DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA:    HABEEYTAH
DUBAI PART 2

15

Hamdala Abba yayi yace “kasanar da yayan?” Ce masa yayi “aa ban fada masa ba tukunna” “aje waya” ya fada tare da miqewa aunty Zahra dake kwance a gefensa tace “waye ya mutu?” Juyowa yayi ya kalleta yana zura jallabiyarsa yace “bangaren Taheer zani Habibatullah ta farka dare jiya” dafe qirji tayi a firgice tace.
‘what wanne irin farkawa yanzu kuma ana zaune qalau Abba?” Yanda tayi maganar yayi bala’in fadar masa da gaba amma bashida lkcn sauraronta ya zura siliper dinsa ya fice da sauri ya nufi bangaren na Taheer.

Yana zuwa ya kwada masa Kira bugu biyu ya daga ya janye bakinsa daga na Habeey da yake qoqarin bawa kashi ya daga wayar da sarqewar murya Abba yace “nakasa jurewa Taheer kazo ka budemin qofa na ganta”
Miqewa Taheer yayi yana gyara zaman wandonsa ya fito yana miqa ya budewa Abba qofar parlourn yayi masa jagora har dakin baccinsu inda Habeey take kwance saman gadon ya lullubeta da duvet.
Kunna swech din fitilun dakin yayi idanunta na lumshe har yanzu tana tsiyayar da hawaye, matsawa yayi gabanta ya kamo hannunta yace “Habibatullah!”

Bude manyan lumsassun idanunta tayi tar a saman fuskar mahaifin nata tana kallonsa kallon tsoro da fargabar yau Kuma da wanne mummunan labarin yazo mata? Durqushewa yayi ya rungumota jikinsa zuciyarsa na bugawa da qarfi ya fashe da kuka yace.
“Haqiqa bazan taba yafewa Hajar ba Habbatullah ta cutar dani ta cutar da rayuwata ta wulaqantamin jinina Habbatullah Ina raye wadannan munanan qaddarorin suka rinqa faruwa gareki wayyoh Allah kaico Na ni Salahu Allah ka yafemin ka yafewa yata kada ka tuhumeta da laifukanta ka rubuta matasu a matsayin qaddararta”

Wani sanyi ne yake kwarara zuciyar Habeey ta qara lafewa a jikin Abba tana kuka me tsuma zuciya tace “meye yasa ka banzatar da rayuwata har ta fada cikin kwale²n da bazata taba fitowa ba nasan zan dawwama na qare rayuwata a qunci da nadama yakai mahaifina kunyi wasa da rayuwata kaida Adda wanda nasan da baka barmata ni ba da abubuwan da suka faru dani basu faru ba, nikam kayi hqr nayi murnar ganinka a matsayin ubana amma bana buqatar wani Abu a yanzu gareka ku barni na qarasa rayuwata cikin qaddarata….”

Ji tayi an saki wani ihu an rungumeta sai kuma taji an fashe da kuka me shiga jiki ta juyo da kanta kawai sai taga matashiyar kyakkyawar budurwar da Taheer ya nuna Mata a asibiti yace matarsa zata riqe masa yarsa.
Rintse idonta tayi lkcn da taji bugun zuciyarta ya qaru yanzu ya tabbata Taheer mijin wannan yarinyar ne?” Kukanta ne ya qara sauti ta qara qanqame Abba tana rintse idonta zuciyarta na bayar da wani sauti fat-fat.
Gaban Abbane ya shiga faduwa yayi saurin dafe mata qirjin yace “me…meye yake daga miki hankali haka meye yake neman tashin ciwonki?” Da sauri a galabaice ta nuna Saudat da taketa kuka ta matso gabanta tace “kada ki riqeni a zuciyarki yake yar’uwata alaqata dake ta fiyemin duniya da abinda yake cikinta wlh tun ranar da nasan cewa Yaya Taheer jinina yake haukanso har ya tsaneni saboda ita nasan cewa ke yar’uwata ce dana dade Ina mafarkin haduwa da ita Aunty Habbatullah tun a ranar na sallama miki mijinki indai don wannan ne Aunty Habbatullah ki saki jikinki dani ko mutuwa kikayi na haramtawa kaina auren mijinki….”

Tana gama fadin haka ta miqe ta fice a guje Habeey ta miqa hannu zata riqota amma tariga ta fice daidai lkcn da Mom ta danno ta shigo da sauri ja tayi ta tsaya turus tare da murje idanunta ta matsa ta qara haska fuskar Habeey da wayar hanunta ta tabbatar itace.
Ja tayi da baya da sauri Taheer ya matsa yace “kinga ikon Allah ko Mom jiya da dare wajen qarfe uku saura ta tashi….” Daukeshi tayi da wani kidimammen mari ta danna masa zagi tace “ina ruwana Taheer Ina ruwana da farkawar wannan shegiyar yarinyar nifa bari kaji Taheer na tsani Habeey kuma bazan taba sonta ba har abada wai garin yayama ta farka ita da akace zatayi shekara a kwance?”

Tsoro da mamakin yanayin tashin hankalin da Mom ta shiga ya bayyana a fuskar kowa shikam Taheer tuni idanunsa suka rine sukayi jawur da bala’i yace “to ba saiki hana Allah ikonsa ba tunda kina baqin ciki ta tash…”
Wata uwar shaqa tayi masa data firgita Dad da yake shigowa dama Abba tace “na rantse da Allah indai ni Safinah nice na dauki cikinka watanni tara na tsugunna na haifeka saika saki Habeey saki uku kamar yanda ka saki Saudat yar qanwata da nasha nono na saki uwarta takama”
Bazai saki ba taji an furta a bayanta ta juya da sauri kawai sai taga Granny ta matso tace “sakeshi butulu marar mutunci”

Sakinshi tayi tana haqi Granny ta dubi dai tace “duk ranar da Safinah ta qara furta danta ya saki jikata Habbatullah bazan hanashi ba domin uwarsa ce tanada matsayi a gurinsa amma kuma nima zan murda nawa kambun domin nima uwarkace Aliyu nasan bazakaqi yimin biyayya ba domin dama Safinah zabina ce, wajibine Habeey bazata bar qarqashin igiyar auren Taheer ba harsai ka fara rattabawa Safinah saki uku tukunna kaga zawarcin zaifi ma’ana uwa nayi ya nayi”
Juyawa tayi ta kalli Taheer tace “kaikuma na dawo gareka ka tattare matarka da duk abinda kasan zata buqata ka dawomin da ita gdana dama baayi mata gyaran amarci ba itama a gyarata idan ta qarajin sauqi ta tare a gidanka ba gdan ubanka ba inda zaa hanaku rawar gaban hantsi bance ka saurara Mata ba domin zabinka ce kuma horonka ce Taheer kayi komai ba komai takace har abada so nake nan da shekara biyu naga gdanka ya cika da yara kaji Lelen Granny”…………….

Sorry sisters yau kunjini Shiru kuyi manerge da wannan zuwa tomorrow muga abinda zai wakana tunda Granny tabawa jarumin mu damar yayi komai ba komai

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number dake sama.

17 Qwanqwasa qofar da akayi yasashi tashi a gajiye ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa ya tsaftace jikinsa ya fito ya sanya kayansa ya juya ya kalleta tanata binsa da kallo har ya iso gareta ya dagota a hankali ya rinqa taimaka mata tasa kayanta ya hade mata magungunan ta ya kamata a hankali tana daga qafarta a kasalce har suka fito Dad shidai baiso tafiyar ba yaso su zauna a kusa dashi amma Bai Isa yaja da hukuncin tsohuwar tasa ba.
Ita kuwa Mom tana sama ta zubawa Taheer da Habeey idanu tana qare musu kallo Koda bata qaunar Habeey tasan duk fam dinsu babu mace me kyawun halittarta wai a hakama don ta rame babu rabinta, numfashi ta sauke ta saki labulen tace “wlh indai ina raye sai ka rabu da yarinyar nan Taheer kyau! Kyau shine yake rudarka zan samo maka wacce tafita kyau da…” Saikuma tayi shiru saboda tasan intai mgnr nasaba yanzu ta zagi kanta ne kakan Habeey shine ya saki nono ya bawa ubanta saboda haka kininsu gudane.

Dafe kanta tayi tace “ko Zahrah ce tunda bansonta bansonta” tanajin tashin motarsu ta figi mayafi ta fice fuuuu ta shiga mota tabar gdan ta nufi gdan Ummah anan suka hadu da Zahrah suka dunguma suka nufi dajin falgore gurin wani bokan Hajiya Ummah.
Bai barsu sun masa bayani ba yace “nasan komai watsattsu nasan abinda ya kawoku danki yayi aure ya auri yar uwarsa wadda baki qauna to shakka babu wannan aure babu rabuwa an daurashi kenan yar qanwarki saidai ta rungumi sorry akwai so akwai qauna sannan akwai rabo”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button