HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 16-20

   Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne.

   Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa, masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman.

   Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga jikin ta.

“Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta.” 

Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki

“Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri.”

“Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na.”

” Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki.”

” Taro? Ke kina ganin za’a cigaba da taron nan?”

” Toh me za’a yi Yaya?”

” Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza.” Sai ta sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud’e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai dinki ba’a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba’a za’a basu ba, da k’yar Aunty Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.

   Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.

   Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru.

Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin dagawa, da dai taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran tayi ta daga na Maman.

“Kina gidan uban wa wai?”

“Mama kinsan fa ina saloon.”

“Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni.”

“Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir daga nan…”

“Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo gida ba, sai kinga yadda zan miki” tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik’e da wayar cike da mamakin Maman.

“Me ya faru kuma?” Ta Tambayi kanta cike da mamaki.

  Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata yarda ayi auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan.

” Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba.”

” Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da nake ciki.” Ta fad’a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa Allah. Jugum sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su, Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri.

” Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai.”

“Waye? Wai Mama menene ya faru?”

” Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?”

” Eh Mama, dan baki ganshi ba.”

Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace

” Toh dan ubanki dan sarki ne.”

” Sarki!!!” Zeenat ta fad’a da karfi tana zaro ido

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_1aHALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

1/21/22, 12:57 – Buhainat: Halin Girma

    17

Hafsat Rano

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****************

“Sarki!” Ta zaro ido cikin tsananin kaduwa

“Laifin ki me, duk laifin ki ne, da baki yi min karya ba, da baki boye min abinda kika gani ba, da nasan abinda ya kamata nayi tun a lokacin.”

“Haba Yaya Hajara, komai fa da kika gani ya faru toh dama chan haka yake a rubuce.”

” A ah Maimuna, wannan kam sakaci na ne, ni ce duk na jawo komai, gashi yanzu bansan yadda zan ba, komai ya kwabe min.”

” Hakuri kawai zamuyi mu tayasu da addu’a, kudi ba shine kwanciyar hankali ba,rufin asiri  shine, idan har Bashir din zai kula da ita ai shikenan, a hankali sai suyi kudin su.”

” A ah, ba zai yiwu ba, shegen yaron nan da har zai iya yaudarar mu, ya ha’ince mu ke kinsan ba mijin kwarai bane, dole Dr yazo a sake sabon zama, wallahi ba zan bawa yata mayaudari ba.”

” Toh wai yama akayi? Kika ganshi a fakiri sannan kuma ya koma dan sarki? Ta yaya hakan ta faru? Bayan babu wani abu da ya nuna hakan tun farkon zuwan sa?”

” Salamu alaikum.” Habib ya yi sallama kafin ya shigo dakin, su i su ne a ciki shiyasa ya shigo kai tsaye, ya gaida sisters din Mama sannan ya kalli Zeenat dake gefe tana matsar kwalla, yayi kwafa ya zauna akan kujerar gaban mudubi yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button