HALIN GIRMA 16-20

“Kiyi hakuri Mama dan Allah, amma ni da kaina na fad’a miki Bashir ba mutumin kirki bane, yanzu dai hakuri kawai za’a yi tunda lokaci ya riga ya kure, dan Allah karki yiwa Abba wata magana kinsan dai ba zai saurara ba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kiyi musu addu’a arziki ai na Allah ne. ”
Wani kallon banza Mama tayi masa, kafin ta nuna masa kofa
” Fice ka bani waje bana bukatar maganar ka. ”
Mikewa yayi, yana jin babu dadi abinda Maman take yi, tun daga irin rikon da tayi wa Iman din wanda sun sha haurawa sama a kai idan yayi mata magana, daga baya sai ya daina kawai ya watsar amma kuma ya kan yawan yiwa abokin sa sadeeq maganar ta akan zai bashi Iman din saboda yadda yaga zaman da take yana so yaga ta samu yanci, akwai ranar ma da hira ta saka ya kwashe komai ya sanar wa sadeeq din duk da yasan kamar tonawa mahaifiyar sa asiri yayi amma kuma ya zai? Baya jin dadi sam.
 Kofar ya ja musu ya bar gidan ma gaba daya dan ba zai zauna ya cigaba da kallon bacin rai ba. A waje suka hadu da Abba ya aike shi karbo wasu kaya sai kawai ya biya ya dauki sadeeq suka wuce tare.
 Â
***Har dare Abba be shigo ba, idon Mama kamas tana jiran sa, Zeenat ma idon ta biyu sun shirya samun Abban ita da Maman ayi magana dan da gaske take ba zata kuma auri Bashir ba yanzu, musamman bayan taga kayan da aka ce wai nata ne, toh wai mana, dan bata saka rai ko hasashen irin su ba ko kad’an.
  Kamar Abban yasan za’a yi haka yaki shigowa da wuri har sai da suka soma kosawa, gaba daya duniya bata musu dadi sam, Bashir sai kiranta yake amma sam taki dagawa dan bata da lokacin sa balle ta wayar sa.
  Wajen sha biyu Abba ya shigo bayan ya gama kallon kayan iman din a bangaren Gaji duk da be iya kallon komai ba sama-sama shima don sun matsa masa ne, Gaji ce ta kirashi daki tace ko me Maman zatayi kar ya yarda ya biye mata, ayi a gama komai lafiya shine kawai.
  Yana shigowa ya gansu a falon Zeenat na rakube a k’asan kujera tana cigaba da matsar kwalla, yi yayi kamar be gansu ba, yayi hanyar dakin sa Mama tayi saurin tare shi
“Dr.”
“Kinga dai a yadda na shigo kinsan akwai gajiya, ki bar duk wata magana zuwa gobe da safe idan ALLAH ya kaimu.”
“Ba zai yiwu ba, idan na bari aka kai gobe na samu matsala, yanzu zamuyi ta mu san abinda muke ciki.”
Kada kansa yayi ya dawo ya zauna sannan yace
“Ina jinki.”
“So nake a fasa auren Zeenatu, ba zata auri Bashir ba.”
Wani banzan kallo Abban yayi mata, kafin ya hade rai sosai yace
“Ashe ma ke mahaukaciya ce ban sani ba Hajara, Ashe baki da tawakkali ma, ashe ma baki san komai game da rayuww ba, bari kiji.”
Ya juyo yana kallon ta
“Dama shi sharri dan aike ne da kike ganin sa, duk in da yaje sai ya dawo, dan haka Wallahi, Wallahi kinji ma rantse ko?”
” Ba zan karya alkawari na ba, ba kuma zan zama mutumin banza ba, sai dana jaddada muku ke da ita gata nan, nace kunji kun gani? Sai yanzu da ya rage yan awowi shine zaku zo min da maganar banza? Saboda bansan me nake ba ko?”
” Idan kana kaunar Allah Dr ka rufa min asiri a fasa auren nan dan Allah!”
” Lallai Hajara kin haukace, wallahi babu abinda zai hana auren nan sai dai idan cikin mu biyu babu wani, ko ni na mutu ko ita Zeenat din ta mutu, amma in dai da ranmu da lafiyar mu wallahi sai an yi, kinji ma na gaya miki.”
” Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi zan iya mutuwa.”
” Allah ya jikan ki.”
Ya tashi yayi shigewar sa daki ya saka key kar ma ta samu damar biyo shi dan a yadda ya hangi tashin hankali a idon ta, zata iya jure su kwana a tsaye akan maganar da babu komawa baya.
Wani irin marayan Kuka Zeenat ta fashe dashi, bata san ba son Bashir take ba, kwadayin abun sa da kuma kishin Iman ya sakata ganin kamar son nashi take, sai yau ta gane kawai bakin cikin da take wa Iman ne ya sakata amince dashi.
 A zaune suka kwana, babu kalar tunanin da Mama batayi ba akan washegarin, har da tunani ko ta dauki Zeenat ta gudu da ita? Kafin gari ya gama haske tuni hayaniyar gidan ta cika ko’ina wanda ta tabbatar da gangan suke yi don a kular da ita.
  Da k’yar taayi sallah ta saka Zeenat ma tayi lokacin yan uwa har sun tashi sun fara gyara shashen Maman.
  Dakin Abba Mama ta shiga, ta same shi ya fiddo sabbin kayan sa da zai saka ya ajiye a saman gado, yana waya da Maman Iman, duk da ta shigo amma be daina wayar tasa ba, ya cigaba da yi mata bayani
“Masu zuwa daurin auren su taho da ita, kinga anan dinma za’a so a ganta, in yaso daga nan sai a wuce kawia da ita.”
“Owk shikenan.”
Ta amsa sannan ta kashe wayar. Haushi ya sake turnuke mama amma ta share dan ba abinda ya dameta bane a yanzu, matsalar da take ciki yanzu tafi wannan.
“Ina kwana?” Ta durkusa a k’asa ta gaishe shi,
“Lafiya lou.” Ya amsa a gajarce yana cigaba da duba sakwannin wayar sa.
“Dan Allah Dr kayi hakuri, hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, kar ka hukunta yar ka akan laifin da ni na aikata, naji duk hukuncin da zaka yi min kayi min amma dan Allah a fasa auren nan.”
” Kinsan Allah?” Yace yana ajiyewar wayar hannun sa
” Ba zan fasa auren nan ba, iyayen yaron nan sun zo na karbi maganar su nayi komai har sun kawo lefe sai yau ranar kawai kice a fasa? Nace musu me kenan? Tun farko ban fad’a muku ba? Ban nuna muku illaar abinda kuka nace akai ba, kuka nuna min ku ba zaku fasa ba, har kika saka zeenatu ta watsa min k’asa a ido ina mahaifin ta, ko da ace Bashir yaron kwarai ne idan nace ta hakura dashi ba zaki taimaka wajen ganin ta yi min biyayya ba? Amma me kikayi? Sannan sai yanzu, sannan zaki zo min da maganar banza, ya kike so nayi?”
” Dan Allah nidai kayi hakuri ka yafe mana,dan Allah ka taimaka.”
” Wallahi Hajara babu abinda zan iya akai, kinji ma na rantse, ki barni dan Allah.”
Zama tayi dabas a k’asa, sai kuma ta tashi da sauri ta fice ta nufi shashen Gaji, ta same su a falon yan uwa ana ta shewa, ta wuce su zuwa ciki kamar wadda ta zare. A k’asa ta tsuguna ta gaida Gaji wanda rabon da tayi haka an dade.
” Dan Allah ki taimaka ki saka baki Dr ya fasa auren nan, wallahi idan akayi auren komai zai iya faruwa, nasan ke kadai yake jin magana dan Allah.”
” Yana ina?”
” Yana gida, dan Allah ki taimaka min.”
” Kije kice idan ya gama ina neman sa, Allah ya kyauta ya rufa asiri, sai a hakura kawai.”
Tashi tayi da sauri, ta manta ko godiya bata yi ba, ta fice kowa ya bita da kallon mamaki cike da jin haushi. Ko da ta fadawa Abban be ce mata komai ba, da ya fito ya shiga wajen Gajin bata yi masa maganar ba, ya gaisa da kowa sannan yayi breakfast da masa ya wuce wajen yan uwan sa.
 Â
***Daren ranar Moh be runtsa ba, duk wasu bakin da zasu iso sun gama isowa a lokacin kowa an sama masa masauki na alfarma. Abokan sa da sukayi karatu tare suke kuma aiki tare sai dai kowa wajen da take daban ne suka sauka a cikin gidan a bangaren Moh din, kafin a daura auren su wuce adamawa sannan su sake dawowa Kanon saboda events din da za’a yi a Kanon.
  Raba dare sukayi ana hira, anan suke fad’a masa suma fa sun shirya masa kayataccen bikin sword crossing amma a abuja saboda suna so manyan su na wajen aiki su ma su zama sun samu halarta. Abubuwan sun so suyi ma Moh yawa saboda shi dai tsakanin sa da Allah zai fi so ace da an daura auren kawai su yi tafiyar su shi da ita,amma kowa kokari yake ya shirya wani abu da zai sake rik’e su, shi dai kawai dan kar ya fito fili yace baya so ne, amma har ga Allah da kowa ya hakura.