DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Murmushin takaici Granny tayi ta juya zauna daidai lkcn da Dr shattima ya sake shigowa yace “nan da 30 minutes zata iya farfadowa don Allah a kawar mata da duk wani Abu dazai sanyata damuwa” jinjina kai sukayi ya sake fita, haka kuwa akayi 35 minutes da fitarsa ta farka a firgice tana Kiran Taheer kada kayimin haka don Allah wlh nafi kowa sonka kada ka rabani da yata ita kadai na mallaka duk duniyar nan kada ka sanyama yata maraicin uwa a halin uwarta tana raye kada ka qara tabbatarwa da zuciyata namiji tuwon rezar ne miyar Allura ashe wannan ranar zatazo Taheer Kaine da kanka kayimin gori?”
Kuka takeyi Addah na riqeta tace “da nasan wannan ranar zatazo Dana roqi Allah ya kasheni kafin lkcn, wayyoh Allah qirjina Allah ni yaushe zanyi farib cikine kamar kowa….”

Ta qarashe mgnr tans kakarin amai kamar zata amayar da kayan cikinta amma aman yana qara tsanani sai jini, wani ihu Addah tayi ta qanqame yar tata Saudat ta nufota da gudu itama ta riqeta tana kuka tace “nashiga ukuna Taheer kada kayi kisa don Allah ka dawo ka janye kalamanka Taheer asheni ba sonka nakeyi ba ga wacce take sonka…”
Daqyar cikin taimakon Allah Dr Shattima da Dr Zainab suka samu aman ya tsaya suka daura mata na’urar shaqar iska saboda Athmer dinta data tashi tanata gwama numfashi Dr Shattima cikin tashin hankali yaketa fadan ya akayi aka bari ta tuna abinda ya faru?

Wannan rana sunga ikon Allah dukkansu anan suka kwana akanta Kiran duniya Bushirah tayiwa wayar Taheer amma a kashe saita Dad ya Kira ta fada masa abinda yake faruwa shima ya shiga rudu saboda zuwa yanzu tausayin Habeey ya gama ratsa jikinsa yace su jirashi gashinan zuwa.
Haka kuws akayi jiransa sukayi bai dadeba ya iso.
Granny ce tayi masa bayanin komai ya zauna yana salati tare da tunanin mafita a fili yace “aikuwa saidai ya hada biyun ya aura wannan ma zalumcine ya gama lalata mata rayuwa sannan yace bazai aureta ba” da sauri Addah tace “aa kada ayi haka Alh tunda yace bayaso ku qyaleshi matar mutum kabarinsa qila dama ba matarsa bace” duk yanda Dad yaso yabawa Addah hqr ta tubure qarahema tace itafa indai ta isa da Habeey bazata auri Taheer ba.

Jikin kowa yayi sanyi Dad ya dauki takarda da biro yayi rubutu ya miqawa Addah yace “ku riqe wannan don Allah kafin a daidaita komai ina ganin Taheer ba a cikin hayyacinsa yake ba” girgiza kai tayi tace “bama buqatar komai daga gareku ranka ya dade iya hakama min gde Allah ya qara daukaka”
Daqyar ya roqeta ta karba check din kudin sannan ya debe yayansa suka tafi amma banda Bushirah da takejin ciwon abinda ya faru kamar ita akayiwa, sai dare Habeey ta farka ta bude idonta tana kallon silling din maganganun Taheer sunayi mata yawo a kwanya “ballagaza banza me zanyi da ita karuwar yarinyar nan…”

Wata qara ta saki Dr Shattima daya kasa ya tsare ya miqe da sauri ya isa gurinta ya fara dubata ya cire mata abin taimakawa numfashin da aka maqala mata ya zare mata allurar drip din yana Mata murmushi ita kuma sai kallonsa takeyi hawaye na zuba a idonta.
Zama yayi a gefenta yace “idan baki manta da komai kin fawwalawa Allah ba Zaki kashe kanki Habbatullah akwai darasi me yawa a cikin rayuwarki kuma ita qaddara bata shawara lkcn da zata fadowa mutum wlh a iyakar kwanakinki a asibitin nan bantaba sanin Taheer ba mijinki bane sai kwanaki uku da mahaifiyarki tazo, shima waya naji tanayi tana kuka tana fadawa wata halin da kike ciki”

Shassheqar kuka takeyi ta yunqura zata miqe yayi saurin kamota ya tallafa mata ta zauna yace “kiyi hqr muyi addu’a Allah yayiwa kowa zabi na alkhairi amma ni dama nayi tunanin faruwar hakan ba yanzu bako a gaba”
Itadai batace komai ba har ya zauna ya zuba mata ido zuciyarta suya takeyi sosai qaddarorinta sun fara bijirewa kwayarta a firgice ta dago tace “ina yata?” Dago idanunsa yayi da suka kada sukayi jah tunda yake aiki baitabajin tausayin wata mace kamar yanda yake tausayin Habbatullah ba yace “babanta ya dawo ya dauketa kiyi Mata addu’a duk inda take zata isheta” miqewa yayi da sauri ya fice saboda zuciyarsa ta gama karyewa.

A cikin kwanaki biyun da suka qara sosai Addah da Granny ke qarfafa mata gwiwa tare da kafa Mata misalai da hujjoji da zasu sanya ta manta da Taheer a rayuwarta saboda juyin duniya Dad yayi dashi akan ya koma kodan safnah su daidaita da Habbatullah suyi aure Amma fir yaqi yace shifa baisan meye yasa masa tsanarta ba ko sunanta aka Kira gabansa faduwa yakeyi.
Ganin yanda ran Dad ya baci ne yasashi fadawa jikinsa ya fashe da kuka yana cewa “wlh Dad qasan zuciyata danqare take da qaunar Habeeytah amma jikina da ruhina tsanarta suke qarayi Dad bansan meye ya canzamin qaunar Habeeytah da tausayinta zuwa qiyayyarta ba, alfarma days zakayimin Dad kada ka daura aurena da Saudat wlh idan ka daura mutuwa zanyi kabarni na rayu da yata ta isheni rayuwa nayi maka alqawarin kare kaina nayi maka alqawarin zan rinqayin azumin litinin da alhamis”

Lamarin ya fara girmamewa tunanin Dad duk yanda yake tunanin Taheer ya wucce nan kamashi yayi ya dagashi zuwa yanzu ya daina ganin baqin dannasa tausayinsa yakeji a sanyaye yace “bazan taba takura maka ka auri abinda ranka bayaso ba amma zamanka haka risk ne kayi hqr ka auri yar uwarka Saudat nasan zakaji dadin hakan a gaba Taheer inajin kunyar na kira sahabi na fada masa na fasa aurawa dana yarsa shi tunani yakeyi na isa dakai kayimin wannan alfarmar Taheer”
Miqewa yayi yana hada hanya ya shiga bangarensa ya fada gado yanajin qirjinsa yana zafi ya zubawa qaton hotonsa da Habbatullah ido yana kallon yanda suke cikin nishadi lkcn da sukayisa yana kukan zucci qaunarta tana qwaqular qasan zuciyarsa amma ya kasa gane hakan yanda ya zuba mata ido yana kallonta har wani buda hannunsa yakeyi wai ta shiga qirjinsa.

Kwana biyu suka qara Granny ta rakasu har Gombe har sukaje Habeey na kwance a kafadar Granny zuwa yanzu ta daina kukan rabuwa da Taheer kukan rabata da yarta takeyi a sanyaye tace “don Allah Granny ki kawomin Safnah naganta nayi Mata addu’a Ina roqon Allah kada yakaita lkcn da zata dandani irin abinda ubanta ya dandanamin, Allah kaji qanta ka tausaya Mata kada ka juya sakayyar bataji ba bata gani ba a kanta Allah ka rayamin ita rayuwa me albarka, shikenan yanzu Granny bazan qara ganinta ba?”..………

Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa 10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne.
Account 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB, saiki tura evidence of payment ta wannan number 09013718241
Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400  ta wannan number 09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa.

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
UMMUH HAIRAN

8

Sosai kalamanta suka ratsa zuciyar Granny jin kukan nata takeyi kamar tana dora mata dutsi aqirjinta a hankali taci gaba da rarrashinta har suka isa gidan sukayi sallama da Granny akan cewa idan an gama biki zasu dawo suga yanayin jikin Habeey.
Tunda suka shiga ta qule daki taja bargo ta rufe jikinta sanyin zazzabi yana ratsata tana nunka nadamarta tanajin ninkin tsanar jinsin da namiji a zuciyarta, ashe dama muguntar da Taheer ya shirya mata kenan ya nace saita soshi saida ya koya mata sonsa sannan ya juya Mata baya ya rabu da ita rabuwa mafi ciwo a lkcn da tafi kowa buqatarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button