HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 16-20

   Shigowar su ya saka kowa na falon bin su da kallo, kai tsaye dakin Mama ta wuce Khadija na binta a babu yadda zatayi. Kusan zabura mama tayi ganin ta, ta tamke fuska tamau tana jin haushin shigo mata da tayi a halin da take ciki. Har kasa ta duk’a, ta gaida Maman sannan ta gaida su Aunty Maimuna. Duk sun amsa banda Maman da tayi kamar bata ji ba, tashi tayi bayan nan ba tare da wata magana ba ta wuce zuwa dakin su. Tayi mugun mamakin ganin Zeenat din, sai taji tausayin ta ya kama ta, ta durkusa a gabanta tana tuna lokacin da ta taimaka mata da bata jin dadi.

“Zeenat?” 

Ta kira sunan ta, sai a lokacin ta san sun shigo dakin ma. Da ido tabi Iman din kamar taga sabuwar halitta, 

“Iman?”

“Na’am, baki da lafiya ne? Kin ganki kuwa Zeenat?”

“Bani da lafiya Iman, bana jin dadin komai, wallahi bana son auren nan gashi an riga an daura, tsoro ma nake ji kar naje na aikata wani abu mara kyau.”

” Me ya faru? Me yasa bakya so?”

” Bashir karya yayi min, babu gaskiya a maganar sa, bashi da komai fakiri ne wallahi.”

Shiru Iman din tayi dan bata san me zata ce ba, tunanin yadda akayi hakan ta faru take, sai dai bata san yadda zata dauki maganar ta kuma ajiye ta ba. Kuka Zeenat din ta sake fashewa dah, kuka dacin da take jin sa a chunkushe a makoshin ta. Baki Iman din ta dinga bata, ta samu da k’yar tana maida numfashi. Tashi Iman din tayi ta duba wajen da ta ajiye jakar islamiyyar ta, ta dauka sannan ta sauki abubuwan da tasan zata bukata ba kaya ba. Khadija ta bawa ta tafi kai mata wajen Mamma sannan ta dawo ta cigaba da kwantar wa da Zeenat din hankali.

   Kamar ba Zeenat ba da take taka Iman din tayi mata duk wulakancin da ta ga dama, tayi laushi sosai,har tana dora kanta a kafar Iman din. 

   Wayar hannun ta ce tayi k’ara,  Moh ne yake kira, dagawa tayi tana tashi daga gaban Zeenat din 

“Amaryata.” 

“Umm.” Ta turo baki, dariya yayi sosai kafin yace

“Ki cigaba da turo bakin nan, babu ruwana aka samu matsala wallahi”

Murmushi ta samu kanta da yi, ta jujjuya kanta tace

“Kaiko?”

“Me nayi?”

“Ba komai.”

“Sharri kawai zaki min dan kin ganni bawan Allah.”

“Nima ai baiwar Allah ce.”

” Na yarda kuwa, are you ready?”

” Mefa?”

” Shigowa fadar Moh.”

” Ummm.”

” Get ready kinji? Yanzu zasu zo, kwana biyu zuwa uku zamuyi anan sai mu wuce adamawa.”

” Adamawa?” Tace tana zaro ido

” Calm down, zan miki bayanin komai.”

” Shikenan.” Tace a sanyaye

” That’s my wife, Allah yayi miki albarka.”

” Amin.” Ta amsa tana sakin murmushi a hankali.

Kashe kiran yayi, Zeenat ta bita da kallon sha’awa, tana hango tsantsar dacewar da Iman din tayi, gashi ita ta tashi a tutar babu.

“Zeenat bari na tafi, zamuyi waya in sha Allah, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki.”

Jumbur ta mike, ta rik’e jikin rigar ta tana goge kwallar da ta zubo mata

” Dan Allah Iman karki tafi ki barni, wallahi ba zan iya zama da Bashir ba.”

” Me yasa? Bakya son sa ne wai dama?”

” Wallahi bana son shi, ko kad’an wallahi laifin Mama ne.”

” Iman!” Taji muryar Mamma a kofar dakin tana kiran ta, juyawa tayi ta fita tana kallon Zeenat din cikin tausayawa

” Ke kuma daga zuwa daukar abu sai ki zauna? Kinga ai lokaci yayi ko?”.

Bata ce komai ba sai kawai tabi Mamman suka bar bangaren, ranta babu dadi ko kad’an.

   Wanka mamma ta sake sata tayi, kayan da zata chanja ta tarar a dakin, an turara mata su da turarurruka masu dadin kamshi. Tana shiryawa tana tunanin halin da Zeenat din take ciki, yadda ta firgice ta shiga tashin hankali zaka gane akwai wani abun a k’asa, ba wai kawai dan Bashir din bashi da hali bane kamar yadda ya Maryam ta bata labari.

   Duk shirin da tayi da taimakon su Harira, aka kuma kawo wata sabuwar alkyabbar aka dora mata, tayi kyau ainun, babu make-up babu komai amma yadda fuskar ta take sheki kadai zaka gane ba karamin gyara tasha ba.

  

   La’asar likis sai ga jama’ar gidan su Bashir, motoci goma ne gaba daya har data amarya , yadda za’a samu kowa ya je har mutanen unguwa, a lokacin babu irin kiran da be yiwa Zeenat din ba akan gasu nan amma bata dagawa, shiyasa kawai ya kyale ta domin shi a yanzu ba ta ita yake ba, yadda zasu kwashe da hajiyar ce kadai matsalar sa, labari ya riga ya kai mata ya kuma san gamon su bazai taba yin kyau ba, gashi akwai wasu kudade da ya ta bashi da nufin zai mata wani aiki ya bi ta kansu.

   Hankalin Mama ne ya kara tashi sanda suka iso, ta tabbatar da gaske Zeenat dai sai ta tare gidan Bashir, kiran Abba tayi, kafin ma ta fadi komai yace

“Ina falon Yaya idan kun gama ki turo min Zeenatun.”

Daga haka ya kashe kiran, cikin sanyin jiki Mama ta nufi dakin su Zeenat din, ta tarar da Aunty Maimuna na ta fama da ita akan ta tashi ta shirya, ganin shigowar Mama ta saka ta saurin tashi ta nufi wajen Maman.

“Jeki shirya Zeenat, kiyi sauri Mahaifin ku yana kiranki.”

“Mama?” 

“Ya zanyi? Ya zanyi? Aure an riga an daura ba kuma zan je na chakumi wuyan Bashir nace lallai sai ya sake ki ba, tunda kuma an daura ai dole ki tafi, dole ki bishi shine mijinki, ya zanyi.”

Fashewa tayi da kuka, tayi saurin fadawa toilet din ta rufo kofar, danne zuciyar ta sosai Mama tayi, ta juya ta bar Aunty Maimuna a dakin ta kuma jaddada mata kar su bata lokaci. Mamaki sosai Aunty Maimuna tayi da yadda Maman ta dake, amma kuma ta hango tsantsar tashin hankali a tattare da ita.

   Da k’yar ta taimaka mata ta fito ta shirya har lokacin kuka take, kaya kawai ta saka sai turare babu batun powder ko makeup. Lullube mata fuska Aunty Maimuna tayi suka fito, kai tsaye aka wuce da ita wajen Abba. Su uku ne a dakin daga shi sai Abba kabiru sai Abba (Babba) nasiha suka soma mata, me shiga ciki akan rayuwar da zata shiga sabuwa, yawanci magana daya ce hakuri wanda Zeenat din ta kasa fahimtar su, bata gane me suke cewa balle ta san a wanne mazauni zata ajiye maganganun nasu ba, har suka gama bata fuskanci komai ba, hankalin ta ma baki daya baya wajen su ta tafi tunanin kalar rayuwar da zata fara a gidan Bashir din. Sadakin ta Abba ya dauko a aljihun ta ya mik’a mata

“Gashi zeenatu,Allah ubangiji yayi miki albarka ya baku zaman lafiya.”

K’asa karba tayi, ta fashe da kukan da take ta rikewa, mikewa Abba yayi ya fice daga dakin zuciyar sa na tabuwa, yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya a lokaci da ya dinga nunawa Zeenat din illar abinda take shirin aikatawa.  

   Abba Kabiru ne ya karbi kudin a hannu Abba yace

“Barshi Yaya, bari wani cikin yaran nan sai yaje ya saka mata shi a account, idan yaso bayan komai ya lafa sai ta ciro tayi amfani da abinta.”

“Hakan ma yayi, shikenan zeenatu kudin ki za’a saka miki shi a account kinji? Ki daina kuka.”

Tashi tayi da k’yar tana gid’a kai kamar gadangaruwa ta fita, daga nan ne kuma kowa ya firfita dan zuwa kai ta gidan Ango Bashir. Sai dai duk mutane suka gama shiga mota sannan aka fito da ita aka sakata a mota, tana kuka Mama na yi haka aka tura ta a motar. Dangin Bashir din sukayi ta mamakin abinda yake faruwa dan kowa ya ga kukan yasan ba kawai na rabuwa bane akwai wani abu daban.

    Shiru kake ji a motar babu motsin kowa kamar ba ma mutane a ciki. Wata Yayar su Abba ce da Aunty Maimuna suka sakata a tsakiya, hannun ta na damke ana Aunty Maimuna tana cigaba da kukan ta a ciki ciki. Har suka karaso bata daina kukan ba. Sauran jama’ar motar ne suka fiffito, kowa tayi cirko cirko suna jiran a nuna musu gidan Zeenat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button