DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Sunfi awa biyar a kanta komai na jikinta saida aka cire Mata ya rage daga ita sai under siket hstta bra saida Abba ya balle Mata saboda kokawa sukeyi da numfashinta da yakeyin sama suna fincikoshi daqyar zuciyarta kuwa bugunta yayi qasa fiye da mizanin da ruhi zai iya rayuwa da harbawarta.
Daqyar da taimakon oxygen suka samu bugun zuciyarta ya rinqa dawowa a hankali cikin abinda bai wucce daqiqa talatin ba ya dawo yanda zata iya rayuwar qila wa qala dashi, amma anyi rashin sa’ar shigarta commar da zata iya shekara guda a cikinta saboda duka jijiyoyin da suke kai saqon tunani qwanyarta sun tafi hutun wuccin gadi idan aka matsa musu dawowa zasu iyayin bombing gabadaya.

Wannan dalili ya tashi hankalin kowa dake cikin asibitin musamman Saudat da taketa kuka tana tsinewa son zuciyarta da yakaisu wannan matakin qiri² saboda rashin tausayinta da son kanta gashi ta jazawa yar uwarta tilo daya tal a duniya fadawa halin rai kwakwai mutu kwakwai wannan abu zai dade yana taba zuciyarta.
Shima bangaren Taheer yana cikin tsaka me wuya Amma shi da dan dama dama akan Habeey shi karo na farkone daya samu heart attack akwai yuwuwar nashi ya lafa da sauri.
Granny bata samu labarin abinda ke faruwa ba sai dare aikuwa a daren tace sai ankaita taga jikokinta, lkcn da tazo Bushirah tana kuka take fada Mata halin da Habeey take ciki ta rinqa salati tana matsar hawaye tace.

“Ni dama tun ganina na farko da yarinyar nan nasa akwai wani boyayyen al’amari game da haduwarta da Taheer Allah shi kadai yasan abinda ya boye tsakaninsu yanzu gashi gaskiya ta bayyana Kuma dole dan baqin ciki yaji kunya wlh Koda Taheer bai saki wannan ja’irar yarinyar ba sai ubansa ya saketa kuma a daren nan ko Habiba zata mutu saita mutu matsayin matar Taheer a wannan daren zaa daura”
Hakan kuwa itace ta faru a wannan dare Granny ta gwada ikonta Hajiya tanacan gaho da baki aka daura auren Taheer da Habeey wannan abu yayiwa kowa dadi duk da daga angon har amaryar basusan abinda ake ciki ba.

Sai sha daya na dare Dad ya koma gda shida su Kubrah da Saudat ta take dauriya saboda wani mugun zazzabi daya rufeta, suna zuwa gda ta shige dakinsu taja bargo ta rufe jikinta tana rera kukanta a zahirin gaskiya ba kukan rashin Taheer takeyi ba saboda a yanzu tanajin so da qaunar Habeey fiye da kanta.
A haka Aunty Zahrah mahaifiyarta tazo ta sameta a kwance cikin halin jinya ta dagota ta bude idonta da suka kumbura saboda kuka tana ganin mahaifiyarta ta fada jikinta ta rungumeta ta sake qarawa kukanta sauti tace “nayi baqin cikin zamowata silar shiga tsakanin yar uwata da bani da tamkarta a duniya da masoyinta haqiqa gsky ne layu’alimul gaibu illallah wlh da ace nasan Habeeytah yar uwatace da banyi sakacin da soyayyar mijinta ta huda zuciyata ta shigaba yanzu gashi gsky ta bayyana nice a qasa”

Tana fadin haka ta sake fadawa jikin Aunty Zahrah tace “shikenan Taheer ya tabbata ba nawaba dama yasha fadamin shi na Habeeytah ne gara nabarshi tun kafin lkc ya sanya nabarshi ta qarfi yanzu gashi ta qarfin zan barshi aunty naga samu naga rashi ya sakeni saki uku minti uku da daura aurens dashi ya turomin text massage a baya na qudurce bazan fadawa kowa ba amma yanzu dole lkc yasa na fada harma an maye masa gurbina da yar uwata Habbatullah….”
Jijjigata Aunty Zahrah tayi tace “keni kin cikani da shirme wace Habbatullah?” Bushirah dake shigowa tayi murmushin jin dadi tace “uwar wannan yarinyar” ta nuna Safnah dake kwance a kafadarta tana baccinta taci gaba da cewa “dama qarya fure take bata yaya rabon gsky ta bayyana mu qara dangi ne yar uwarmu ta dawo garemu yasa har hakan ta faru ni na tabbata Koda ace auren nan ya dade to bazaa zauna lfy ba saboda zuciyarsa tana gurin uwar yarsa” ta juya ta kalli Mom tace “kema yau kaifin harshena bazai tsallakeki ba Mom an dade anayi Ina sanya ido to yau dai gsky ta bayyana Habeey da kike qi har kike shirka saboda ki rabata da danki itama jininki ce dake da Abba Sahabi abokan wasane da babansa da babaki uwa daya uba daya yanzu kije a zuqe jinin Abba Sahabi daga jikinki kinga shikenan kin huta mudai munason yar’uwarmu sannan aure Allah baiyi hadin naki ba nasa ya qullah Yaya Taheer ya angwance da amaryarsa Habibatullah dan baqin ciki saidai ya mutu Safnah zata tashi cikin gatanta ta zama yar gata haihuwar dangi duk wanda ya zagi uwarta kansa ya zaga ka zagi ubanta ka gingimo dutsin dala dabara ta rage take Mom nidai shawara na baki kiyi maza kije a zuqe miki digon jinin Dad da Abba Sahabi a cikin jininki”…………….

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
    UMMUH HAIRAN

Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account 0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment dinki ta number dake sama.

10

Dafe qirji Mom tayi tace “Nashiga uku ni Safinah Bushirah me kike cewa ne wlh qwanyata ta tafi hutu bana gane komai” tabe baki Bushirah tayi ta dauki Pampers din baby Safnah ta fice tana cewa “kanku dai akeji aure Allah yayi alqawarin Habibah ce matar Yaya Taheer sai ku hadiyi zuciya ku mutu ku huta”
Binta sukayi da kallo har ta fice kalma daya ta kasa fitowa daga bakinsu Mom ta zube a gurin dabar tare da Dora hannunta aka ta zunduma ihun days firgita kowa suka sake yowa dakin da sauri, zare idanu takeyi tana kallon kowa ta cafki hannun Kubrah tace “me…meye yake faruwa Kubrah don Allah fadamin me ake Shirin yimin ne”

Dariya tabawa Kubrah tace “mom kema da abin haushi kike to meyene kuma alqawarin Allah ne ya cika Taheer mijin Habbatullah kinqi Allah yaso ya qulla abinsa yabarki da kunya amma Mom ai kina da wani dan ki hadashi da wannan yarinyar mana, dama ai gadon ari sai fanna”
Miqewa Aunty Zahrah tayi tana sharar hawaye tace “ashe dama wulaqancin da kuka shirya yimin da yayanki kenan Yaya Safinah kuka matsa saida muka baro England mukazo 9ja, tur wlh kin bani kunya ashe isar taki ta banzace baki isa da danki da mijinki ba Yaya kinbani kunya nayi nadamar zama qanwarki tunda kin kasa cikawa tilon yata burinta data rayu dashi tun quruciya har kawo girma”

Fincikar Hannun Saudat tayi tace “duk Dan daya hana uwarsa bacci to yasa a ransa shima bazaiyi ba zan dauki mataki farin ciki dai Taheer bazaiyishi bs kamar yanda ya hanamin yata ta warwasa”
Riqeta Mom tayi tace “kada muyi haka dake Zahrah ki muje dakina mubi komai a sannu fadan ya canza salo halan ke baki fahimci ma abinda suke cewa ba, to bari nayi miki bayani wannan karuwar yarinyar da nake fada miki Lele ya mutu akansa ta tsaface zuciyarsa ba kowa bace face yar Hajar matar Alh Sahabi ma’ana babbar yarsa da muka kashe maqudan kudade dan batar da babinta cikin rayuwar zuri’ar Maje Bauchi”

Wani mugun tsoro ne ya kama Zahrah ta zame qasa cikin tashin hankali tace “nashiga ukuna Yaya ai ban fahimci abinda yake faruwa ba dama ashe bata mutu ba Mal yacemin zai batar da ita a duniya zata lalace sannan daga baya a yawon barikinta ta dauko abin kunya ta jajubo cutar qanjamau ta mutu ashe duk qarya yayimin”
Rufe mata baki tayi lkcn da Dad yake shigowa ya bisu da kallo Mom tayi saurin miqewa tace “dama yanzu nake shirin kiranka Dad kaji abinda yaron nan yayi mana minti uku da daura aurensa da yar’uwarsa Saudat ya rattaba mata saki uku?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button