BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

A kwance ya sameta a doguwar kujera ta Sha kitson attach da tayi parking,sai riga yar kanti armless da taje mata har kasa duk da batayi kwalliya ba bata yafa komai ba tayi wa mahfuz kyau.
Nanarkewa kawai take tana shagwaba Kamar bazai tafi ba lubna dake ta kiransa a waya yasa ya Mik’e ya Mata sallama ya ajiye Mata kayan dubiya ya fito.
Wani ikon Allah Koda ya dawo gida suna Hira da lubna Yana tuno Hadeeza da yanda ta ringa Masa shagwaba tunda ga wanan lokacin ya dawo da Hadeeza rayuwarsa ta samu matsayi a zuciyarsa dan ta Kai yanzu har breakfast take Masa idan zai wuce ya karba da Rana ma abincin take aika Masa.
Dak’yar yake yakice cin abincin dare a wajenta gudun kar Lubna ta zarge shi.
Zuwa yanzu baya iya kwana biyu bai ga Hadeeza ba duk da ba abinda Lubnarsa ta rage shi dashi wanan kenan.
LUBNA
Jan kunshi mai kunshina ta rangada min a hannu da kafa.
Tana ciremin na sallameta ta tafi na hada Abubuwan da nake dan gyaran jiki dashi na hada na mulka a jikina dashi sabida fatata ta Kara laushi.
Iya kokarina zanyi dan na dawo da hankalin Mahfuz kaina bazai yu wata Yar iska can ta kwace min shi ba,nima sai a yanzu naga wautata da na hau fushi da shi,waya sani ma ko kwana ma yayi jiya yana waya da yar iskar SR.
Sai da na goge ko’ina na jikina na Shiga wanka har wani iska naji Yana Kara Shigana.
Mahfuz na san shinkafa da wake da salad hakane yasa na dafa shinkafa da wake na hada masa zobo sai da na gama na koma d’akina Ina duba kayan da Zan saka yau nayi Masa kwalliya yasan har yanzu da saurana ciki ne kawai yasa bana kwalliya duk kayana sun min kad’an dak’yar na samu wani kamfala da nayi wa dinkin bubu mai kalar dorawa da bak’i ya shigeni ya kuwa min kyau dan na cika kayan bansa breziya ba dan mahfuz bai fiye San na saka breziya ba, Hoda da Jan baki na shafa Nima kaina nasan nayi kyau na mulka jikina da turare na fito daga d’akin na koma Palo na zauna.
Wayata na dauko na kira shi a waya Yana fara ringing ya dauka na sauke ajiyar zuciya da naji muryarsa
“Matata ta kaina kin sauko kenan”?
“Hmm dama ni ba fushi nayi ba kishin mijina kawai nake aka nuna nayi laifi”
“Mijinki nakine ke kadai bai Kamata ki dagawa kanki hankali ba”
“Tom mijina ya Kamata ka dawo yanzu matarka nasan ganinka”
“Mai Kika ajiyemin”?
“Kaima kasani”
nace Ina sakin murmushi kamar Ina gabansa
Murmushi yayi yace gashi nan ya kashe wayarsa yana kashe wayar Kiran Hadeeza na shigowa wayarsa.
Bayaso ya d’auka tace Masa yazo tunda har ya samu lubna ta sauko da kanta Kamata yayi shima ya faranta Mata.
Kashe wayarsa yayi gabad’aya dan yasan Kira zatayi tayi
Ana kiraye kirayen sallah magriba naji tsayuwar machine d’in mahfuz ido na zubawa kofar har ya shigo idonsa kyam a kaina Nima idon na zuba Masa ina dan sakin murmushi dan har dan sakin baki yayi nasan mai hakan ke nufi
IIyye wai duk wanan kwalliyar ni akayiwa Kinga yanda kikayi kyau kuwa aikuwa ya Kamata na biya kudin kwalliyar nan daga haka ya nufo wajen da nake baiyi wata wata ba ya daukeni dak’yar Yana nishin nayi nauyi
Nasan Mai yake nufi ce Masa nake ya bari muyi sallah fir yak’i har sai da muka samu nutsuwa da juna na gamsu da mahfuz nawane ni kadai ba wata Yar iska da ta Isa ta rabani dashi sannu a hankali zan rabashi da wata SR.
Tare muka yi wanka muka yi sallah mu kaci abinci tamkar lokacin da nake amarya.
A kan cinyarsa bacci ya d’aukeni Yana ta shafa min kaina Ina jinsa ya d’aukeni dak’yar ya je ya kwantar dani a d’aki bacci mai dadi da nutsuwa yayi awon gaba dani.
MAHFUZ
Daga sakin munsharin da lubna keyi yasan bacci yayi awon gaba da ita,baisan Mai yasa hankalinsa ya rabu gida biyu ba so yake kawai ya Kira Hadeeza ya riga ya Saba sai sunyi waya ko video call yaji muryarta ta masa shagwaba a hankali ya zare jikinsa daga jikin lubna cikin sand’a ya fito daga d’akin ya fito daga palon ya fita can waje gudun ma Kar lubna ta Kara kamashi.
Akan dakalin gidan ya zauna ya fara Kiran Hadeeza da tak’i daga wayarsa hankalinsa yayi balain tashi hakane yasa ya dage da kiranta.
LUBNA
karar bud’e k’ofar palona yasa na bud’e idona dan banida nauyin bacci ko kad’an
Mikewa nayi a hankali na zauna da naga mahfuz baya d’akin.
Haka kawai gabana ya Yanke ya fadi Allah yasa ba Kara Kama mahfuz zanyi Yana waya ba.
Daga idona nayi na kalli agogon d’akin 12:20am.
Saukowa nayi daga Kan gadon haka kawai naji zuciyata na rayamin Mahfuz na palo Yana waya da Yar iskar yarinya Nan da bansan adadin tsinuwar da na mata ba.
Kishin daya rufe min ido yasa na fito daga d’akin da sauri sai dai Koda na fito baya palon hakane yasa nayi wajen tsakar gidan dan k’ofar palon a bud’e yake haka ma k’ofar gidan dagani sai sleeping dress na nufi wajen k’ofar a hankali kirjina na bugawa,zuciyata Raya min kawai take na koma Kar naji abinda zai daga min hankali daya zuciyar tawa da bakin kishi na ingizani da gwara na ganewa idona mai mahfuz keyi waje.
“Dan Allah kiyi hakuri haba mana na fada miki bada gangan na kashe wayar ba abinda ya sauka a kunne na kenan….
mg’s skincare
Shin Ina matan suke????️????️????️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi????????
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg’s organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum????hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg’s b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki????
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi’iznillah sister’s duk Wanda yayi using mg’s sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy ????ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg’s skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg’s babushi akasuwa????
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go????
Then @mgs skincare gat you covered ????
Now is time to glow????
Pamper ur skin????
Shine like bride????????♀
Glow????♀️
???? tested nd trusted????
Guarantee
BUDURWAR MIJINA
*NA SADNAF*
E.W.F.
PAID BOOK
PAGE 4
Runtse idona kawai nayi jikina na rawa badan nayi da gaske ba ba abinda zai hanani faduwa.
Tamkar a handsfree ya saka haka nake jiyo maganar ta Cikin shagwaba da kuka
“Dan kaga Ina sanka da kaunarka kake wulakantani mahfuz mai yasa kake min haka”?
“Wlh ba haka bane haba sweetyna ya za’ayi na wulakantaki ban isa ba cajina ne ya d’auke Kuma wani uzuri ya tasomin naje gidanmu ban baro can bama sai goma na dare wlh “