DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa 10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne.
Account 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB, saiki tura evidence of payment ta wannan number 09013718241
Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number 09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa.

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
UMMUH HAIRAN

Qarshen free page na Happy sallah

Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah

5

Shafa kanta tayi tana tausarta saboda tasani iyayenta basason bacin ranta shiyasa take lallabata saboda a gudun abinda kaje yazo amma taci alwashin duk yanda Taheer zaiyi saidai ya mutu aure tsakaninsa da Saudat babu fashi.
Yini sukayi tanata rarrashinta hardai ta samu ta ware Bushirah da Kubrah suka fito cikin shigarsu ta alfarma suka tarar dasu a parlour Mom ta dubesu tace “Ina zakuje?” Cikin yauqi Kubrah tace “zamuje mugano yarmu ne kada Yaya yasamu a blacklist” wata uwar harara ta watsa musu tare da jan tsaki ita kuwa Saudat mutuwar zaune tayi saboda mamaki wai zasuje su gano yarsu yar zinar?

Bushirah ce ta dubi Saudat tace “dama kin tashi munje kya ragewa kanki damuwar son maso wani ko banza kyaganshi acan gurin gudaliyar yarsa da matarsa da yakejin amutu ko a rayu a kanta”
Wasu hawaye ne suka zubo mata ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da kuka ta fahimci a gidan daga Mom sai Dad sune suke sonta yaran gidan gabadaya yan partyn abinda Taheer keso ne hatta da Mahfuz da baya qasar da aka kirashi aka fada masa cewa yayi kema dai Mom shirme kikeyi kinsan dai blood bazai taba yi miki biyayya ba indai akan baben nan ne wlh Mom ni kaina don dai blood ya rigani afkawa ne badon hakaba da tafi haka zaayi, Mom ki share kawai irin wannan auren fah dadine dashi tasanshi yasanta awonsu daidai ne Zaki wani zo ki hadashi da wata qyailar yarinya….”

Kalaman na dawowa Saudat tanajin bugun zuciyarta na qaruwa ta miqe zumbur ta fita ta tarar dasu suna shirin tashin mota ta qarasa da sauri ta bude ta shiga suka kalleta sukayi dariya Kubrah tace “iska tana wahalar dame kayan kara nifa banga abinda zaisa na rinqa bata lkc na akan namijin da baya sona ba musamman Yaya Taheer me masifar tsaurin raayi kinaji fah a gabanki Jabir yake fadawa Mom ita kanta Habeeytah bata tsira daga wulaqancinsa ba idan ya tashi itama da yake iqirarin yanaso kenan balle ke yar karere”
Itadai Shiru tayi batace qala ba har suka dauki hanya suka fara tafiya sunata hirar samarinsu Saudat dai bata cewa komai sai tsiyayyar hawaye.

Sai magrib suka isa suna zuwa sukayi parking suka fito daidai lkcn yana fitowa da waya a kare a kunnensa yana cewa “wlh blood bakaga babyn ba kamar kai itama da Mom take kama nayi Mata huduba da Safeenatul Najah…..”
Katse maganar yayi lkcn da sukayi karo da Saudat yayi baya da sauri tare da tsartar da yawu yace “ke wacce irin banza ce bakya ganine” cikin rawar jiki tace “ban…ban kula ba Yaya Taheer kayi hqr” tsaki yayi ya matsa gurin yan uwansa suka rungume juna dama gaisuwarsu kenan yace “ashe zakuzo na dauka Mom bazata barku ba” dariya Bushirah tayi tace “ai dole abu namu maganin a kwabemu”

Dariya sukayi dukkansu banda Saudat data zubawa sarautar Allah ido ya kama hannunsu suka shiga dakin Granny tana sallah itakuwa Habeey tana kwance kamar gawa saboda shaqar da Mom tayi Mata ta mayar da ciwonta farko, ya saki hannunsu ya matsa ya sanya hannunsa ya tattare Mata gashinta daya rufe Mata fuskarta yayi kissing lips dinta yace “a kowanne hali kyaune dake Habeeytah”
Gyaran muryar Granny yasashi saurin janyewa kunya kamar ya nutse ya juyo tare da sosa kansa ta sakar masa ranqwashi tace “kaikam kwai fitinannen namiji a jinyacen ma bazaka qyale yar mutane ba anya kuwa Taheer ba Mata hudu zan aura maka ba?”

Murmushi yayi yace “bazasu mayemin gurbin Habeeytah ba ita kadai gayyace Granny a duk matan duniya babu wacce zata iya dani sama da Habeeytah” wani mashine ya caki zuciyar Saudat tayi saurin juyawa zata fita Kubrah ta riqo hannunta tace “bakiga yar taki ba don nasan a hannunki qila zata rayu” sake hadiye wata kibiyar baqin ciki tayi ta caki qahon zuciyarta ta nemi guri dabar ta zauna.
Shikam yama manta da an halicceta a gurin surutu kawai yakeyi yana fasaltawa Granny irin son da yakeyiwa Habbatullah tare da zubawa Safnah ido yana murmushi yace “wlh Granny ji nakeyi kamar na hadiye my daughter saboda nakasa fasalta irin son da nakeyi mata nifa yanzu ko ke kikace bakison yata Allah idan muka rabu har abada bare wani banza da rayuwata batayi kama da tasaba dan karere”

Sarai duk wanda yake gurin ya fahimci da wadda yake amma shi har cikin ransa bada itan yakeba, Bushirah ce ta karbi Safnah ta zuba Mata ido tace “wow! Yaya wannan babyn kamar jinin larabawa Masha Allah amma Yaya kamar ba bakwaini ba”
Granny ce “nima da aka haifeta nace ba bakwaini bace saida likitan ya aunata yace kawai dai me girmance amma watanta bakwai da kwana daya a cikin mahaifa yanzu ma ance a daina jagwalgwalata amma wannan dan rawar kan yaqi barinta ta huta” murmushi yayi yace “aini dama komai zanyi ban iyaba indai a gurinki ne tsohuwa dake”
A kasalance Saudat ta taso ta leqa fuskar yarinyar ta zuba mata ido tanajin faduwar gabanta na tsananta a ranta tana raya dama itace ta haifa masa ita qila da soyayyar yarinyar zatasa yasota itama.

Miqo hannu tayi zata karbeta yayi saurin dauke abarsa yaje ya kwantar da ita a kusa da uwarta sai yanzu Saudat ta samu damar kallon Have dake kwance matsayin gawa tayi saurin matsawa gabanta tana furta “lahaula wala quwwata illah billahil aliyul’azeem” hannunta takai zata taba fuskar Habeey yayi saurin riqe hannunta cikin tsawa yace.
“Idan kika kuskura kika tabamin mata wani abu ya sameta wlh sai nayi shari’a dake gabadayanki na tsaneki Saudat….”
Rufe masa baki tayi jikinta na rawa tace “nikuma inasonka a haka Yaya kuma saina aureka Koda kuwa zaka kasheni don qiyayya, Taheer ba takai nakeyi ba yanzu na gama dakai domin ko kanaso ko bakaso saika aureni dole”……….

Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa 10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne.
Account 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB, saiki tura evidence of payment ta wannan number 09013718241
Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number 09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa.

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
UMMUH HAIRAN

6

Tsayawa tayi sake da baki yana kallon ikon lillahi wai saita aurets dole ko a Ina aka taba yiwa namiji auren dole? Murmushin tausayinta yayi shi gabadaya ya gama raina hankalinta hakanan yakejin amai yana taso masa idan ya kalleta.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn wayarsa tayi qara ya daga da sauri tare da kasheta ya mayar aljihunsa kusan ko yaushe a tsakanin jiya da yau sai an kirashi da number qanin na habeey Ibrahim shikuma haushin abinda Addah tayiwa Habeey akan cikinsa yasa yaji ya tsani duk wani wanda ya rabeta basu da adalci dangin Habeey ko kadan basusan darajar dan Adam ba, basu da damu da itaba itace ta damu dasu take sadaukar da komai domin danginta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button