DUBAI PART 2

Yanayi mata wankan yana wasa da jikinta yanajin feel dinsa na qaruwa daqyar ya gama yimata wankan hakanan yaji yana sha’awar ya daura Mata alwala yayi Mata alwala ya daukota ya bude cikin wardrobe ya zubawa wardrobe din ido kayansa ne da nata a jere komai sabone yayi ajiyar zuciya wannan yasan aikin Abba Sahabi ne.
Wata baqar doguwar riga ya dauko ya juyo ya wareta ya kalleta yace “kinasonta baby?” Zuba Mata ido yayi sai kuma ya ninketa ya mayar yace “nasan bakison baqin kaya bari na dauko miki ja” wata jar doguwar riga ya dauko ya bude wata wardrobe din ya dauko jajayen band da dankunne fashion shima ja ya dawo ya ajiye ya dauko wasu mayuka masu masifar kyau da tsada ya matsa ya shafa mata ya taje Mata kanta a hankali sannan ya sanya band din ya daure mata ya kama jelar gashinta ya tufke kamar yanda yaga tanayi masa.
Kayan ya saka mata ya fesa mata turare ya koma gefe yana kallonta yana ajiyar zuciya tare da murmushi yace “Rayuwata inasonki” shima wanka yayi ya dauko wani blue din jeans yasa ya dauko jar riga yasaka ya kalleta yace “nayi miki kyau My life?” Murmushi yayi ya matsa ya lakace mata hanci ya fita yana cewa jirani na dauko alluranki…”
Turus yaja ya tsaya ganin Mom dinsa a tsaye a parlourn ita da Saudat ya kallesu a wulaqance, a zahiri kallonsa ne a haka indai ba saninsa kayi ba zakace tsabar iskanci ne, jikin Saudat rawa ya fara yasa hannu ya karbi Safnah dake hannunta yace “lafiya da safen nan?” Yanda Mom taga yanayinsa babu damuwa da Kuma kalaman da taji yana furtawa ya fadar Mata da gaba amma saita dake tace “dama munzo ganin jikin matar takane” murmushi yayi daya bayyanar da kyawawan haqoransa yace da sauqi fa sosai shiga ki ganta Mom har kwalliya nayi Mata”…….
UMMUH HAIRAN
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2
13
Zaro ido Mom tayi tace “kwalliya kuma gawar kayiwa kwalliya?” Tsuke fuskarsa yayi yace “aa Mom banason ki qara cewa matata gawa qila saima ki mutu ki barta waike meye yasa kullum bakinki baya taba fadin alkhairi akan matata ne nifa banson irin haka wlh rai zai iya baci”
Sakin baki tayi tana kallonsa har ya gama fadansa ya juya ya koma dakin ya kwantar da Safnah kusa da mahaifiyarta ya miqe domin fitowa suka hada ido da Mom ya sake tsuke fuskarsa yace “banason a dameta muje parlour” murmushin takaici tayi tace “indai wannan hoton hotiho dince da kanka zata isheka Taheer tunda ta zama Liability komai sai kayi mata”
Ko sauraronta baiyi ba ya dauko feedar Safnah ya zauna ya daukota yana Mata wasa ya hada mata madara ya jorner mata ganin bashi da niyyar basu guri yasata cewa da Saudat “ki zauna ki tayashi aiki”
Dagowa yayi ya watsa mata wata uwar harara ya mayar da kansa wa yarsa har saida Mom ta kusa ficewa daga dakin yace “dallah malama ki bacemin da gani anan banza mayya uwarki zaki tsaya kiyimin nida matata sai ansamin ido idan wani abin nayi niyyar yimata jiya da ubanwa muka kwana”
Tsorone ya kama Saudat tasan tana cewa wani abu jibgarta zaiyi ita ta rasa Ina Taheer ya kwaso wannan baqar zuciyar tasa, bin Mom tayi da sauri har ta fita ta dawo tace “am Yaya Safnan fa?”
Wata uwar tsawa ya daka Mata yace “uwarki ce ta haifamin ita da yazama dole na baki ita?” Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tace “amma dai Yaya kasani yar yar’uwata ce nima inada haqqi akanta…”
Wani kallo da yayi matane yasata ficewa da gudu ta nufi bangaren Mom din tana zuwa tayi kicibis da Mahfuz ya daka Mata tsawa yace “ubanme kike yiwa wannan uban gudun ballagaza kawai kizo ki shirya ni bazan iyada da zafin 9ja ba komawa inda na fito zanyi bandama su Dad da abinsu wani ni zaace na tafi dake ke wlh bama zan tafi dakeba kawai kice musu na tafi”
Yana gama fada Mata haka ya juya ya fice da sauri ta tabe baki tace “banza a banza duk izzarka baka kama qafar Hussain dinka ba, batakai nakeyi ba”
Shiga ciki tayi ta fara hada kayanta tare da cin alwashin ba zata qara kwana uku a 9ja ba ko su Abba bazasu koma ba ita zata tafi,
Itakuwa Mom tana shiga dakinta ta dokawa Hajiya Ummah waya tace “gsky Ummah banga alamun nasaraba shegen yaron nan bazai sare ba wlh bakiga yanda yake rawar qafa akan yarinyar nan ba abin haushin iyayensa sun daure masa gindi duk wasu shagunansa Dad ya sanya yaransa a ciki zasuke juya masa dukiyarsa sannan har wani albashi ya yanka masa hatta mara lfyr saida ya yanka Mata salary”
Dariya Ummah tayi tace “shine me da har zai sanya ki sare Safinah yau da gobe fah sai Allah wlh dole sai Taheer ya gaji da jinyar yarinyar nan Kuma duk ke kika bata abin aida kin bari sun tafi wajen inda babu wanda zai taimakeshi da komai”
Shiru tayi tana tunani kafin tace “Germany fah zasu tafi nafiso su tafi inda basuda kowa…” Katseta tayi da cewa “ki aiwatar da aikin da aka baki kawai kice da Excellency ya kadasu su tafi acen din komai zaifi tafiya daidai kuma kada ki yarda a bar miki yarinyar nan ya tafi da kayarsa kinga itama qarin wahala ce”
Dake lusara ce haka ta yarda cikin farin ciki ta rinqa gudanar da al’amuranta cikin dare ta tashi batare da kowa ya ganta ba ko tsoron girman gdan bataji ta shiga bangaren nasu Taheer tayi saa ko lkcn daya fito zai raka likitan Safnah ta fara kuka ya koma da sauri bai dawo ya rufe ba bayan yayi Mata wanka ya hada Mata madararta ya bata ya dorata a kafadarsa tayi bacci ya kwantar da ita a gadonta ya koma ya daga Habeey ya gyarata yayi mata wanka ya dawo dawo da ita ya kwantar da ita.
Shima ya gaji saboda haka yana kwanciya bacci ya daukeshi har cikin ransa yafi tausayin Abba Sahabi fiye dashi kansa saboda yanda duk ya susuce akan ciwon na Habeey yau sun dade dashi suna tattaunawa akan ciwon yana cewa dashi yana shirya musu tafiya Saudia Wani Islamic Hospital akwai abokinsa acan yace yawanci irin wannan ciwon biyu ce take haduwa kodai tanada junnu a tare da ita ko kuma an jefeta dasu abin ya tadda ciwon, saboda haka Dr Manzir ya bashi shawarar a kawota nan a dorata akan magungunan Islamic.
Yaji dadin shawarar ta Abba Amma yace da abban yayi Shiru harsai komai ya kammala na tafiyar, nan Abba yake fada masa cewa mahaifiyar Habeey dinma batada lfy cikin dare aka jita tana ihu kamar mahaukaciya tun daga lkcn itama ta daina magana saidai kallo kawai ta kwatance Kuma bama kowanne mutum take ganewa ba yanzu haka tana Ɓillire gidan mahaifinta anata sauke mata qur’ani.
Jinjina kai Taheer yayi yace “amma lamarin da daure kai kuma Ina mijinta da yayanta maza da sukayi saura?” Girgiza kai Abba yayi yace da Taheer “tun ranar data tashi da ciwon da safe kafin kowa yazo kanta akace yazo ya tattare yayansa maza ya tafi dasu har jiya baa qarajin duriyarsu ba” da wannan tunanin bacci ya dauke Taheer nasararsa daya shi ko bazaiyi nafila ba baya kwanciya babu alwala Kuma ko iskancinsa yayi daya gama yake wanka wannan dalilin yasa hatta Habeey da batasan waye a kanta ba sai ya daura Mata alwala duk lkcn da zaiyi sallah.
___________Itakuwa Mom tana shigowa ta kunna turaren tsafinta ta banka a parlourn ta tsaya idanunta a rufe hayaqin yabi ta qasan qofar dakin ya shiga daidai lkcn Taheer yana saman sallaya yayi sujjadah yana nemawa matarsa sauqi gurin me duk.
Bajewa hayaqin yayi sannan ya nufi jikin Habeey dake kwance kamar gawa ya rinqa kewayeta abin mamaki hikima ta ubangiji Taheer yana cikin sujjadar nan kawai sai yaji motsi a saman gadon ya dago da sauri yayi tahiya yayi sallama yanajin Motsin na qaruwa baidai juya ba tunaninsa Safnah ce ta tashi.
Ji yayi anyi attishawa hakanne ya basa damar dago idanunsa da sauri ya saukesu akan gadon kawai sai yaga Habeey ce take motsawa bakinta yana furta “ LA’ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM, ASHHADU ALLA’ILAHA ILALLAH WA’ASHHADU ANNA MUHAMMADUN ABDUHU WARASULIHI”………