DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi’u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki  ta wannan number dake sama Idan VTU ne ta wannan layin Zaki tura dari biyunki ko dari 600 ki/ka 09013307566 idan fah kika tura a wancan layin na sama to ki qaddara sadaka kika bani shi evidence of payment kawai zaa tura

25 Sake matseta yayi a jikinsa yana sunsunar wuyanta ya dorata a gado ya zauna a gefenta yana shafa cikinta tare da kwantowa jikinta da haka har bacci ya dauketa shima ya kwanta.
Washegari da safe ko karyawa bai tsaya yayi ba ya nufi asibiti iyakar binkicensu sunce qalau yake babu wata matsala a tare dashi, hakanan ya dawo gda a kasalance wanna rana sunga ikon Allah shi naci dole sai yayi sex abu Kuma yace baisan zance ba.
Days gaji saiya kwanta kawai zuciyarsa nayi masa zafi tunda yake bai taba shiga tashin hankali irin na yau ba ita kuma sai rarrashinsa takeyi tana fada masa yayi hqr zai samu sauqi.

Wasa wasa abu sai qara gaba yakeyi itadai Habeey bata wani daga hankalinta ba tanayi masa addu’a kullum sannan taqi barinsa ya fadawa kowa tace suyi addu’a kawai, suna addu’a yana zagaya duk wani asibiti amma babu wani sauqi sai kamar qara gabama da abin yakeyi.
Lkc sai qara turawa yakeyi lamura suna qara tsamari tsakanin ma’auratan musamman Taheer da yabi ya tsangwami kansa ya hana kansa sukuni kullum cikin damuwa yake.
Mafi yawan lokuta zuwa zatayi ta tarar dashi a dakinsa ya hade kai da gwiwa yana kuka hakanan zata zauna tayita rarrashinsa idan yaqi yin shiru itama saita sanya masa kuka dole ganin tanayi shidin ya haqura yayi shiru.

Watanninsu takwas lkcn cikinta yanada watanni biyar, a ranar da ya gama abinda yakeyi yace ta fara package na kayanta jibi zasu tafi cikin murna tace “wlh dama duk na gaji My life” kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya fice.
Jikinta ne yayi sanyi ta dafe qirji a ranta tace “yanzu fah sai yayi tunanin da wata manufa nayi maganar nan ko?” Ilai kuwa yana dawowa taga idanunsa ya kada yayi jajir ya kalleta yace “kin gaji da zama dani saboda bani da amfani a gurinki ko Habeeytah?”
Idonta ne ya kawo ruwa ta matsa gabansa ta ruqo hannunsa yayi saurin janyewa tare da komawa jikin bango ya dora kansa a bangon yace “nasan ba kowacce mace takeda qarfin imanin zama da namijin da yake da matsala irin tawa ba”

Juyowa yayi suna fuskantar juna tana girgiza masa kai ya matso gabanta yace “hakanma kinyi qoqari Habeeytah ko iya haka kika barni kinyimin halacci ki fadi duk abinda kikeso kafin muje zanyi miki shi Koda kuwa Zaki zabi rabuwa danine….”
Dagowa tayi da sauri ta fada qirjinsa ta rushe da kuka tace “meye yasane Taheer me yasa kullum kake dangantani da abinda bantaba dangantaka dashi ba meye yasa kakemin kallon butulu Taheer meye yasa ka kasa gane matsayinka a gurina? Kullum nayi magana saika fassarata da wani abu daban, ta yaya Taheer tayaya zan zabi nesanta kaina dakai, aa ka dainamin haka don Allah kana saremin qwarin gwiwata ne please kada ka kuma inasonka a duk inda kake zan rayu dakai ko bakada wani abin amfanawa rayuwata….”

Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya dora bakinsa saman kuncinta yana lasar hawayenta nasa suna zubowa yace “inaji kamar Ina cutar dake Habeey inajin kamar Ina zalumtarki ne kunyata da soyayyarki gareni tasa kin kasa gane hakan wlh Habeey banajin ruhina zaici gaba da zaga gangar jikina matsawar baki tare dani”
Sake narkewa tayi a jikinsa tace “ni takace har abada My life” da wannan suka mantar da junansu damuwarsu suka shiga bathroom sukayi wanka sukazo suka shirya suka fita wani shopping mall sukaje duk wata siyayyarsu ta Safnah ce da babyn dake cikin Habeey itakam kallonsa kawai takeyi.
Koda suka gama suka juya gida sunata shagalinsu a parlourn yanata qissima mata irin dadin da zaiji idan yaga Safnansa, wayarsa ce tayi ring ya dauka yana murmushi ya kara a kunnensa yace “hello Dad…” Zabura yayi ya miqe yace “what innanillahi wa innah ilaihirraji’un yaushe?” Jifa yayi da wayar ya zube a gurin jikinsa na rawa.

Nufoshi tayi da sauri ta zauna a gabansa da rawar murya tace “waye ya mut…” Dago kananun idanunsa yayi da suka canza launi yace “Mom ce tayi accident ta hadu da matsalar spinal cord”
Dafe kanta tayi tana fadin “innanillahi wa innah ilaihirraji’un garin yaya” share hawayensa yayi yace “bansani ba nima” Shiru ce ta ratsa babu abinda kakeji sai shassheqar kukan Habeey kawai akeji dagota yayi yace “meye kikeyiwa kuka?” Cikin kuka tace “ina tuna halin da mutum yake kasancewa idan ya rasa gabar da zatayi motsi a jikinsa”
Kwantar da ita yayi yana murmushi yace “karki damu kowanne bawa baya wucce qaddararsa gobe zamu tafi Dad yace akwai jirgin da zai tashi da kayansa gobe sai mu bisa” jinjina kai tayi suka tashi suka shiga daki suka kwanta kowa da abinda yake saqawa a ransa har bacci ya daukesu.

Tashin asuba jirginsu yayi suka lula 9ja abbanta ne yazo ya taresu tsoro ya kamashi ganin yanda yar tasa ta rame sosai shima Taheer din duk ya zabge sai dogon hanci.
Bai iya tambayarsu ba har sukaje gdan gwomnatin yana riqe da hannunta suka fara ratsa parlourn gabanta sai faduwa yakeyi da Bushirah sukayi kicibis da tsohon cikinta tana ganinta ta saki wani ihu ta rungume Habeey tana cewa.
“Allah dai ya biya yayana sunqi Allah yaso kace mun kusa cika Fam da yara” kunya ce tasa Habeey yin qasa shikuma yayi yaqe yace “ya jikin Mom din?” Tabe baki tayi tace “au Wai dama saboda matarnan ka dauko baiwar Allah ka wahalar mana da baby? Hmmmm tana ciki tana girbar abinda ta shuka”
Kallonta sukayi da rashin fahimta ta nuna masa dakin tace ka shiga ka ganta tana ciki ke kuma zona rakaki bangaren yar’uwarki kiga mugun abinda son zuciyar uwarta yaja Mata Habeey ki godewa Allah dakansa yake baki kariya”

UMMUH HAIRAN

[8/12, 5:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: 26 Bin bayan Bushirah tayi gabanta na faduwa suka shiga bangaren Saudat din tana kwance saman kujera lullube da wani mayafi suka qarasa, a razane Habeey take kallonta tace “Subhanallahi meye haka” tsugunnawa tayi wani wari da qarni ya daki hancinta zuciyarta ta hautsina ta toshe hancinta da sauri tana duban jikin Saudat da da yake cike da wasu munanan manyan quraje sai zubar da mugunya sukeyi ta zabura ta miqe tace “Innanillahi wa innah ilaihirraji’un meye haka Bushirah meye ya sameta haka me yasa baa kaita asibiti ba?”
Numfashi Bushirah ta sauke cikin kuka tace “Anyi maganin har an gaji watanni takwas kenan take fama da wannan ciwon satinku daya da tafiya su Mom da Aunty Zahrah da Hajja Ummah suka tafi wani qauye a Zuru kwanansu uku sannan suka dawo cikin dare Aunty Zahrah ta tashi ta dora ruwa a saman gas ta dauki barjajjiyar maiwa ta zuba a ciki ta kawo wani ruwan asiri ta zuba taje ta bawa shanu suka shanye ta koma ta kwanta, tsakiyar talatainin dare gefin asuba Saudat ta tashi ta rinqa ihu jikinta yana qaiqayi ana haskawa akaga wasu manyan quraje ne suka feso a jikinta”

Rungume Habeey Bushirah tayi tace “da gari ya waye lbr yajewa Aunty Zahrah ta rinqa ihu tana kururuwa wai ta manta ashe cewa akayi ta kiraki ta tabbatar da darene a U.S.A sannan tayi ita Kuma ta manta tayi amfani da darenmu na 9ja Habeey ke akaso a dorawa wannan mugun ciwon bakiji ba baki gani ba kawai saboda jahilci da zalumci bansan me kika tarewa bayin Allan nan ba”
Hawaye ne ya rinqa sintiri a fuskarta ta sunkuya ta riqe hannun Saudat ta bude idonta a hankali tana kallonta itama wasu hawaye na zuba a idonta ta buda bakinta da yake cike da quraje tace “kin…kinga yanda Allah yayi dani ko Aunty Habbatullah Aunty ta jamin saboda Allah ba azzalumin sarki bane gashi Mahfuz yace bazai iya zama dani Ina wari ba harma ya qara aure sun tsallake sun barni shida matarsa sun tafi yawon cin amarci….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button