DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Hudu na yamma aka fara walima sai takwas na dare aka shirya kai amare gidajensu itadai Habeey kuka takeyi da zuciyarta da ruhinta wanda tasan ba kukan rashin sabo bane kona takaicin nesa da dangi aa kukane na tunanin irin rayuwar da zata fuskanta a sabon ginin tubalin qarfen da ta shiga wanda take fatan mutuwa ta zama silar rabuwarta dashi tabbas tana jinjinawa mazantaka da hallaccin Taheer a rayuwarta kullum tunaninta dame zata saka masa wanne halacci zatayiwa rayuwarsa dazai zama makwafin wanda yayi Mata?
Da wannan tunanin taji an tabata ta baya ta juya da sauri kawai sai taga Mom tayi Mata murmushi ta jata gefe gaban Habeey na tsananta faduwa ta rusuna domin girmamawa ga surukar tata,
Sakeyin murmushi tayi tace “tabbas karo da dama habiba kece kike nasara akai na kin samu saa kin auri Taheer uhmmm yaro yarone ba auren ba zaman kije kiji dadin zaman gidan mijinki bazan hanaki ba habiba ace Allah yabada saa”

Kalma daya ta kasa fahimta cikin kalaman Mom amma saita girgiza kai tana shassheqar kuka tace “nan… Na gde Mo…” Dagota tayi tace “meye abin kukan Kuma ai kin saba Taheer awone daidai qugunki ga shaida nan kowa yana gani a bariki ma kin jure bare kuma auren sunnah”
Jin an fara horn ne yasa Mom kamota a jikinta tana bubbuga bayanta tana cewa “kiyi hqr ku zauna lfy shine burinmu ke amana ce gurin Taheer Taheer ma amanarki ne Allah ya kawo yan biyu sau biyu na sunnah mu goya”
Mamakine yasata dagowa kawai sai taga Abba akansu ya miqa mata hannu tayi saurin komawa jikinsa ta qanqameshi ta rushe da kuka “bansan ko nayi maka wani abuba tsayin rayuwata dakai Abba ka yafemin kasawa aurena albarka nasan zata bibiyeni rashin samun albarkar bakinka cikin rayuwata yana daya daga cikin dalilan lalacewar rayuwata a baya….”

Rufe Mata baki yayi yace “zanci gaba dasa muku albarka har na koma ga mahaliccina ki riqe wannan ya zama abokin hirarki” ya miqa Mata qur’ani da carbi da sallaya yace “a duk lkcn da kika samu wasu wasin shaidan kiyi alwala ki fadawa Allah bijahi rasulullah zai kawo miki sauqi da gaggawa kada wani jarabta ya ratso cikin aurenki ki alaqantata da wani Habibatullah ki danganta komai da Zaki fuskanta cikin aurenki da ubangijin daya halicci kowa da komai Allah yayi muku albarka! Allah yayi muku albarka!! Allah yayi muku albarka!!!”
Yana fadin haka ya janye jikinsa daga nata Granny ta rike hannuta suka nufi mota abin mamaki Taheer ne kadai a cikin motar ya hada kansa da sitiyari suka bude suka sanyata ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur Abba yace “kai yayanta ne Taheer kai mijinta ne idan kuka daga kuka tafi U.S.A Kuma zaka zama uwa uba miji Yaya qani aboki duk kai kadai, Taheer amana nabaka Habbatullah inasonta inajinta a jinina fiye da yanda nakejin rayuwata nasan insha Allahu zaku zauna lfy inayi muku fatan hakan kayi hqr! Kayi hqr!! Kayi hqr!!!”

Barin gurin yayi da sauri daidai lkcn da hawayensa ya gangaro masa qwarai nasihar iyayen nasu ta ratsa jikinsa tausayi da qaunar qanwarsa matarsa yana ratsashi yaja motar suka fara tafiya mota daya ta security a gabansu daya a bayansu har sukaje cikin unguwar da gidajen nasu yake sukayi horn aka bude suka shiga sukayi parking ya bude ya fita ya bude mata ya ruqo hannunta fuskarta na rufe cikin alqabbar jikinta.
Bude masa qofar sukayi ya sanya hannu ya dagata cak ta kwanta luf a jikinsa ya shiga cikin katafaren parlourn bai ajiye ba saida ya haura da ita sama inda dakunan baccinsu suke ya direta a tsakiyar surper din dake saman wani hadadden carpet ya tsugunna a gabanta ya janye mayafin data rufe fuskarta ya saita fuskarsa da tata ya sauke mata wani zazzafan kiss yace “fadamin abinda yake sanyaki kuka a wannan ranar ta tarihi cikin rayuwarmu?”
Kukanta ta qarawa qarfi ta zame ta fado jikinsa tace “banso ba Taheer banso qaddararmu tazo a haka ba naso ace yau itace ranar da zan baka amanar dake tsakanin kowacce mace budurwa da mijin da Allah ya zaba mata wayyohh Allah Taheer baqin cikin rashin wannan abin da zanyi tutuya dashi matsayina na budurwa yana neman sanya zuciyata ta tarwatse….”

Dora bakinsa yayi saman nata ya lumshe idonsa yana murmushi yana tsotsar lips dinta saida ya tsotsa sosai ya saki yace “samunki kamar tikitin shiga Aljannah nake ganin ubangiji ya bani a hannu na saboda kece silar shiriyata Habeey ke rayuwata ce don Allah indai akan wannan ne kada ki qara yimin asarar hawayenki wlh yana daya daga cikin dalilan da sukasa na dage kaida fata saidana mallakeki saboda a irin wannan lkcn idan bani kika aura ba babu namijin da zai samu qwarin gwiwar qarfafa miki gwiwa waima ni da kike wannan mgnr waye ya karbi abinda kike kuka saboda shi a gurinki ne”…….

* UMMUH HAIRAN*

[8/11, 10:41 AM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki  ta wannan number dake sama Idan VTU ne ta wannan layin Zaki tura dari biyunki ko dari 600 ki/ka 09013307566 idan fah kika tura a wancan layin na sama to ki qaddara sadaka kika bani shi evidence of payment kawai zaa tura

22 Sake narkewa tayi a jikinsa yana shafa bayanta a hankali daidai lkcn da wayarsa tayi ring ya dauka yace “ok” kawai ya janyeta a jikinsa ya miqe ya fice,
Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da wasu manyan ledoji guda uku ya ajiye a gabanta ya shiga bathroom ya dauro alwala yazo ya shimfida sallaya yace.
“Tashi kiyo alwala muyiwa Allah gdy” qasa tayi da kanta ya girgiza kai duk plan dinsa na yau ya rushe amma babu komai yasan bata wucce kwanaki uku, sallar ya tayar yayi raka’a hudu yayi addu’o’insa ya matso gabanta ya kama kanta yayi Mata addu’a sannan yaja gwauron numfashi yace.

“Duk a sanyaye jikinki yake why?” Shiru tayi masa har yanzu hawayenta ya kasa tsayawa ya janyota ya hadata da jikinsa ya dago fuskarta ya dora harshensa saman kuncinta yana lashe ruwan hawayen dake zuba yace.
“Zanyi miki Allah ya isa idan kikaci gaba da zubarmin da hawayenki a banza ke wai meye yasa hawayenki suke da araha ne haka?”
Kwantar da kanta tayi a faffadan qirjinsa ya sanya hannu ya zame mayafin dake kanta ya cire dabkwalin ya dora bakinsa tsakiyar kanta ya sauke mata kiss ya tura hancinsa yana sunsunar qamshin dake tashi me dadi akanta yana ajiyar zuciya.

Saida yaji tayi shiru sannan ya janyo kayan da ya shigo dasu ya dauke leda daya ya bude biyun daya tarkacen namane da dangoginsu dayar Kuma madara ce kala² sai fruit.
Fita yayi ya dauko flat ya dawo ya sanya musu komai da kansa ya rinqa bata bata iyacin na kirki ba saboda hakanan takejin wata masifaffiyar kunyarsa.
Ya lura da haka Amma Bai kulata ba don yasan yanayin magana zata iya fashewa,
Saida ya gama bata shikam baici naman ba sabods farin cikin daya cika masa ciki yasha hollandia milk ya miqe itama ta miqe ta tattare kayan zata fita dasu yayi saurin juyowa har ya cire rigarsa da dogon wandonsa sai singlet da boxes kawai a jikinsa ya janyota ya dago kanta.
Idonsa ya shigar cikin nata ya karbe kayan yace “daga yau zuwa wata guda na hutassheki aikin komai idan har ba nawa bane a gdannan so nake ki dawo da jikinki harma kifi baya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button