DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

23 Kwanakine masu tsayawa a zuciyar masoya zamane me cike da qauna da tattalin juna, so qauna da kulawar da Taheer yake bawa Habeey abin gwanin burgewa wa kowa itakam salon soyayyarsa har kunya yake bata, abu daya da yake damunta dashi shine fitinarsa,
Ko yaushe idan yana gda yana liqe da ita Kuma ko ya fita baya wani dadewa zai dawo yace mata so yake yabawa shukarsa ruwa idan taqi Kuma yasa mata qarfi yayi abinda zaiyi bayan ya gama yayita yimata dariya yana cewa ai tama fisa jin dadi kawai don dai shi aka dorawa jarabar ne.
Cikin wannan kwanaki na farkon zuwansu abubuwa da dama sun faru abun da takasa mantawa shine kyautar wata siririyar sarqa da barimarta da Chan’s din hannu dana qafa sai zobe da yayi mata na white gold and diamond da kudinsu a qimance suka haura lissafin da qwanyata zata iya yace mata.

Tun washegarin ranar da tayi masa kyautar budurcin ta ya bayar da aikin qera masa su da qudurin duk ranar da suka kwana suka tashi cikin yanci matsayin ma’aurata zai batasu a matsayin tukuicin qauna,
Ranar tayi kuka sosai itakam batasan irin qaunar da dan’uwanta Kuma mijin nata yakeyi Mata ba,
Abu na biyu shine mugayen mafarkan da takeyi da Mom da Aunty Zahrah kullum sunayi mata gargadi akan kada ta kuskura ta dauki Taheer a matsayin abokin zama na dindindin saboda talala sukayi mata me kamar sake.
Wannan abu yana damunta musamman lkcn da ta fara mugayen mafarkan wai Taheer ya kamata ya nada mata duka ya saketa saki uku ko kuma tayi mafarkin ya biyota da bindiga ko wuqa zai kasheta.
A kowanne lkc takan tashi tayi alwala tayi sallah tare da tubarwa Allah da neman daukinsa wajen galaba akan maqiyanta.

Duk sanda sukayi waya da yar’uwarta Saudat takance mata Aunty Habbatullah ki rinqa kusanta kanki da ubangiji akwai maqiya gabanki da bayanki don Allah kada kiyi wasa da addininki nasan Allah zai iya miki Ina tsoron lamarin Hajiya Ummah Mom da Aunty Zahrah bansan me kika tsare musu ba da suka sakoki a gaba basa iya boye qiyayyarki sai a gurin mazajensu.
Takance “karki damu qanwata wata qiyayyar batada dalili hakanan Allah yake kimsawa bawa ita a cikin zuciyarsa kedai ki tayani da addu’a kawai”
A haka har sukayi watanni uku a U.S.A, a wannan lkcn ne Kuma abubuwa suka fara canzawa tsakaninta da mijinta babu kyara babu habaici saidai kawai idan taganshi taji gabanta yana faduwa takan danni zuciyarta da addu’o’i sannan ta tareshi suci gaba da rayuwarsu, to shima a bangarensa mugayen mafarkai ne suka aureshi ga wani mugun zargin Habeey da yakeyi a zuciyarsa hakan da ya fita sai zuciya ta rinqa raya masa gatacan tare da wani namijin a gdansa.

Babu shiri zai dawo ya gama dube dubensa bazaiga kowa ba lamarin da yake sanyashi shiga tashin hankali shidai yasan ko lkcn da suke zaman dadiro baya zarginta to meye yasa a yan kwanakin nan zuciyarsa takeqin nutsuwa da itane?
Tambayar da yakeyiwa kansa kenan amma bayada me amsa masa saboda haka ya barwa zuciyarsa yaci gaba da addu’a kawai,
A wannan taqinne kuma ta rinqa rashin lfy ciwon bazai tashi ba sai dare ta kwana tana sheqa amai da safe Kuma saita warware suna zuwa asibiti ana aunata akace shigar ciki gareta.
Wayyoh zo kuga murna gurin Taheer kamar ya hadiyeta haka yakeji itama tayi murna saboda kadaici yana damunta ga qulafucin yarta Safnah data sanya a ranta to shima gogan hakane don ko qofar gdansu ya fita saiya shigo da tsaraba yace ta Safnah ce.

A ranar da suka dawo gda zazzabinta ya tsananta ga faduwar gaba data aureta cikin kwanakin nan ko qofa aka taba sai gabanta ya fadi, dakewa kawai takeyi saboda kada abin yayi masa yawa.
Da dare tanajinsa wayarsa tayi ring tana rungume a jikinsa ya daga suka gaisa da Dad yake cewa dashi “eh wlh dazu mukayi waya da Abba nake fada masa mun samu qaruwa My life cikine da ita amma tanashan wahala yanzu haka kaganta a jikina zazzabi ya hana mata sakat”
Murmushi Dad yayi yace “zataji sauqi dama qaramin ciki sai a hankali ai” hakanan sukayi sallama ya aje wayar baiyi minti goma da ajiye wayar ba ya fara lalubarta a cewarsa idan ya jijjigata zataji sauqi,
Wayar ta qarayin ring ya janyo ganin number Mom yayi kamar bazai dagaba Habeey tace “Allah My life ring dinnan fadarmin da gaba yakeyi ka daga”

Karawa yayi a kunnensa kawai sai jinta yayi tana huci tace “wato harma dama ka samu kayiwa wannan shegiyar yarinyar ciki ko aikuwa baka isaba ni nama gaji da zamanta a qasar nan tana qara nisantani dakai kayi gaggawar hadota da kayanta ta dawo gda tayi rainon cikin anan”
Ajiyar zuciya yayi yace “bansan meye yasa kikasa mana ido ba Mom kodai kina daya daga cikin matan da suke kishi da matan yayansu ne haba don Allah Habeey fa zabina ce kuma yar’uwata ce kodon zumunci yakamata ki sassauta mana mu samu salama a rayuwarmu”
Yana farin haka ya kashe wayar yaci gaba da abinda yakeyi itama tana tayashi saida suka gamsar da junansu sannan sukayi wanka suka kwanta.
Me zai faru? Cikin dare yaji Habeey tana buge buge tana kiran sunansa ya zabura ya miqe ya dagota jikinsa yana Kiran sunanta amma Shiru sai surutai da takeyi daya kasa gane me take cewa jikinta yana qara daukar zafi tana rirriqe cikinta,
Hankalinsa yayi masifar tashi ya sake matseta a jikinsa yanata yi mata addu’a, kusan awa guda sannan ya samu bacci ya dauketa yayi ajiyar zuciya ya miqe ya dauro alwala ya tada sallar asabu da lkcn ya riga ya shiga itakam sai safiya ta tashi yanata yimata sannu yana binta da kallo tare da tambayarta inane yake mata ciwo,

Kallonsa takeyi da alamun rashin fahimta tace “meye ya hana ka tasheni nayi sallah akan lkc?” Murmushi yayi yace “bakida lfy ne shiyasa”
Dirowa tayi daga gadon tace “tunda ka riga ka hadani da aiki lfy kam ai sai Allah ya rabamu tukunna nidai kada ka qara barina nayita bacci har lkcn sallah ya wucce don Allah” mamaki ne ya hanashi cewa komai saboda ya lura batamasan meye ya faru da ita jiyan ba so shima bai bawa abin muhimmanci ba ya shiga kitchen ya hado musu abin karyawa ita Kuma tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin wani yadi mara nauyi dinkin riga da siket ta fito parlourn yana zaune a dinning yana jiranta kamar yanda suka saba ya miqe suka rungume juna tare da tsotsar bakin junansu yace “kin wahalar min da baby jiya da dare fatan kinji sauqi dai Kuma bazaa Kuma ba?” Murguda masa dan qaramin bakinta tayi tace “idan kabani hutun sex ba” dariya yayi yace “tabdi aikuwa kina ruwa”

Zama sukayi suka fara breakfast cike da nishadi idan ya kalleta wani dadi yakeji inda ita kuma gabanta yaketa faduwa,
Matsowa yayi jikinta yace “bansan me kika sanya a ranki haka ba cikin wata daya zuwa biyu sai ramewa kikeyi My life don Allah ki cire ko menene muyita addu’a kinji”
Dago kanta tayi idonta ya ciko da ruwa tace “ciwon faduwar gaba ya sarqeni sama da wata guda shi kadai lalata farin cikin mutum yakeyi balleni da dama ba lfy na cika ba Kai shaidaine akan hakan sannan kuma kullum cikin tararrabi da tunanin yaushe mafarkaina zasu fara tabbata nake duk da ina addu’a amma inajin kamar zasuyi nasarar rabani dakai Taheer…”
A razane yace “su waye!” Yanda yayi mgnr da qaraji yasata firgita tace “A baya fuskar mutum uku nake gani amma yanzu basu nake gani ba fuskar Pappa nake gani kullum yana firgitani tare da cemin saiya cusa maka tsanata saika tsaneni fiye da yanda ka tsani mutuwarka Taheer idan hakan ta qara faruwa dani ya zanyi a baya ni kadai ka tsana amma yanzu bansan mu nawa zaka tsana b….”
Rufe mata baki yayi yace “to Kuma wanne Pappan bayan Pappa ya mutu anya Habeey bakida aljanu kuwa?”
Kuka ta sake rushewa dashi tace “kaima abinda Addah tace shi ka maimaita Taheer ni kadai nasan abinda nakeji a jikina wani lkcn ji zanyi kamar tsutsa tanayimin yawo a cikin jikina na rasa meye matsalata anya Taheer ba mutuwa zanyi ba….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button