HALIN GIRMA 16-20

  Sun dan jima a shashen Fulanin mutane daban daban manya wanda suka zo bikin suka dinga zuwa suna ganin Iman din, kunya kamar ta nutse ta dinga boye kanta wanda hakan ya saka suka kara son ta kowa ya dinga yabon ta yana yaba sa’ar da Moh din yayi.
  Rakasu bangaren Moh din Fulani ta saka akayi, wanda dama chan aka ware wa Iman din da wanda zasu tayata zama kafin gobe yan uwan ta su dawo shagalin da za’a yi a babban Hall din gidan da tun a ranar an gama tsara shi an kawata shi.
  Two bed room ne sai falo da kitchen, tuni masu kula da shashen sun gyara komai, daya daga cikin dakunan aka kaita, sannan su Mamma sukayi mata sallama aka bar mata Amaani, khadija, Zahra sai su Amira, duk dai yan matan aka bari a zuwan su Mamma sai su dawo gobe. Kamar zatayi kuka haka taji da zasu tafi amma kasancewar ta me dakiya ta daure kawai tayi shiru tana cigaba da kallon komai tamkar almara.
  A falon su Amira suka zauna bayan sun raka su Maman sun dawo suka dasa kallo da hirar gidan Iman din da irin yadda aka karbe su a masarautar. Tana jin su sama sama bata fito ba sai ma tayi kwanciyar ta saman gadon dakin tana shakar kamshin da ta tabbatar da kamshin sa ne dan shine kamshin da ko da yaushe take jin sa yana yi.
  Tana kwance taji kamar motsi, ta daga kai ta duba, sai taga kofa a jikin karshen bangon dakin wanda sai ka lura sosai zaga gane don ta saje da kalar curtains din dakin. Budewa taga kofar tayi, ta mike daga kwanciyar da tayi da sauri kafin ta gama daidatuwa har ya shigo, cikin shigar bakin dogon wando da riga armless, cikin mamaki take kallon sa har ya shigo cikin dakin gaba daya. Mikewa tayi tsaye lokacin da ya karaso daidai in da take. Ya saka hannu ya shafi gefen fuskar ta.
“Wai tsoro kika ji?”
Da ka ta amsa, ya rik’e ta ya zauna a gefen gadon sannan ya zaunar da ita a daidai kusa dashi, k’asa kallon sa tayi, ya zuba mata ido yana kallon ta kamar a ranar ya soma ganin ta. Farin cikin da yake ciki a yau din mara misaltuwa ne, ba zai iya tafiya adamawa be sake ganin ta ba shiyasa kawai ya hakura da zuwan sai da safe.
  D’agowa tayi da nufin ta ga abinda yake, tayi saurin sake maida kanta k’asa ganin yadda idanun sa sukayi k’asa sosai. Hannun ta ya kamo ya rik’e a cikin nasa yana murzawa, yana kokarin danne abinda zuciya da gangar jikin sa ke wassafa masa. Yadda yake murza hannun nata da yadda suka samu kusanci sosai ya saka ta a yanayin da bata taba samun kanta ba, shi din ma hakan ce, dan yadda yake ji yayi imani idan aka dauki lokaci me tsawo baa bashi matar sa ba toh komai zai iya faruwa. Lissafin ta yaji sunayi ya saka shi jin gaskiya ba zai iya bari har tsawon kwanakin da su Ammi da nan Kano kowa ya diba na shagalin da zasuyi ba. Kwana daya ya isa anan ko biyu chan kuma daya idan yaga zasu ki yarda zuwa zai ya samu Aunty Fatima ya karanta mata komai a taimaki dan maraya a bashi matar sa ko kuma yayi musu aika-aika.
  Turo kofar akayi, su dukka suka kalli kofar, da sauri Khadija ta juya tana fadin
“Dan Allah kuyi hakuri.”
Tashi yayi tsam bayan ta fitan, ya sakawa kofar key ya dawo ya mikar da ita, ya cire mata alkyabbar da take jikin ta har lokacin, saurin runtse idon ta tayi saboda yadda dinkin fitted gown din jikin ta ya kamata sosai dan sai da suka kusan haurawa sama da Mamma kafin ta yarda ta sakaa. A abuja aka mata duk dinkunan nata kuma kaf babu wani dinkin arziki a duk kayan da Maman ta bayar akayi mata tace idan tazo kayan lefen ta sai ayi mata wasu na fita amma ita nata duk na zaman gida ne ayi wa Moh kwalliya. Dogon numfashi yaja, a karo na farko ya ganta haka babu hijabi balle mayafi. Kayan su zauna das a jikinta,ta wajen hips din sun zauna kamar a jikinta aka dinka su. Idon sa ya shiga rarraawa daga tsakanin kirjinta zuwa kasan hips din ta, yabi flat tommy dinta da kallo wanda zaka rantse ba’a saka masa abinci saboda shafewar sa.
“Masha ALLAH!”
Ya samu kansa da furtawa, kunyar da take ji kamar ta haka rami ta shige gashi ya hanata sakat ya rik’e ta babu damar ta zauna. Sai da ya more kallon ta tsaf sannan ya dawo samar fuskar ta ya matso daf da ita har tana jin hucin numfashin sa a saman fuskar ta, tayi saurin runtse idon ta ya kura wa lips dinta ido, ya kai bakin sa daidai kan nata ya shiga kissing dinta passionately ba tare da ya shirya ba.
  Jikinta ne ya hau rawa tayi kokarin hanashi amma sai ya sake matso da fuskar ta sosai, ya tallafo ta ta baya ya sakata a jikin sa ssosai ya cigaba da aikin sa. Ta saman bayanta taji yana neman abu, har ya kai wajen da zip din ta yake, ya shiga jan shi zuwa k’asa, da sauri ta rik’e hannayen nasa tana girgiza masa kai hawaye har ya fara sauka a idon ta.
“Pleaseeeeee.” Ya furta cikin muryar da taji kamar ba tasa ba, ta shige ciki sosai.
“Dan Allah kayi hakuri.” Tace tana sake rik’e hannun nasa, dan taga kamar ma baya gane me take cewa.
  Wayar sa dake cikin aljihun wandon sa ce tayi kara, ya janye ta yana murmushi ya ciro wayar yana daidaita kansa.
“Zan kira ka Bashir.”
Kawai yace yana kashe kiran. Lokacin ta koma ta zauna tana kokarin daidaita kanta dan ba karamin yanayi ta shiga ba.
  A gabanta yayi kamar kneel down, ya tallafo fuskar sa yana mata kallon tsantsar kauna, turo baki tayi ta harare shi ya tuntsure da dariya
“Pretender kawai.”
Ya saka hannu ya lakaci gefen hancin ta, murnushin ita ma tayi ta juyar da kanta daga kallon sa abinda ya faru yana cigaba da haskawa a idon ta.
“Kaje anan kiran ka.”
Tace ganin yaki tashi ya kuma hanata sakat da kallon sa da idon sa da suke sake bata tsoro a game dashi.
“Kora ta kike? Wallahi sai naki tafiya na kwana anan din dama ai daki na ne.”
” Ya hakuri ni dai dan Allah.”
” Matsoraciya, kin fiye tsoro wallahi.”
” Tsoro ai halak ne.” Tace tana dariya
“Inyee kinyi baki haka? Yarinya zaki maimaita maganar nan ne, for now zan barki amma gaskiya zan dawo, kice ma su Amaani su kwana dayan dakin ke kadai zaki kwana anan, kinga dama akwai secret door dita kawai sai na shigo mu sha soyayyar mu.”
” Tab!”
” I’m serious
 Â
 Â
#Rano💕
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
[ad_2]