DUBAI PART 2

Fita sukayi da jaririyar da nufin kaita dakin da zaake kula da ita Taheer dake zaune ya hade kai da gwiwa sai bugawa zuciyarsa takeyi ya dago da sauri ya nufosu Dr yayi masa murmushi yace.
“Anyi nasarar ciro maka baby girl dinka tana cikin qoshin lfy saidai batakai lkcn haihuwa ba zaa kaita dakin kulawa ita kuma uwar tana cikin halin commer sakamakon hatsarin jijjiga data samu saidai ku tayamu da addu’a Allah ya dawo da ita cikin hayyacinta nan da qarfe biyun rana idan ba hakaba komai zai iya faruwa.
Ba Taheer ba hatta Granny saida cikinta ya kada wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace “Dr kada kuyi sakaci don Allah Tanada muhimmanci a rayuwata” dafashi yayi yace “insha Allahu komai zaizo da sauqi”
Matsawa yayi ya leqa fuskar yar tasa kyakkyawa da ita ya sauke ajiyar zuciya tare da miqa hannu ya karbeta ya zauna ya zuba mata idanu yanajin wani tausayin kansa da Habeey da Kuma yar tasu da yake fatan ta zame masa raba gardama ko kamar da yarinyar takeyi da Mom dinsa ya isa yasa zuciyar Mom tayi sanyi tabarsa ya auri Habeey dinsa.
Da wadannan tunane tunanen Granny ta matso ta kalli yarinyar tace “masha Allah Lele kamar kumbo kamar katanta ga tukuicin sabawa ubangiji nan ka samu sai kayita kallonta a matsayin yar zina…” Ji yayi qirjinsa ya buga yace “Granny don Allah kada ki qara fadamin haka nifa banson a dangantamin yata da laifin dana aikata ba ita tayiba”
Karbarta likitan yayi yace “muna buqatar jini uwar ta zubar da jini sosai zaa daura mata” miqewa yayi yace “zaa iya diba a jikina jininmu iri dayane”
Dakin da zaikai babyn ya shiga yayi Mata abinda ya dace sannan ya dawo suka nufi Lab suka debi jinin nasa duk da haka saida aka nemi qarin leda daya aka siya aka sanya mata.
Ranar a asibitin dukkansu suka kwana saida asuba Granny tace yaje ya nemo musu kayan amfani ya kawo musu, aikuwa taga hauka kaya kamar zasu bude shago ya kawo musu lkcn da aka fito da kayan fada Granny ta farayi tace maza ya rage yakai gda aiba dawwama zasuyi a asibitin ba.
Zama ya nemi guri yayi yace “saidai ki rabar bazasu koma ba gdanma akwai ukun wadannan” bata qara cewa komai ba ta koma ta zauna tare da kiran wayar governor Waziri.
Tun jiya yake Kiran wayar Taheer yaqi dagawa ganin kiran mahaifiyar tasa yasashi dagawa da sauri zuciyarsa na bugawa saboda tunanin ko meyene dalilin Kiran da safe haka.
Sallama yayi mata tace “lfy Lau Wazir ka fadawa Safinah Habeebah budurwar Taheer ta haifi ya mace me kama da ita yanzu haka muna tare anan azare…” Wata firgita Alh Waziri yayi yace “what Inna haihuwa kuma? Wai dama da gaske yaron nan yakeyi ciki yayiwa yarinyar nan haba Inna ya zakiyimin haka don Allah ya zaayi ki daurewa yaron nan gindi yaci gaba da iskancinsa kina gani fah tun jiya da mukayi masa mgnr sa ranar aurenss da Saudat ya fice bai sake waiwayenmu ba kiran duniya yaqi dagawa qarshe ma yasa uwarsa a blacklist haba Hajiya wannan ai zubar mana da qimane da mutunci, kamarni ace…..”
Katseshi tayi da cewa “koma mene aikin gama ya gama Taheer yayiwa budurwarsa ciki ya kawomin ita gata a hannuna kuma dama ai tarbiyyarku ce hakan abinda yaranku sukeso shi zakuyi musu saboda haka shima ku barshi da abinda yakeso sannan qaddarar yaya tanakan kowa itama ba haks iyayenta sukaso ba rubutun tawadar ubangijine sai ta hadu dashi sunyi wannan abin kunyar”
Kashe wayarta tayi ta karbi babyn a hannun Taheer dake shigowa ya zauna yana kallonta tana goge mata jikinta tana shafa Mata zaitun tare da tofa Mata addu’o’i a jikinta tasa mata Pampers ta sanya Mata kayan sanyi tace “kayi mata huduba kuwa?” Girgiza kai yayi ta Kuma cewa “saboda me?” Bude runannun idanunsa yayi yace “na rasa sunan da zansa Mata Granny” murmushi tayi tace “kasa Mata Safinatul Najah” da sauri ya dago yace “sunan Mom?” Daga masa kai tayi tace “eh akwai ma’ana a cikin hakan”
Ajiyar zuciya yayi ya karbeta yayi mata hudubar yanajin qaunar yarinyar tana mamaye duk wani gurbi da qaunar uwarta ta rage a zuciyarsa dagowa yayi yace “tun ranar da na fara bata rayuwar Habeeytah Allah ya jarabceni da qaunarta har inajin kamar mutuwa zanyi idan ban aureta ba Granny nasani Habeey batasona saboda tana kallona kallon mafi munin qaddararta don Allah ki shigemin gaba muyi aure da ita badon kaina ba saidon maslahar rayuwarmu dukkanmu da ta Safnah”
Mamakine da tausayinsa ya cika zuciyar Granny ta dafashi ya dago kansa kawai sai taga hawaye yana shatata a idonsa tace “subhanallahi Lele meye kuma abin kukan a cikin wannan lamarin mutum ko yaqi Allah ai bazaice maka aa ba saidai babbar matsalar shine daidatawar yarinyar nan da mahaifanta”
Share hawayen yayi ya miqe ya matsa gaban gadon da take yace “ban damu da kowa yaso tarayyata da Habeey ba burina kawai itan ta amince dani ta daina yimin kallon da takeyi min Granny inason Habeeytah nini kadai na dace da zama mijinta saboda nine silar kowacce irin lalacewa tata”……….
UMMUH HAIRAN
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2
FAUZIYYA TASI’U UMAR
UMMUH HAIRAN
Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah
3
Kansa ya dora a qirjinta yaji yanda numfashinta yake sauka so slow ya shafa fuskarta ya sauke murmushi ya kwantar da babyn a kusa da ita ya fice, Granny miqewa tayi taje ta tsaya kan Habeey ta zuba Mata ido gabanta na tsananta faduwa har baccinta irin na Sahabinta ne hatta fatarta itadai wannan kama tana bata mamaki tabbas da ace sahabi yana qasar nan da zatace wannan yarinyar akwai wani Abu da ya hadasu.
Komawa tayi ta zauna tanaci gaba da kallon fuskar Habeey a fili tace shekara goma sha tara kenan da sahabi ya koma England da zama baitaba zuwa ba Koda ziyara, share hawayenta tayi tace “idan na mutu qila zaizo”
A haka Dad yazo ya sameta a firgice ya shigo ta miqe da sauri ya daidaita tsaiwarshi yace “haba Inna meye hak…..” Maganarce ta maqale a bakinsa lkcn daya sauke idanunsa akan fuskar Habeey maimakon ya qarasa abinda yake Shirin fada sai ya qarasa da fadin “Sas…sahabi”
Kallonsa Granny tayi da sauri tace kaima ka gani ko Aliyu na dauka ni kadaice nake ganin kamar nayi tunanin qulafuci na dason ganinsa ne yasa nake ganin wannan yarinyar tanamin kama dashi”
Zama yayi dabar a qasa yace “tunda nake bantaba ganin abinda ya tsinkamin laka irin wannan halittar ba Inna a Ina Taheer ya samo wannan yarinyar?” Share kuncinta tayi tace “bansaba Aliyu nidai inajin tsoron wani Abu”
Girgiza kai yayi yace “karki kawo wannan a ranki babu haka a files din rayuwar Sahabi kawai dai kamace Kuma kinsan ita halittar ubangiji aya ce nasan shima Taheer bai taba kula ba Koda yake baisan baffansa sahabi ba sai awaya”
Miqa hannu yayi ya dauki yarinya dake ta baccinta ya zauna yana qare Mata kallo a hankali ya hadiyi yawu me ciwo ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur ya zubasu akan fuskar Taheer da suke shigowa da likita, yayi saurin kawar dakai daga kallon Dad yana cewa likitan “kazo ka dubata idan bazaku iyaba na fita da ita waje kawai”
Juyawa Dad yayi yana kallon sarautar Allah bai iya cewa dashi komai ba har saida likitan ya gama abinda zaiyi ya fita shima ya juya zai fita sannan yayi gyaran murya tare da kiran sunansa.
Tsayawa yayi ya juyo a sanyaye hawayen da yaketa kokawar tsayarwa suka zubo masa sosai yake tausayin mahaifinsa saboda yasan wannan abinda yayi kamar sanya fetur ne ya qasta ashana saman martabar Governor Waziri, yafitosa yayi yazo ya zauna yace “inayi maka murnar samun qaruwa da kayi Taheer Allah ya raya maka ya bamu ikon tarbiyantar da Safnah bisa sunnah”
Dagowa yayi idanunsa na digar hawaye yace “Dad…”daga masa hannu yayi yace “ya zamuyi dakai Taheer tunda mun haifeka hakamma na godewa Allah ni kuma dakai da Dan’uwanka ya jarrabeni Taheer Mahfuz kun zamemin jarabawa a rayuwata”