DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Girgiza kai yakeyi sosai yana kuka me cike da nadama yace “wlh Dad ko yanzu idan baku amincemin na auri Habeey ba bazan iya riqe kaina daga gareta ba saboda zuciyata ita kadai takeso”
Murmushin takaici yayi yace “zaka aureta Taheer gara nabaka abinda kakeso kafin ka jamin abinda yafi wann….”
“Wlh tallahi bazai aureta ba Aliyu” cewar Mom da take shigowa kenan, tsayawa tayi a gabansu tace “bazai taba yuwuwa ka cakudamin zuri’a da shegu ba sannan ka canzawa shegiyar yarka suna baka isa ka shegantamin suna ba….” Miqewa yayi yace “don Allah ya isa Mom Habeeytah batason hayaniya kada ki tasheta…” Wani daukakken ta sauke masa wanda yaga tartsatsin wuta a idanunsa ya zuba mata ido tare da sauke numfashi

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
UMMUH HAIRAN

Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah

4

Ashar ta danna masa ta matsa ta fincike robar jinin dake maqale a hannun Habeey ta cafki wuyanta tana jijjigata tana fadin “wlh baki isa ki zama surukata ba tsinanniya matsiyataciya yar tasha karuw…” Wani kira dayakeyi Mata tare da finciketa daga jikin Habeey dinne ya dawo da ita hayyacinta ta saki wuyan habeey da sauri taja baya.
Tana kallon yanda take fitar da numfashi a wahalce ga wata kumfa da take fitarwa a bakinta tayi saurin juyawa zata fice governor Waziri ya kira sunanta tare da cewa “kafin ki fita kisan da saninki indai yar mutane fa mutu sanadin taaddancinki wlh sai kinyi zaman jarun”

Wata ajiyar numfashi Habeey tayi komai nata ya daina motsawa Taheer ya dira gabanta ta dagota yana danna qirjinta yana Kiran sunanta Dad ya miqe da sauri ya fita yaje ya taho da likitan itakuwa Mom tayi wuqi² cikin tsoro da tashin hankali Granny kuwa mamakin lamarin Mom ne ya hanata cewa komai sai dauke Safnah da tayi tasata a sabon gadon da ubanta ya siyo mata.
Rufuwa likitocin sukayi akan Habeey harda Taheer sun bata sama da awanni uku sannan suka samu numfashin ya daidaita suka fito zuwa lkcn Mom ta sace jikinta tabar asibitin ta wucce gidan yayarta tana kuka take zayyane mata komai har auren Saudat yar qanin Dad Sahabi data nema masa tasa Saudat ta dawo daga England kawai saboda ta hadata da Taheer amma abin yana neman gagara.

Yanda take kuka yasa Hajiya Ummah yayarta dariya tace “kece uwa kece kike da wuqa kike da nama fah yanzu dai shawara daya itace tunda ya kafe saiya auri yarinyar nan ki qyaleshi ya aureta din kodan rufuwar asirinku game da wannan yar kafin fatiha din ayi auren cikin sirri ta tare ta yanda babu Wanda zaisan ba aure aka haifeta”
Girgiza kai tayi tace “aikin gama ya riga ya gama Ummah sirrin dan siyasa baya buya ni kaina baa gurin Taheer naji haihuwar ba kirana akayi da baquwar number aka fadamin karuwar dana ta haihu a asibiti kaza har lambar dakin aka turomin”

Shiru sukayi na wani dogon lkc sannan Ummah ta magantu da cewa “shawara ta biyu kije ki hada baki da likitan ayiwa jaririyar allurar guba ta mutu kowa ya huta…” Da sauri Mom ta kalli Ummah tace “kuma nayi kisa Ummah aa bazan iya ba nikam inajin tsoro na lura daga Granny har Dad hankalinsu yana kan wannan jaririyar”
Murmushin takaici Ummah tayi tace “shikenan kije zanyi tunanin mafita kafin a sallamesu daga asibiti cikin wata biyun da kukasa na bikinsa da Saudat dole ne a mantar dashi tunanin wannan karuwar yarinyar idan ba hakaba tabbas da matsala don zama ku iya daura masa auren ya saki matar” miqewa Mom tayi tace “dakuwa na tsine masa ya qarasa lalacewa”

Da haka ta fice a gdan driventa yajata suka fice suka nufi government house suna tsayawa ta fito ta shiga gdan bangaren yammatan nata ta shiga ta tarar dasu sun rufu akan Saudat sunata rarrashinta itakuma sai kuka takeyi, salati Mom tayi ta shiga cikin dakin tana tambayarsu menene.
Kuka bai bari Saudat tayi bayani ba sai shassheqa da takeyi Bushirah tabe baki tayi ta shige bathroom Kubrah ta dago tace “Yaya Taheer ne ya dawo ya shiga dakinsa yana neman wani abu kawai ita kuma sai tabisa dakin munyi qoqarin hanata taqi hanuwa, bamusan me tace masa ba kawai sai gani mukayi ya fito da ita a hannunsa ya jefar da ita a parlour yana jibgarta kamar Allah ya aikosa yana gama dukanta ya fice ya hau motarsa yabar gdan itakuma munyi munyi da ita ta fada mana me tace masa taqi”

Zama Mom tayi zuciyarta na tafasa tace “ke me kikace masa da yaja miki wannan dukan sa’ar haka?” Cikin shassheqar kuka tace “wai…wai don na shiga ya fito daga wanka shine na matsi mai zan shafa masa ya juyo ya dakamin tsawa wai na fice masa daga part shi…shine nace karuwa ma ta samu lkcnsa balleni da zanzama matar sunnah shine ya juyo yacemin wai karna qara cewa da uwar yarsa karuwa domin tabashi abinda a duniya babu wanda ya amince ya bashi sai itadin kuma Koda zaa bashi to bayan wadda tabashi zasu biyo, nikuma sai nace ai ko a shari’a shege bashida gado saboda haka matsayin dan halak yana sama qololuwa dana dan zina, wlh Mom ban qaraba ban rageba kawai naji ya shaqeni ya hadani da bango ya gwaramin kaina da gini ni bansan ya akayi ba kawai saiji nayi ya zubar dani a parlour yasa belt ya rinqa dukana kamar jaka daqyar su Solomon suka qwaceni….”

Ta qarashe mgnr cikin gunjin kuka ta zame bayanta Mom tayi saurin rintse idonta saboda yanda ya farfasa Mata jiki da belt tace “yanzu Mom haka zan rayu da Yaya Taheer babu tausayi babu soyayya ace karuwa ma tafika matsayi a gurin mijinka, gsky Mom da sake duk da inason Taheer Allah ya jarrabi zuciyata da qaunarsa tun bangansa a zahiri ba Mom zan iya jure kowanne wulaqanci a gurinsa indai zai rayu dani matsayin matarsa saboda nasan yanda ciwon so yake nasan abinda yakeji Mom amma bazan dauki duka akan karuwa ba Mom waini meye Habeeytan nan da yake yawan ambata take dashi dani bani dashi? Meye tafini don Allah ki fadamin meye aibina da Yaya Taheer yaqi naam da soyayyata duk da kasancewata yar uwarsa ta jini wacce na yarda da naqasunsa da komai na aminta zan rayu dashi a haka”

Shafa kanta Mom tayi ta share mata hawayenta tace “na rasa meye yasa Taheer ya zama me taurin kai akan yarinyar nan wlh a baya duk abinda na nuna masa bana raayinsa duk son da yakewa abinnan ya hqr dashi amma nakasa juya zuciyarsa akan yarinyar nan wai harni Taheer yake kallo yacemin indai ban janye auresa dake ba nabarsa ya auri Habeey ba to shakka babu zakiyi nadamar zuwanki duniya kuma zina yanzu yafara saboda zuciyar Habeey a hannunsa take duk yanda yayi da ita haka takebi, Saudat zanji tsananin kunyar Sahabi da Zahrah qanwata idan har nakasa tanqwara zuciyar Taheer ya aureki bari kiji wani Abu” kunnenta ta kama ta rada Mata wata mgn sukayi dariya tare da rungumeta tace “shiyasa nake sonki Mom har mafarkin first night dina a gidan Yaya Taheer nakeyi yauma saida nayi mafarki ganinan a kwance a qirjinsa yanata shafa sumata”

Rufe mata baki tayi tana dariya tace “saudat bakida dama wai yaushe Abbanki zaizo 9ja ne?” Lumshe idonta tayi tace “yacemin tunda ya rasa “Matarsa ta fari Hajar lkcn da cikinsa watanni uku a jikinta ya fara wannan ciwon zuciyar yakejin idan an ambaci 9ja gabansa na faduwa yacemin kullum mafarkinsa shine yazo 9ja amma gani yake kamar idan ya dawo abinda ya faru shekaru ashirin da daya baya shine zai qara faruwa”
Girgiza kai Mom tayi tace “har yanzu Sahabi yana mafarkin ganin wannan Dan nasa ko yarsa don ko jiya da mukayi waya da Mamanki take cemin wai yanzu firgita yakeyi yana yawan Kiran sunan Hajar yana ambaton Ina dansa ko yarsa? Kuma fah bayan rabuwarsu ance nemanta akayi aka rasa wasu ma suna cewa ta mutu”
Share hawayen tausayin abbanta Saudat tayi tace “nima kullum Ina addu’ar indai dan uwana ko yar uwata tana raye tazo gareni ko yazo gareni Mom kadaici ya isheni Mom banida abokin kuka banida na dariya banida shaqiqin da zanyi hira dashi naji dadi nasan yanzu da dan’uwana ko yar’uwata tana kusa gareni da zata rinqa tausata da tayani addu’a akan wannan mugun son da nake yiwa Yaya Taheer shikuma baya sona dama tun Ina qarama Yaya Taheer ya tsaneni” ta qarashe maganar cikin kuka me narkar da zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button