DUBAI PART 2

DUBAI PART 2

Kallon inda Saudat take nade yayi yace “haka Allah ya tsara muma godewa Allah da abin ya tsaya iyanan da baiyi hakan ba da abin ya rikice mana ashe yarinyar nan Habbatullah yayar Saudat ce ubansu daya kinga kuwa ai da anyi abin kunya duk da kasancewar aure ya halatta tsakanin Saudat da Taheer tunda a baya ba auren Habbatullah yayi ba Amma ai ana barin halak ko don kunya musamman da yake Taheer ba Saudat yakeso ba Habbatullah yakeso”
Girgiza kai Mom tayi tace “Lallai kam da anyi abin kunya to Allah yasa hakan shi yafi alkhairi yanzu Ina suke ance kun dora auren ko?”

Jinjina kai yayi yace “Granny dinsu ta tursasa aka daura auren tace Koda dayansu zai mutu saidai su mutu matsayin ma’aurata” wani mashi ne ya sake sukar maqoshin Mom amma sai tace “hakanma yayi yanzu ina suke?” Cikin jin dadin yarda Mom ta Basu hadinkai governor Waziri yace “a halin da ake ciki ita Habbatullah jin cewa Taheer ya zama mijin qanwarta yasata yanke jiki ta fadi qanwar matacciya a fadar likitoci sunce zata iya daukar watanni goma a wannan halin na doguwar suma shikuwa Lale ya samu heart attack yanzu haka yana samun kulawa daga likitocin asibitin Sahabi dake gombe amma akwai yuwuwar zaa tafi dasu England acan zasufi samun kulawa”

Cikin tashin hankali Mom tace “taheer din yanzu Kuma mutuwa zaiyi don Allah Dad ayi duk abinda ya dace” miqewa yayi yace “insha Allahu zasu tashi suyi rayuwa me tsayi sai sun Haifa mana halattatun jikoki, Ina Safnah yau banganta ba”
Tabe baki tayi tace “tana gurin iyayenta” sai yanzu ya tuna da yayan nasa mata duka matsayin matan wasu suke, yace “Subhanallahi meye ya hanasu tafiya gidajen mazajensu bayan an gama komai”
Itadai bata bashi amsa ba ya juya ya fice yayi niyyar tasosu yakai kowacce gdan mijinta Amma sai yaga har shabiyu na dare kuma Basu gama bidi’arsu ba.

Kallon Mom Zahrah tayi tace “shikenan burinsu ya cika na yata ya wargatse haka kike nufi Yaya?” Dafata tayi tace “har yanzu akwai quruciya a jikinki Zahrah idan rawa ta canza dole kida canzawa yakeyi kuma Shirin zaune yafi na tsaye a yanzu nuna qiyayyarmu ga yarinyar nan baqin jini zaija mana musamman ke, sakin ranmu zamuyi mu nuna komai ya wucce in yaso sai mu koma gefe mu sake shiri, ai wlh tunda na rantse banasonta bazan taba sonta ba sufa maza basu da tunani saboda haka mu bisu da yanda sukeso sai muci galaba akansu”

Haka suka rinqa tattaunawa har Hajiya Ummah yayarsu saida suka taso suka fada mata abinda yake faruwa, tayi dariya tace “kuma tanan suka bullo? Hmmm ku bar yan iska zamu iya dasu badai a kwance take ba to kuwa a haka zata qare rayuwarta saidai suyita asarar kudinsu a banza amma bazata tashi ba”
Dubanta Zahrah tayi tace “amma Yaya Ummah sai naga kamar yayi tsauri jinya tanada cin zuciya da jiki mudai nemi wata mafitar wannan batayi ba” harararta Mom tayi tace “bantaba yin tsafi ba sai akan shegiyar yarinyar nan nifa wlh yanda nakejin tsanarta da zata mutu ma da zanfi kowa farin ciki, Yaya Ummah shi Kuma wannan gardamammen yaron ya zamuyi dashi?”

Shiru tayi tana tunani sannan ta dago tace “kada ki damu dashi a barshi ya samu lfy ya warke qalau ita kuma a qara dora Mata jinya kuma ki tubure kice saidai a bashi ita yaje yayi jinyar matarsa ta hakane kawai zai fara nadamar bijire miki saboda zaiso kusanci da iyalinsa babu dama zaiso shima yaga matarsa a cikin halin lfy daga haka zai fara tunanin mafita zai fara danasanin aurenta zaiji tsanarta zai fara tunanin qara aure to daganan ne zamuyi amfani da wannan damar mu sanyashi sakinta sai mu maye masa gurbi da Saudat kinga shikenan ciki lfy baka lfy idan ta warke saita dauki jaka ta koma bariki lkcn komai ya kankama tsakaninshi da Saudat qila ma ta haihu kinga aure ya haramta tsakaninsu indai ba mutuwa Saudat tayi ba”

Wani ihu Mom tayi tace “shiyasa nake sonki kanki naja Yaya Allah yabar mana ke” murmushi Zahrah tayi itadai har yanzu da sauran imani a ranta amma ya zatayi bata da wata hanyar ceton yarta saita amince da wannan gurguwar shawarar.
Miqewa tayi ta matsa ta taba jikin Saudat da tayi baccin wahala jikinta zum da zazzabi, gyara Mata bargo tayi ta kwanta a kusa da ita tana shafa kanta tana tausayawa tilon yar tata tasan zafin rashin masoyi tun akan Abba Sahabi lkcn daya gujewa aurenta yaje ya auri Hajar, tana tuna irin azabar data rinqaji a heart dinta tana tunz irin wahalar da gangar jikinta ta shiga a lkcn, hawaye ta share tace badan wata kusan tafi wata ba da bazan bari a cutar dake ba Habibah duk da kasancewar harda sanya hanuna a lalacewarki amma bayyanarki da abubuwan da suka faru sun sanyayamin jiki lkcn da Yaya Safinah ta shigemin gaba wajen bata rayuwarki sai ya kasance kuma da gudan jininta kuka lalace ita ta tsarawa boka tanaso kiyi cikin shege yanzu gashi ita zata goya yar da ta assasa zuwanta duniya tabbas akwai matsala gaba bamusan meye zai faru ba, Amma Kuma ni Yaya zanyi da tawa yar idan naqi basu hadin kai”………….……

UMMUH HAIRAN

[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: HABEEYTAH
DUBAI PART 2

FAUZIYYA TASI’U UMAR
    UMMUH HAIRAN

Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account 0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment dinki ta number dake sama.

11

Haka kwanaki suka rinqa turawa kwanan Taheer biyar a kwance ya fara samun sauqi tunda ya farfado habeeytah kawai yake kira wani lkcn har sai an hada masa da Allurar bacci sannan yake samun nutsuwa, cikin kwanakin zuciya da jikin Mom sunqi hutawa duk inda zasu shiga su fito sun sun shiga.
Itadai Zahrah burinta a sake mantar da zuciyar Abba Sahabi Habeey Amma abin ya faskara qarshe bokan nasu da suka bawa amanna ya sanar da ita indai ta cika matsawa zata bata gomanta daya bata gyaruba dole ta hqr sukabar lamarin tsakanin Habeey da Taheer.

Kudi ba qanqana ba Mom ta kashe akan lallai a cusawa Dad aqidar qin bijirewa mgnrta haka kuwa akayi cikin lkc qanqani take juya ragamar governor Waziri.
Kwanaki goma Taheer yayi ya samu sauqi sosai zuciyarsa wasai da kyakkyawan albishir din da Dad yayi masa na musanya masa Habeey a matsayin matarsa farin ciki a gurinsa kamar zai zauce, Saida ya gama murnarsa da kukan dadinsa sannan yace “yanzu Dad tana Ina koma kun gama bikinku ban sani ba ankaimin ita gdana?”
Shafa kansa Dad yayi yace “kayi har an samu matsala lkcn da Habeey taji labarin an daura aurenka da Saudat ta yanke jiki ta fadi har yanzu batasan waye yake kantaba tana tsakankanin mutuwa da rayuwa Taheer likitoci sun tabbatar mana cewa bazata farfado ba sainan da watanni goma….”

Katse Dad yayi da cewa “what Dad! Kuma shine kuka tsaya kuka zuba Mata ido saboda bakusan ciwonta ba so kuke ku kashemin mata haba Dad haba Dad yaushe zaku fara daukan Habeeytah a matsayin da kuke daukar sauran yayanku….”
Shigowar Abba ne yasashi yin shiru Abba ya dafa Taheer yace “kayi hqr Granny ce ta takura Saida aka daura aurenka da Habeey a halin tana cikin jinya, Taheer naso ace sai Habeey ta warke akayi bikinku kukayi farin ciki kamar kowacce amarya da ango”
Girgiza masa kai yayi yasa hannu ya share masa qwallarsa lkcn da tasa take saukowa yace “inason ganinta Abba ka rakani naganta don Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button