muka wuce saloon,Ashe ba karamin gashine dani akanta ba.
Kitso aka fara Mata na kari shuku,ni Kuma aka fara yarfa min kananan kitso da iya gashina dan idan akwai abinda na tsana bai wuce Karin gashi ba banayi Sam duk da kitson Karin na balain saka mace kyau ni iya gashina ake kitsemin Kuma Ina kyau a haka.
Ummi kuwa ta balain yin kyau dan kitson nata har gadon baya aka Mata.
Bamu koma gida ba sai wajen shidda
Da sauri sauri nayi wanka na fito na Dora Mana jollof din taliya da kifin gwangwani ummi Kuma tunda muka dawo data shige daki bata sake fitowa ba.
Mahfuz Bayan magriba ya dawo gida.
Kamar yanda muka Saba bayan sallah Isha na zuba mana abinci na zuba wa ummi nata daban.
Na Kai Mata har daki,sakin baki nayi Ina kallonta dan sleeping dress ta saka fara iya cinya shara shara Ina iya hango komai na jikinta ta saki gashin dokinta har baya, konida nake matar Aure bana fesa uban turaren da ta fesa yanda nake kallonta tasa ta jawo hijabi ta saka tana “Aunty wlh yau zafi nakeji”
Gyada Mata Kai kawai nayi na ajiye Mata farantin na fito kaina na Kara daurewa da lamuranta.
“Kisa Ido sosai akan yarinya Nan lubna wlh ban yarda da ita ba bansan Mai yasa nakejin kamar ba alherine ya kawota gidanki ba”
Na tuna chatt din da nayi da mmn iman dazu
Duk sai naji jikina yayi sanyi har muka gama cin abincin abin na damuna a Raina sai matsawa kaina nake da tunani ko dai akwai abinda mmn Iman ta Sani akanta Wanda ni bansani ba,Ni mahfuz ba wani kallonta yake ba ballantana ince zata kwace min miji.
Haka dai na zauna mahfuz na latse latse a wayarsa.
Lokacin baccinmu nayi nace ya tashi muje mu kwanta sai yace min bayajin bacci
Ido na zuba Masa dan a da ba haka yakemin ba ko lokacin da yake ganiyar soyayya da wanan tsinaniyar Yana kwanciya sai dai ya saci jiki ya sake fitowa,Sam bana so Kuma na zarge shi muna zaman lafiya a yanzu.
D’akin nawa na shige na bar shi a palon Ina kwanciya bacci ba dadewa bacci yayi awon gaba dani.
Mugun kishirwar da nakeji ne yasani tashi daga baccin daya d’aukeni.
Idona ya sauka akan agogon daki karfe biyu na dare,ba abinda ke tashi a palon sai karar Tv.
Mik’ewa nayi dan naje kitchen na d’auko ruwa kila ma bacci ya d’auke mahfuz akan kujera.
Ina zuwa palon na ga ba kowa bansan Mai yasa kirjina bugawa da balain k’arfi ba nayi sauri na Shiga kitchen nan ma mahfuz baya ciki.
Na fito da sauri,kwakwalta ta kasa bani wani tunani abinda kawai na iya ayyanawa a zuciyata shine Kar nayi kwakwaran motsin da zaa jini.
Hanyar wajen na nufa Ina tafiya cikin sand’a kirjina Kamar ya fado, Hoton ummi kawai nake hangowa a idona data Sha sleeping dress da mijina a d’akin.
Tunanin nan ya Sakani tsayawa Dan ji nayi Kamar an caka min wuka a kahon zuciya na Dade a tsaye dan kasa motsa kafata nayi Ido kawai na zubawa d’akin da ummi take dan Ina tsaye a tsakiyar tsakar gidan ba abinda nakeji sai karar fankar dakinta sai gani da adduar Allah yasa mahfuz na waje Yana Hira a waya da budurwarsa ba a d’akin Ummi zan gan shi ba na kara taku biyu zuwa k’ofar dakinta na manne a jikin k’ofar da aka turo ban Bari k’ofar tayi Kara ba.