DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Addah ce ta shigo da qanwarta suka zauna kusa da ita abin mamaki wai Addah ce take gyarata dakanta hadin magungunan mata ta rinqa bata harda su jijjibi da kaza duk tayi mata tsimi kuwa tayi Mata yafi kala nawa ga wani matsiyacin matsi da aka hado Mata daga Niger itadai da aka batashi akace ta matsa a gabanta Saida ta ta saboda tariga tasan karonta da Taheer.
Amma babu yanda zatayi hakanan tayi saboda tsayawa Addah tayi akanta Saida ta turashi daqyar ta zare hannunta sannan ta bata ruwan magani tace tayi tsarki dashi tanayi tana yarfe hannu saboda yanda taji fatar gabanta tana wani tsukewa ga ruwan ma da dumi sosai.
Bayan ta gama Addah ta debo garwashi ta zuba wani turare a ciki tace ta tsugunna akai ranar nan Habeey tayi kukan wahala yafi dari sai yamma suka gama shiryawa suka nufi cikin garin gombe gidan Addah wayyoh Habeey taga ikon Allah gda yayi gida saida suka shiga parlourn taga manyan hotunan Addah da Abba Sahabi da ita a tsakiya.

Tsayawa tayi tana kallon qudurar ubangiji ta juya tana kallon mutanen dake parlourn babu Wanda zata tambaya saboda haka ta sulale ta koma waje ta dauki wayarta ta lalubo lambar Abbanta ta danna masa kira ya daga yace.
“Amarya kinsha qamshi yanzu angonki yake cemin bakida lfy halan mun samu sabon jika ne?” Wata muguwar kunyace ta rufeta ta kashe wayar daidai lkcn da wayar Taheer ta shigo ta daga tace “wai maye tsakanin Addah da Abba ne?”
Murmushi yayi yace “aure mana” zaro ido tayi tace “wanne irin aure Taheer” katseta yayi da cewa irin wanda kika sani yau ta tare a gdanta jibi ke kuma zaki taho naki akwai dinner bikinmu yau da dare fah anan Gombe idan an gama zamu tahi dake nan harda Addah ayi kamu sai ayi walima tare da saukar qur’ani sai abani ke mu wucce U.S.A jibi”

UMMUH HAIRAN

[8/9, 7:21 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number dake sama.

20 ajiyar zuciya taja ta sauke yayi murmushi yace “inasonki my life” kashe wayar tayi juyawar da zatayi taga Abba yayi Mata murmushi tare da shafa kanta yace “motoci sunzo ga qanwarki can a tana jiranki dame kwalliya fatan bazaki bata lkc ba”
Kama hannunta yayi suka shiga ciki ya rakata har dakin da su Saudat da Kubrah da Bushirah suke sunata yi mata tsiya ta zauna a kunyace itama akayi Mata kwalliya tare da bata kayan da zata sanya Wanda ankone da angonta shi arsh din dakakkiyar gezner ita kuma less ne me masifar tsada.

Tasanya arsh aikuwa taja magana Saudat saita lalace a kallon yayar tata tace “aunty kece amarya nikam yar rakiya ce” dariya sukayi Mata Kubrah tace “komai Yaya Taheer ya zaba tun muna yara idan aka zubeshi sai kinga special ne”
Murmushi Saudat tayi tace “sun dace sosai saidai fatan dawwamar zaman lfy” Dad ne yayi sallama ya shigo har dakin ya kamo hannun amaren yayan nasu ya fara kai Saudat motar mijinta yasata sannan ya juya ya kai Habeey motar da Taheer yake a hakimce.
Yana sanyata ya sanya hannu ya riqo qugunta ta galla masa harara yayi dariya yace “aini mayene akanki indai kina kusa dani bazaki huta ba”

Haka motocin suka wullah har zuwa wani babban Hall da yake cikin gdan governor of Gombe state ashe abokin Dad ne shine ya shirya musu dinner din sosai dinner ta qayatar kowa dake gurin ya jinjinawa so da qaunar da Taheer yake yiwa Habbatullah data sanyashi rashin kunya baya iya boye maitarsa akanta.
Suna tashi suka nufi gdan da niyyar sauke Habeey sukuma su tafi a mota ta dago idanunta da suke lumshewa tace “maimakon naga Shattima matsayin angon Saudat sai naga Yaya Mahfuz yaushe lamarin ya canza?”
Janyota yayi jikinsa yace “ni Kai bansan dashi zaayi ba saida na koma Dad yake fadamin” daga haka bata kuma cewa komai ba saboda tasani sarai Saudat batason Mahfuz ko kadan basa ga maciji.

Da suka sauketa itama Saudat sauka tayi tana kuka ta rungume Habeey tace “kinga abinda nake gudu ko kowa ya auri masoyinsa amma ni an hadani da maqiyi na” tanajin Taheer na rirriqeta ta janye taja qanwarta suka shige ciki.
Yaji haushin abinda tayi masa hakan yasashi juyawa ya shiga mota suka tafi, ita kuwa suna shiga gda ta zaunar da Saudat tace “ba duka abinda zuciya takeso take samu ba Saudat nima a farkon haduwata da Yaya Taheer banasonsa na tsaneshi fiye da kowa saboda Ina kallonsa matsayin qaddara mafi muni a rayuwata amma yanzu ji nake kamar bazan iya rayuwa babu shi ba”
Haka ta rinqa lallashin Saudat har ta hqr tayi shiru sukaci gaba da harkokinsu sai dare Addah amarya ta shigo sanye da wani dakakken yadi ta zauna ta dauko wani cup na danyen nono da wani mugun hadin cukudi tabawa kowacce.

Habeey ta turo baki tace “nifa Allah Addah nagaji da shan wannan abin ku bakwa nemawa mutum sauqi sai wahala dai wahala dai” daquwa Addah tayi Mata tace “wannan mijin naki da ido a tsattsaye idan bada gamje²n ba don ubanki kinajin zakikai labari ne”
Qasa tayi da kanta cike da kunya kowa ma yasan Taheer dinta jarabbaene karba tayi ta shanye kamar zatayi amai ta jefa tomtom a bakinta itama Saudat ta shanye Addah ta miqe tayi musu sallama ta fice.
Da asuba suka tashi ita dama Habeey ba sallah zatayi ba da dare taji period dinta tazo ba qaramin murna tayi ba harda dariyarta ta mugunta tasan tacishi wannan wasan text ta rubuta ta tura masa aikuwa ya kirata kamar zaiyi me saboda masifa Wai ai tana sane tabari period dinta yazo saboda ta tsaneshi ba itaba hatta Saudat qunshe dariya take a ranta tana cewa Allah ya rabata da qaya Taheer ai masifa ne.

Kuyi hqr nayi typing nayi saving wtsp dina yayi expire Saida nayi update koma ya goge

UMMUH HAIRAN

[8/9, 9:04 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number dake sama.

21 A ranar da safe suka nufi Bauchi gaban Habeey na faduwa saboda ta gaza jure tsanarta da take gani a qwayar idanun Mom kullum idan ya kasance zasuyi gaba da gaba da Mom sai taji wannan faduwar gaban da take rasa dalilinta,
Suna isa government house din akaci gabada shagali itadai Habeey innanillahi wa innah ilaihirraji’un taketa maimatawa saboda fadadar zuluminta bawai akan Taheer bane aa tana tuno rayuwarsu ta baya da sukayi matsayin zaman dadiro yanzu kuma gasu matsayin ma’aurata zasu rayuwa rayuwa ta dindindin.
Janyo Safnah tayi da taketa rarrafenta a qasan gadon da take zaune ta rungumeta tsam a qirjinta bugun zuciyarta na qaruwa soyayyar yar tana na sake ratsa gabobinta a fili tace.

“Dama qaddarata ta jira zuwan wannan lkcn na samar dake cikin yanayin tsafta meye yasa zanen qaddara baya barin yaron da baijiba ba gani ba ashe haka zan qare rayuwata da ciwon abu biyu kaico na ni Habibatullah Allah ka tsayar da wannan muguwar qaddarar iyakar kaina kada ta haura kan wani Allah kada ka bani ikon bijirewa mijina saboda zafin mikin da zan mutu dashi a raina”
Ta manta da yawan mutanen dake dakin ta rungume Safnah sosai a jikinta tana kukanta me tsuma zuciyar duk wani Wanda yake cikin dakin,
Babu wanda yayi tunanin rarrashinta saboda rarrashi ma anayinsa ne a gurin da akasan kukan na taqi qalilan ne ba kuka na dindindin ba,
Zamewa tayi ta kwanta yinin ranar duk jarabar Taheer bai samu ganinta ba saboda Granny da kanta ta kasa ta tsare ta hana kowa ganin amare sai ita da wata kanuriya data nemo takeyi musu turaren taran angwaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button