DUBAI PART 2

Miqewa yayi ya nufi qofa Abba da Dad suka miqe suka rufa masa baya har dakin da Granny take jinyar jikanyar tata ya tsaya a bakin qofar ya zuba mata ido yana hawaye ya rinqa jan qafarsa a hankali har ya qarasa gadon ya durqushe a gabanta tare da kama hannunta yana kallon na’urorin da aka daddaure qirjinta dasu.
Wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo masa suka zuba a saman hanun Habeey ya sake rungume hannunta a qirjinsa cikin kuka me sauti yace “rayuwata dake a haka tafimin dadi fiye da na rayu da matan duniyar nan Habeeytah ko tausayawa masoyinki me qaunarki domin Allah kada ki yankemin farin cikina wlh nayiwa wannan rayuwar tanadin farin ciki me dorewa har abada Habeeytah nayi alqawarin da sanina bazan qara sanyaki zubar da hawaye ba duk ranar da kika zama mallakina, ki tashi Habeeytah don Allah ki tashi kamata yayi ace a daidai wannan lkcn muna kwance a dakinmu ne a gadonmu na sunnah kina kwance a qirjina Ina shafa wannan dogon gashin naki”
Yakai hanunsa ya shafo gashinta dake baje saman pillow wanda kullum sai Granny ta gyara matashi sai sheqi yake baqi sudik dashi, ya shagala sosai da kallonta da shafa sumar tata ya zubawa dan qaramin bakinta da smile face dinta idanu gani yakeyi kamar murmushi takeyi masa ya dago ya kalli Abba yace.
“Zo ka gani Abba murmushi takeyimin don Allah ka fada Mata karta mutu akai gift din da nakeson bata wacce na siyeta tun ranar farko dana fara saninta mace, na ajiyeta a matsayin kyautar da zan bata duk ranar data zama mallakina Abba ka fada mata da hannunta nakeson ta karba don Allah”
Ba Abba da ciwon yar tasa yakecin zuciyarsa ba hatta likitar dake kula da ita kuka takeyi cike da tausayin Taheer din tunda take bata taba ganin kojin lbrn irin wannan soyayyar ba, Tasha ganin irin wannan usue din da zarar namiji ya fuskanci mace batada amfani a gurinsa zubar da ita yakeyi Amma shi yanzune ma ya fara sonta itakam zataso jin mafarin wannan sarqaqqiyar qaunar.
Da wannan tunanin ta dafashi tace “kayi hqr zata warke insha Allahu saita haifa maka yan biyu munzo Bauchi munsha suna yallabai” miqewa yayi yace “na gode Dr amma ya kamata kema kiyi wani taimakon wata goma yayi yawa inajin tausayin matata ni banida matsala wlh ko a haka zata dawwama zan zauna da ita zan sallama lkcna wajen kula da matata”
Dafashi Dad yayi yace “dama jiran warkewarka mukeyi zaku tafi Germany na tanadar muku gdan da zaku zauna da likitan da zaike kula da ita gdan kusa da Royal hospital Germany yake daganan likitocin zasuke zuwa dubata ga kuma abbanku kusa daku”
Granny ce tayi saurin cewa “anya Aliyu wannan tsarin babu wauta a cikinsa jinyar mace sai mace kuma yaushe ma zakace zaka bawa Taheer wannan yarinya ya tafi da ita shi kadai nidai wannan shiri bai kwantamin ba”
Shigowa Mom tayi itada Zahrah tayi saurin cewa “wannan tsarin kwata² baiyi ba shima Taheer din ai zai iya kula da matarsa gsky bazasuje ko inaba kabarta anan yake kula da matarsa ga qanwarta nan saita zauna tare da ita”
Saurin kallonta Saudat tayi ta qifta Mata ido ta juya ta kalli Taheer ya zabga mata wata uwar harara yace “amma dai sainaji kamar baa sanyaki cikin maganar nan ba ko” daga masa hannu Dad yayi yace “hakan zaayi Taheer kawai a hqr da tafiyar nan tunda zatazo da matsala ko ya kagani Salahu?”
Jinjina kai yayi yace “duk yanda kukayi ma daidaine amma Saudat bazata gidan Habbatullah ta zauna ba kamar yanda na datse duk wata alaqa ta kusanci tsakanin Habbatullah da mahaifiyarta Hajar haka na datseta tsakanin Saudat da Habeey harsai zuwa lkcn data samu sauqi dakanta ta nemeki kinji ko?”
Daga Kai tayi cikin qunar zuciya tace “naji Abba Amma…” Daga mata hannu yayi yace “kune musabbabin faruwar koma saboda haka banson jin komai daga gareki Taheer ka kula da matarka Allah ya taimaka maka zan nemo muku yan aiki biyu da zasuke tayaka jinyarta”
Murmushi yayi yace “na gde Abba amma bana buqatar tallafin kowa wajen kula da matata zan iya komai nasani idan nine a irin wannan halin Habeey bazata taba yarda wani ya kula dani ba ita zatayimin komai saidai idan fin qarfinta akayi”
Sosai zuciyar Abba tayi sanyi yaji dadin kalaman Taheer duk da yasan hana tafiya da Habeey din wani salon makirci ne saboda sarai yana hango qiyayyarta a idanun Mom da matarsa Zahrah.
Itakuwa Saudat a duk lkcn da taga yanda Taheer yaketa jagwalgwala Habeey sai taji wani shauqi yana shigarta duk da tasan cewa yayi Mata nisa amma ta kasa daina kallonsa da fuskar qauna inda shi Kuma bata hangen komai a idonsa sai qiyayyarta.
Ran Mom baiso hakaba taso aja maganar har rai ya baci amma sai taga akasin haka suka fice zuciyar kowa babu dadi suka nufi gida Mom ta daki sitiyari tace “wannan abin yana firgitani anya kuwa Taheer mutum ne”
Tabe baki Saudat tayi tace “to wai Mom meye yasa kika tsani Aunty Habbatullah ne nifa indai danni kike wannan abin kima daina nariga na sallamawa yar’uwata mijinta dama tun farko rashin sanine yasa nayi yunqurin shiga tsakaninsu, Mom abin yayi yawa da wanne zasuji ne sunason juna kuka cusa musu tsanar juna lkcn da muke tunanin haqanmu zai cimma ruwa lkcn ne kuma Allah ya zartar da nasa hukuncin ya qullah auren da bakwaso….”
Wani bugu Zahrah takaiwa yar tata tace “shashasha mara kishin kai dama ashe kema haka kike inata kashe kudina don ginaki ke kina qoqarin rusani to wlh kika sake tausayin wannan makirar yarinyar ya ratsa zuciyarki sai ta rabaki da duk wata fada da kike taqama da ita uban naki ma saiya daina kallonki”
Shiru tayi batace komai ba qasan zuciyarta yana tunano mata yanda taga Taheer yana shigewa jikin Habeey tayi saurin kawar da tunanin ta dauki wayarta tana wasa da ita har sukazo gdan.
Kwanaki biyu Habeey ta qara a asibitin aka sallameta zuwa gda Taheer yaso su tare a gdan da Dad ya mallaka musu amma fir Dad yace saidai ya bari idan matarsa ta warke saisu tare, hakanan badon ransa yasoba saidon nasihar da Abba sahabi ya rinqa yi masa, shine dalilin da yasa ya hqr ya zauna a cikin government house din bangare guda aka ware musu aka zuba musu yan aiki sosai….
UMMUH HAIRAN
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2
12
Ranar da suka tare kwana yayi yana kallonta yana hawaye yau ga Habeey dinsa yar uwarsa jininsa matsayin matarsa amma saidai ya kalleta.
Miqewa yayi ya dauro alwala ya tayar da sallah yana kuka yana nemawa rayuwarsa lafiya gurin Wanda yake da ikon canza al’amura sai asuba ya kwanta bacci ya dan daukeshi yana rungume da ita yanajin dumin jikinta na ratsashi.
Takwas ya tashi ya zuba Mata ido yana murmushi ko yaushe a kowanne hali fuskarta bata rabo da annuri ya share hawayensa ya sunkiyo daidai bakinta yace “kinaso nayi miki wanka?” Zuba mata ido yayi kawai sai yaji kukansa yana qara qarfi ya kwantar da kansa a jikinta yana lasar jajayen lips dinta da suke kullum kamar tasanya musu jambaki.
Dagata yayi a hankali ya cire mata komai dake jikinta yanajin faduwar gabansa na tsananta, ya dade yana kallonta daqyar a galabaice ya dauketa ya shiga da ita bathroom ya sanyata a ruwan wankan daya hada Mata ya diba ya watsa Mata a fuskarta duk ta rame yayi murmushi yace “nasan zakiso ramawa ko?” Diba yayi ya watsawa kansa yayi dariya yace “komai kikeso sh izanyi miki ko kaya zansa sai wanda nasan zakiso HABEEYTAH”