DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Da wannan tunanin ya shiga mota yana Shirin tashinta qannen nasa suka fito Bushirah ta matso gabansa tace “sati biyar akasa aurenka da Saudat Yaya a halin da aka ciki Habeey da Safnah sunfi kowa buqatarka don Allah kada kayi sakacin da baiwarka Allan nan zata qara shigs gararin rayuwa Yaya Taheer jin Habeey nakeyi kamar yar uwata ta jini”
Riqe hannunta yayi yace “karki damu qanwata babu Wanda ya isa yayimin auren dole auren ma da wannan tsakuwar yarinyar haba suma su Dad wasa sukeyi wlh Idan suka suka matsa zan iya farke shegiya ta mutu kowa ya huta”

Yana gama fadin haka ya figi motar a guje ya nufi gidan Granny ya shiga bangarensa na gidan yayi wanka ya kwanta ya fara aikin sanar da abokansa cewa anyi masa haihuwa mamaki sukeyi sosai yaushe yayi aure da har matarsa ta haihu.
Shikam ko a jikinsa gani yakeyi ai shima aiki yayi ya samu abarsa sabida haka ya cancanci a tayasa murna, daya gama buge bugen wayar tasa sai ya budo hoton sahibar tasa da yar tasa ya rinqa kallo yana murmushi har bacci ya daukesa.
Cikin sati biyun da habeey tayi a asibiti abubuwa da dama sun faru ciki harda qarfafuwar mgnr auren Taheer da Saudat tabbas Saudat tana cikin matsananciyar damuwa saboda Wanda takeyi dominsa din baisan tanayi ba tana kallon yanda Khamal da Sudess samarin su Kubrah suketa rawar qafar bikin amma banda nata angon dako kallon tsiya bata samu a gurinsa balle na arziqi.

Da taimakon Hajiya Ummah yayar Mom da Zahrah mahaifiyar Saudat aka shiga aka fita aka cusawa Taheer jin tsanar Habeey a ransa sunyi duk me yuwuwa su cusa masa qiyayyar Safnansa amma abin ya faskara saima kamar qara masa qaunar yarinyar da akeyi.
Cikin sati biyun jikinta ya fara kyau sosai ta fara sanin waye yake a kanta, farkon fari kullum a asibitin yake yini amma yanzu sai ya yini sur baizoba saidai ya kira a waya yaji ya babensa, wannan canji ya tashi hankalin Granny da Bushirah dake jinyar Habeey da farko sun dauka mgnr auren nasa ce tasashi a busy amma sai Bushirah ta lura shima auren ba wani murna yakeyi dashi ba kullum ka nemeshi zaka sameshi a garden ya hade kai da gwiwa yanata karatun wasiqar jaki”

Yau ta kama asabarce wadda tayi daidai da satin Habbatullah hudu a asibiti misalin qarfe biyu na rana ta fara motsa qafafunta tare dayin attishawa daga Kubrah har Bushirah da Granny dama Addah da ciwon yar tata yasata saukowa shima Bushirah ce tayi tattaki taje ta sanar da ita.
Dukkansu kanta sukayo ta muqar da hannunta tare da amsa kalmar shahadar da Addah take laqaba mata ta riqe qam tanayi tana girgiza kanta, fita Bushirah tayi da gudu ta fadawa likitan abinda yake faruwa daidai lkcn da likitan ya iso daidai lkcn Taheer suka shigo shida Saudat a zahirin gaskiya shi kansa baisan Saudat ta biyosa ba saboda kaca² suka rabu dutsi a hannun riga amma sai gashi sun shigo tare kafadarsu na gugan juna.

A lkcn ne Habbatullah ta fara bude idonta a hankali tana kallon kowa dake dakin da fuskar rashin sani har takai ga sauke idonta akan Addah ta zabura zara miqe likitan yayi saurin riqeta tare da cewa.
“Kibi a hankali Hajiya zaki tashi insha Allahu” a sanyaye da murya ta alamun jin jiki tace “Ad…Addah ashe zakizo gurina ashe har yanzu kina sona Addah ina qannena Aysha da Fatima ina Taheer Addah ki kiramin shi don Allah” juyawa Kubrah da Bushirah dama kowa dake gurin sukayi inda yake tsaye yana danna wayarsa.
Wani mugun kallo Addah takeyi masa a cikin kwana ukun da tayi a asibitin yaune ta fara ganinsa taja ajiyar zuciya hakanan takejin tsanar Taheer a ranta kuma ta qudurce a ranta indai yarta zataji mgnrta to zata rabata dashi rabuwa ta har abada.

Matsawa Bushirah tayi kusa dashi ta warcr wayar hannunsa tace “haba Yaya kanaji sai kiranka Habbatullah takeyi Amma ka wani basar….” Bata rufe bakinta ba ya sauke Mata wani gigitaccen mari ya sakeyin bal da ita yace.
“Wata banza dake Zaki qwacemin wayata saime to dan wannan banzar ballagazar ta kirani dama jira nakeyi ta warke Kuma alhmdllh ta warke banida haqqinta zata iya komawa inda ta fito Amma karki sake ki daukarmin yata inason abata Saudat zata riqemin ita, yawwa ladan haihuwar kyakkyawar baben nan da kikayimin na mallaka miki gidana dake layin gdan sarkin Bauchi ki duba wayarki nayi miki transfer ta million hamsin nasan ta isheki ki qarashe rayuwarki na bakisu a matsayin fansar budurcinki”

Yana fadin haka ya ajiye Mata want a saman cinyarta ya juya zai fita ta bude bakinta jikinta na rawa tace “na roqeka da girma da matsayin ubangijin daya sanya tausayi da jinqai tsakanin bayinsa kada ka juyamin baya Taheer karka manta kayimin alqawarin duk tsanani bazaka gujeni ba bazaka juyamin bayaba wlh na amince zan aureka Taheer kada ka wofintar dani lkcn da nake tsananin buqatar jin qanka….”
Ta qarasa mgnr cikin sarqewar numfashi baiko qarasa jin abinda zata fadaba ya fice kamar iska yaja motarsa a guje yabar harabar asibitin ta kuwa zabura ta miqe zata bisa Dr Shattima yayi saurin riqeta ya hadata da jikinsa yace “tabbas kina cikin jarabawar ubangiji kamar yanda nake cikinta Habbatullah banyi tunanin wannan lkcn zaizo ba kiyi hqr zuciyarki a kumbure take idan kika mutu bashida asara saboda saura kwanaki biyar ya angwance da sabuwar amaryarsa………..

Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa 10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne.
Account 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB, saiki tura evidence of payment ta wannan number 09013718241
Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number 09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa.

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
    UMMUH HAIRAN

7

Zamewa tayi daga jikinsa ta zube a qasa numfashinta yana sarqewa ta dafe qirjinta jikinta yana rawa Dr Shattima ya matso da sauri ya kamata ya dorata a gadon ya zaro wata allura ya danna nata nandanan jikinta yayi laushi ta suma Granny ta juya ta kalli Saudat data zubawa Habeey ido cike da tsananin tausayawa hawayenta na zuba a qasa tace.
“Meye kuma abin kukan Saudatu kunyi nasara tabbas kuyin nasara Allah ya baku saa kun raba tsakanin Taheer da Habeey, Saudatu badai Taheer kikeso ba gakinan gashi daukar yarinyar dake bacci tayi ta miqa Mata tace “ga yar mijinki nan ki dauka ki riqe kwafi samun nutsuwa amma kafin wannan lkcn inaso kisan wani abu qwaya daya ita duniya juyawa takeyi saboda haka kada kiyi tunanin dawwama cikin farin ciki kin rabashi da farin cikinsa kin yankewa Habiba nata farin cikin shakka babu lkc na zuwa da zakiyi naki kukan babu hawaye”

Kubrah ce ta dubeta tayi “murmushi tace “haqqin rai biyu ne akanku Saudat koma nace uku saboda ke yaya yaci mutuncin Habiba saboda ke ya rabata da yarta saboda ke komai zai iya faruwa dashi kansa yayan, Abu daya nima da zan fada miki shine quncinki sai yafi wanda kika sanya zuqatan masoya sannan babu ubanda ya isa ya raba Safnah da mahaifiyarta harsai idan sune sukace bazasu riqe ba”
Addah ce ta girgiza kai tace ku bashi yarsa kawai bsmu buqata Allah ya rayata a duk inda take wannan qaddarorin na Habbatullah sinyi yawa Allah ka sassautawa baiwarka haka” hawayen saudat ne ya qara tsinkewa tace “wlh tallahi bansan meyene ya kawo wannan sauyin ba Granny yanzu kafin mu taho har zagina Yaya Taheer yayi akan Habeeytah ya rantsemin ya qara kan cewa koya aureni saiya sakeni ni zuwa nayi idan ta farka na roqeta ta nemamin alfarmar ya hadamu ya auremu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button