DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Kuka sosai Habeey takeyi na tausayin yar uwartata da bataji ba bata ganiba laifin uwarta ya shafeta, Saudat ta qara bude bakinta da yake buga wani uban wari tace “ashe dama Mom da Aunty sune suka mantar da ruhin Abba dake da tunaninki tsayin shekaru saboda kawai basason ki bayyana a matsayin yar Abbanmu ya kwanta ya mutu kici gadon”
Miqewa Habeey tayi tace “Allah ya baki lfy Saudat bari naje naga jikin Mom” fita sukayi zuciyar Habeey a karye sukaci karo da Taheer ya finciki hannunta a fusace yace “muje kawai basai kinje ba”
Taso tambayarsa ba’asi amma yanda taji yana huci yasata jan bakinta tayi shiru suka fita ya kira drive yazo yajasu zuwa gdansu da Addah tasa aka gyara musu suna tafe tana kwance a jikinsa yana share hawaye zuciyarsa na quna ya gama tsinkewa da lamarin Mom dinsa Mom tayi nisa ashe duk wahalar da yakesha da kudin da yake kashewa ita ta qullah komai itace ta lalata masa gabansa saboda kawai ta hanasa farin ciki da iyalinsa shikam me yayi mata haka me Habeey tayi mata da suke burin nakasta ta?.

Bashi da amsar tambayoyinsa saboda haka suna shiga ya zube a parlourn yana wuci jikinsa da bakinsa na wani turirin zafi saboda ran maza ya baci, itakam lura da yanayinsa yasata haurawa sama ta shiga tayi wanka ta canja kayanta zuwa wasu marasa nauyi cikinta ya fito sosai da yake bana fari bane ta sauko qasan ta zauna a kusa dashi ta shafo kansa tace “kayi hqr don Allah koma menene kaji” kwantowa yayi a jikinta ya fashe da kuka yace “ashe Mom tasan komai itace ummul aba’isin faruwar komai da yake faruwa damu sune suka dora miki wannan faduwar gaban data qararmin dake ta hanamu kwanciyar hankali, ashe sune suka kwantarmin da gabana ya daina aiki Habeey ashe ciwon da aka cemin Saudat tana fama dashi tsayin watanni ke akaso a dorawa shi Allah ya dawo musu da mugun nufinsu ashe a nufinta na ta sake dora miki ciwon da kika tashi dashine taje sukayi hatsari Munafukar yayar tasu Ummah ta mutu Mom ta samu wannan matsalar ita Kuma aunty Zahrah ta karairaye”

Sake shigar da ita yayi jikinsa yace wlh Mom ta cucemu hatta zargin da nakeyi miki ashe duk sa sa hannunta nayi danasanin sanin Mom dama ba ita ta haifem…”
Rufe masa baki tayi tace “aa kar ka fadi haka don Allah komai yayi farko fa yanada qarshe yamazo qarshen insha Allahu abinda akayi a baya bazaayishi gababa”
Lumshe idonsa yayi ya shafa cikinta yace “zan samu sauqi insha Allahu zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi amma dai yanzu zaki barni na fadawa su Abba matsalarmu ko?” Rufe idonta tayi tace “nidai kunya nakeji gsky…” Bakinsa ya dora saman nata tace “nikam banajin kunyar neman lfy so nake da kin haihu na qara dura miki wani babyn” harararsa tayi shima ya harareta sukayi dariya ya miqe yace “kina wanka Addah ta aiko mana da abinci muci ki huta sai jibi zakije ku gaisa da su”
Abincin ya dauko ya ajiye musu a gabansu tuwon shinkafa ne miyar agusi ta dago ta kalleshi tayi murmushi tace “Allah sarki Addah na ashe tana riqe da abinda nace mata inaso” qasa yayi da idonsa yanajin dama mahaifiyarsa ce haka.

Sunci abincin sosai sunata zuba santi sauran yace ta ajiye ta dumama masa ya fice saboda ya matsu yaga Abba su zauna ya zayyane masa matsalarsa sannan ga shauqin son ganin Safnansa.
Yana shiga gdan ita ya gani tanata wasanta a saman lilo a harabar gdan ya qarasa inda take ta dago ta kallesa ita a zatonta Mahfuz ne ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yanata juyawa da ita yana cillata yana cafewa.
A haka Abba ya fito ya tarar dasu ya tsaya yanata kallonsa yanda ya ke wasa da yar tasa soyayyarsa da yarinyar dabance dama ashe gaskene irin wadannan yaran shiga raine garesu, duba da yanda shima yakejin yarinyar a cikin ransa.

Matsawa yayi suka gaisa yace “ta riqeka ko sarkin surutu ba baki sai gwaranci” murmushi yayi yace “ai bakin ya kusa idan tayi qani zata ware ne” shiga sukayi ciki sun jima suna tattaunawa sosai yasha fada yake cewa “akanme zakuyi Shiru da matsala banda shirmenku”
Qasa yayi da kansa yace “wlh Abba My life ce ta hanani fada wai kunya takeji” haushi ya cika Abba yace “shine kuma kai dake juyin mace ne ka biye mata ko?” Wayarsa ya dauka yace dare yayi yanzu amma gobe ka fito da wuri sai muje Billire gurin Mal Zaa dace insha Allahu” da wannan suka fita ko Addah basu gaisaba tana sama tanata girki.
Da yarsa ya tafi Habeey ta gama aikinta ta haye sama ta kwanta ta rinqa jiyo hayaniyarsa a parlour bata fito ba har ya gama abinda zaiyi ya hauro saman ya taddata a kwance ta miqe da sauri tana murmushi tace “Safnah ta” karbarta tayi da sauri ta rungumeta tace “inata kewarki ke bakiyi tamu ba ko?” Daga Kai yarinyar tayi suka kalli juna sukayi dariya yace “dama ai abinda akaso kenan kada ki shaqu damu to kinzo kenan yarinya”

Sosai suka shagala da yiwa yarsu wasa sai dare yayi mata wanka suka kwanta bacci.
Washegari da asuba ya tashi yayi wanka ya fice itama tayi sallah suka koma suka kwanta goma ta gama komai sukayi wanka suka karya tanason zuwa ta gano jikin Mom amma data kirashi wayarsa busy dole ta hqr ta zauna da yarta wajen qarfe tara na dare ya shigo baije inda take ba Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya canza kaya yayi duk abinda Mal Kakan Habeey ya bashi tun a Billire ya farajin sauyi a jikinsa ya shiga dakin Habeey suna kwance itada Safnah ya janye Safnan a hankali ya kwantar da ita a gefe ya shige jikin matarsa yanajin wani yanayi daya dade baiji a jikinsa ba,
Yanda taji yana shafeta dinne yasata saurin bude idonta ta saukeshi akansa ya daga mata gira tana binsa da kallo shi Kuma yana lasheta tuni ya mantar da ita komai suka lula duniyar da suka dade basu shigaba ranar sun gurzu sun qwaquli juna kamar ba gobe ta dandana Habeey saboda ta dade bataji mazan ba.
Qarfe biyu daidai wayarsa ta buga ya dauka ya kashe batare daya duba me kiranba, sake shigowar kiran ne yasashi dagata ya dauki wayar tare da janye jikinsa daga na Habeey ya kara a kunnensa Kubrah ce cikin kuka tace “ta mutu Yaya Mom ta mutu tana kiran sunan matarka kaqi barinta tazo su gana”

UMMUH HAIRAN

[8/14, 7:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: 27 Miqewa yayi a sanyaye yace “da gaske ta mutu? Innanillahi wa Innah ilaihirraji’un” itama tashi tayi tace “waye ya rasu Life?” Kamota yayi ya rungumeta ya fashe da kuka yace “mom Habeey Mom dinace ta rasu”
Kuka ta fashe dashi jikinta na rawa tace “ya Allah Allah ya jiqan Mom wayyoh Allah Taheer shikenan Mom ta tafi ta barmu” hakanan suka qarasa kwanan nan da asussuba suka dunguma suka tafi gidan government suna shiga suka tarar da gdan a cike da yan’uwa Kubrah ce ta kama hannunta suka shiga dakin da Mom take kwance.

Suna shiga ta matsa da sauri ta bude fuskar Mom ta fada jikinta ta fashe da kuka abubuwa da dama suka rinqa dawo mata tace “Allah ya jiqanki Mom Allah ya gafarta miki” shigowar su Dad ne yasa Taheer ya janyeta daga jikin Mom din suka dauketa suka sanyata a makara aka fito da ita suka fice da ita zuwa harabar gdan akayi mata sallah aka fice da ita gabadaya,
Haka suka yini a gidan suna karbar gaisuwa itadai sulalewa tayi ta tafi bangaren Saudat yau sai taga jikin da sauqi tana zaune ita da me kula da ita sai Abba da Addah sunata yimata sannu Adda na shafa mata magani.
Sannu tayi mata ta zauna sukaci gaba da kula da ita har bayan magrib da Taheer yasa aka kirata yace tazo su tafi, kallonsa tayi a mamakance tace “na dauka anan zamu kwana?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button