KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Basu tsaya ko ina ba sai Airport yayi mata komai tazo Abuja lfy tana fitowa ta hango driver na Na'im yana jiranta,saida Suka gaisa yayi mata sannu da zuwa ta bishi sai gida,tun a mota driver yace Na'im bashi da lfy yana kwance,Salma a fara kuka tana a kara gudun motar tayi maza ta ganshi, fara bata hakuri yayi tare da cewa zazzabi ne kawai,ko kulashi bata yi ba.

Mota na parking a gidan ta fito da sauri Allah yasa ba kowa a Palo kawai ta wuce Bedroom dinsa da sauri ko knocking babu kawai ta fada ciki an samu dai tayi Sallama,tana shiga ta hangoshi saman Bed yana kwance amma zazzabin ya sauka,da sauri ta karasa tare da daura hannunta saman wuyansa taji ko yaji sauki,taji ba zazzabi ajiyar zuciya ta saki,tace Alhmdllh ta juya tare da niyyar tafiya idonsa a lumshe yake kawai taji an rike hannunta ta juyo da sauri cike da masifa yace ina kinka(kika tafi) tafiya haka har 2wks?kinsa gabana yana ta fadowa(faduwa) ina kika shiga? Kamar zai mareta haka yayi maganar.

Baki ta turo tare da kwace hannunta tace gida naje mana ka sani,karya ne kakeyi,if gidane kinka je baza su yarda dake ba har ki zauna 2wks,just tell me,Raheel nefa tace,sai lokacin ya tuna da shi ma,tafiya Bedroom nata tayi tare da yin wanka ta shirya cikin English wear riga da skert tayi kyau matuka marasa nauyi,kitchen taje da kanta tana tambayar masu abincin me suka dafa suka fada mata duk bata son su,Indomie da dankalin turawa ta dafa ta koma saman Dining ta zauna tana cin abarta dama Salma akwai cin abinci tana cikin ci sai ga Mummy da Irfan sun fito,me tafiya ta dawo ko nemanmu ba a ayi?cewar Mummy,  Da murmushi ta juyo da cewa laaaa ai na zata bacci kikeyi,uhm rufe min baki amma nasan dole kin nemo Na'im ko cewar Mummy,Irfan yace wlh tana shigowa bedroom dinsa ta wuce da gudu ina kallonta,Salma tace ai dan bashi da lfy ne zaka sa min Ido,sanmin indomie din taki naga zatayi dadi,Fork ta mika masa ya zauna tace sai dai muci tare bazan iya barma ka cinye du ba,Mummy ta wuce kitchen abinta,Irfan dai ya zauna ya fara sharbar indomie Salma ma tana ci,Na'im ne ya sakko daga side nasa cikin shirin fita yasha kyau,hango Salma da Irfan suna cin abinci shi ya bata masa rai gaba daya yaji haushin abin ai gwara taci tare da shi Na'im dan me sai Irfan,sabo da takaici ko sauraronsu baiyi ba ya fita abinsa, har yaje zai shiga motarsa yana tunanin yanda ya bar Salma da Irfan,fuuuu sai gashi ya dawo tare da banko kofar kamar zai tashi sama,dakinta ya wuce kamar nasa ya dakko mata mayafi kalar kayanta yana zuwa ya yafa mata a kanta da ba dankwali ya ja hannunta tana fisgewa amma ya figeta tare da jefata a mota ya shiga ya figi motar da gudun tsiya suka bar gidan.

Irfan shi abin ma dariya ya bashi amma fa yana son Salma ya fara sonta,Mummy tana kallonsu tace kwaji dashi dai taja bakinta ta tsuke, Aisha ce ta dawo gidan a chake tasha tayi tatil tana layi da tangadi ta shigo tare da jefar da handbag dinta sannan ta fada saman Sofa bacci ya kwashe,lips dinta ya kumbura sumtum kamar anyi mata duka a wajen,ga kuraje kanana sun feso a kansa,Mummy da mamaki tare da tsoro taje ta shinshina bakinta taji kamar warin giya ta tabbata tasha wani abu amma bari Na'im yazo ya duba mata yau ita kadai tasan me zata yiwa Aisha a gidan.

   Na'im bai tsaya ko ina ba sai wani hadadden garden na hutawa,Salma ba tsoro take ji ba domin ta saba da zuwa waje waje,fitowa tayi tare da shakar Fresh air dake kadawa a wajen,wow wajen yayi kyau,sai yanzu ta kula da shigar Na'im 3qrt da T-shirt yayi kyau,jikin wata gada suka karasa kasa titin mota ne sama garden,Daukan Salma yayi cak tare da zaunar da ita saman ginin gadar iska na kadasu me dadi yana kasa a tsaye hannunsa ya daura saman kusa da wajen da take zaune tare da tallafe kumatunsa yana kare mata kallo,cike da nishadi,sai shilla kafafunta takeyi tana murmushi tare da dauke kanta gefe  kunyarsa takeji.

  Cike da shagwabar da ta saba tace sai kallona kakeyi lfy?bai kulata ba sai dan gyalenta daya gyara mata sabo da iska ta kusa cireshi,suna haka sai ga wata hadaddiyar budurwa tasha kyau da wanka tana zuwa tace Oh Na'im kaine a nan yau,juyowa yayi sukayiwa juna murmushi Ajja ya kake(Hajiya ya kike) yace,tace missed u Badly ina so nazo ma ziyara na kasa samun time amma zan daure,
Kafin yayi Magana Salma tace sakkoni na gaji,Daukota yayi tare da direta a kasa,harara ta gallawa wannan wacce ya kira Hajiya,Hajiya tace kaji min yarinya dan ubanki ni kike harara haka?kin San koni wace?wannan Kanwar taka bata da kunya,Salma ta murguda mata baki tare da yin fari da Ido shi ko Na'im ya shagala da kallon murguda bakin da Salma takeyi Bai ma san me Hajiyan ke yi ba,Salma ta kara rike kugu tare da murgudashi tana yi mata kallon up and down,Hajiya tace sai na mari wannan yarinya fitsararriya,sai lokacin Na'im yaji maganar Hajiya,hannu ta miko masa tana zan wuce ni sai munyi waya ko shima ya miko mata hannu zasu gaisa ta wuce Salma ta rigata gaisawar da Na'im ta rike hannun tana jinjinawa yanda maza sukeyi kuma tana kallonsa tana murmushi tace muje kawai,kamar wani rakumi haka ya bi Salma sukayi tafiyarsu aka bar Hajiya da miko hannu,hannunta ta janye tare da cewa kan uban can kai,yarinyar nan batasan wace ni ba amma zanyi maganinta,shi kuma  wai ya bita ya wulakantani to wai ma wace wannan?zan bincika.

 Abun zaman da aka tanada a wajen suka zauna cikin daya aka kawo musu lemuka da chicken's shawarma  Masoya mata da miji sai love suke Sha a wajen ana soyewa,Salma taga wasu Arna mace da namiji sun rungume juna tace Yeee ai Allah Raheel yana yi min irin wannan,can wani ya zauna ta kwanta saman cinyarsa,aaaaaa....wannan ma indai yazo sai na kwanta a cinyarsa cewar Salma,kai kaga wancan ma tab ai duk muna yin irinsu,ta nuna wani yana hurawa wata chika Ido tace an wuce wajen tun ina 5yrs yake min wancan,lemonta ta zuka tare da kallon Na'im tace kai a duniya ana dadewa fa mantawa akeyi,ai ko ni naga yau naga jiya na gobe nake jira kawai,Na'im yace kin San sunanki?tace sai ka fada yace dan Iska indai ko kana da gaskiya duk wannan kina yi tare da Raheel to Ku duka dan iska ne( sunan Salma yar iska itama wai indai duk wannan da ta fada sunayi ita da Raheel to su yan iska ne)

Dariya Salma ta dingayi tace to ai Bana Jin komai ni.tabe baki yayi gaba daya yaji kishin Raheel dole ma yayiwa Salma maganin Raheel,Raheel ne ya fito ya zauna gefen Salma itace kadai take ganinsa komai har kayan iri daya dana Na’im sai taga Raheel guda biyu gefenta Na’im dayan Raheel,Na’im yace gobe zaki fara sallah kullum tare zamuyi,kafin ya gama magana Raheel yace karki yi karyane,Kawai sai ta kalli gefen Na’im ta kalli na Raheel ma kowanne da abinda yake fada mata,Na’im yana zancen Sallah da maganin da zai fara mata yaje wajen wani me maganin Aljanu,Raheel yana hanata karta yarda indai ta yarda sai ya bata wahala zai kasheta ne gaba daya ko ta haukace kuma sai ya dauketa daga gidan su Na’im ya batar da ita,yana gama fada ya bace bata. Na’im dagashi Sai Salma yake gani a zaune,Salma ta fara kuka tana yankani zasuyi,zan haukace.
Na’im yace wlh kome za ayi sai dai ayi amma magani ba fashi nama fasa sai gobe a yau za a fara da dare dole ta rama sallolin yau.

Gida suka dawo ya samu Mummy na jiransa ya duba Aisha,Salma ta gudu dakinta ta buya harda sa key,yana duba Aisha yace giya tasha me karfi tayi mata karfi tana da Allergic da ita shi yasa ta kumbura mata lips magunguna ya bata ya wuce ya bar Mummy da bacin rai,
Yana komawa daki yaje ya shirya tare da daura Alwala yaje yasa spear key ya bude dakin Salma tana saman Bed,ta Mike firgit zata gudu ya damkota zata makaleshi ya matsa can zata iya karya masa Alwala,jawota yayi yace a dakinki zakiyi Sallah,har toilet ya kaita tana kuka da komai tayi Alwala dole,ta fito ya shimfida mata sallaya,ta fara Sallah idan tana karatun rai rai sai bakinta ya harde yaki buduwa bare tayi karatun Sallar,yace wlh sai tayi haka ko baza tace komai ba,haka da kyar akayi isha,magrib,da sauran na rana guda,tana gamawa ya dauko ganyen magariya ya zuba a ruwan ya tofa mata ayatul qursiyyu kafa bakwai,Amanar rasulu bakwai,falak,nas,Iklas,fatiha kafa bakwai ya bata tasha taki yayi yin duniya taki Sha,riketa yayi ta karfi tana tsaga ihu kamar ana yankata,Irfan ya shigo ya karbi maganin Hunaif ma yazo suka riketa ta karfi suka dura mata tana burbuwa aka matse mata baki saida ta hadiye tas sannan suka saketa ta dinga tsine musu a gidan ba wanda bata zaga ba.

Ranar kwana tayi tana Aljanu, da safe da wuri Na'im ya kara zuwa ya mata turare da Habbatussauda sai lokacin ta daina,ya lasa mata wata a baki,tayi shuru ta nutsu tana zaune ta rakube a gefe daya,Qur'ani ya mika mata yace ta karanta aiko ta karba da kyar tana karantawa ta danyi da yawa ya karba ya tafi,yinin ranar kaf bata kara lekowa ko main Palo ba,abinci ko an kai mata baza ta karba ba,ta wani manne a jikin bango kamar Almajira kowa ya shigo tsoronsa takeyi kana bude kofar zata firgita jikinta ya kama karkarwa,tun safe Na'im bai dawo dakin ba, ko wanka bata yi ba taki cin abinci kuma tana Jin yunwa amma Mummy ta kawo mata baza ta karba ba,Irfan ya dinga lallabata sai dai ma ta saka kuka haka suka gaji suka kyaleta idan Na'im ya dawo ya gwada nasa basirar ko zata yarda.

  5pm ya shigo gidan saida yayi wanka ya shirya yaci abinci sannan Aisha ta fada masa Salma bata ci komai ba,abincin ya Eba ya tafi room nata,tana ganinsa ta kalleshi tayi murmushi yana mika mata ta karba taci ta koshi ya karo mata ta cinye tasha ruwa sannan ya nuna mata toilet taje wanka,kafin ta fito ya zabo mata kayan sawa Riga T-shirt fara me hoton mace da gashi,dogon wando ya Ciro mata pencil me kyau dark blue,pant da bra ma du ya Ciro mata,da gudu ta bude toilet ta fito daga ita Sai towel a guje kamar wani ne ya korota tana fitowa ko wankan ma bata fara ba tacewa Na,'im mutuwa zanyi  yau wlh bleeding nakeyi ka gani ina zuwa toilet naganshi zuuu,kafafunta ya kalla jini ke sintiri, period kika fara ba kin taba fada mini ba baki Period shine yanzu ko kina mantuwane? Sai lokacin ta tuna tace to kaje ka siyo pad mana ka tsaya kana kallo na,Ke kinfa rainani ni danki nake ne da zaki bani command haka?to zauna karka siyo wlh ba ruwana haka zan zauna kuma nasa kayana,murmushi yayi wa kika yiwa to? Kanka mana tace, a jikina yake knocking da akayi shi ya katsesu yaji muryar Irfan da sauri ya tura ta toilet ya bude masa kofa,Irfan ya makawa Na'im harara yace wannan jininfa a kasa dis dis? ka takurawa yarinya ka jawo sai tsoronmu takeji.

Na’im Bai saurareshi ba ya fita me aikinsa wacce ke gyara masa part ya aika ta siyo masa ta dawo,yana shiga ya kwankwasa mata door din toilet yace hannu kawai zaki miko,ta bude ta karba ta kulle ya bar mata room din.

 Washe gari har yamma bata leko ba tana Bedroom abinta,Na'im  tambayar Mummy yayi Salma bata fito ba?tace ae yanzu ma rufe ido takeyi idan ta ganmu,murmushi yayi ya shiga room din samunta yayi tana kuka ta kalli sama ta daga hannu tana addua tana kuka Allah ka yaye min wannan period,wannan jini ya isheni Allah ka yaye min har Abada,tana jin ya kara zubowa ta kara barkewa da kuka tana Allah ka yaye min na daina yi har abada.
Na'im yana jikin kofa ya harde hannaye a kirji yana ta dariya marar Sauti sai da ya gaji addua taki ci taki cinyewa,Yace a abin arziki bakiyi addua ba sai a wannan,kin San ma ba karba Allah zaiyi ba,ku da akayi muku gata kuna kara lfy,yana cire muku cutuka shine kike Butulu (butulci)
 Harararsa tayi sannan taci gaba da adduarta sai dariya yake,saman bed nata ya kwanta yana jin addua Allah yaye mata jinin Haila yana ta dariya duk kalma daya in ta fada sai yayi dariyar wannan shirme.

Da dare ma da ta shiga wanka taga ma karuwa yake kawai ta dinga kuka har ta fito idonta jajir kuma wai kyankyamin kanta takeyi bata iya cin abinci da kanta Sai dai Aisha ko Na’im ko Irfan idan Allah ya kawo wani ya bata taci,Mummy ma tana bata a baki sai taci,yau ma Mummy ke bata saman Dining tace sorry kinji zaki daina ne idan kika saba su Na’im duk suna wajen dama Salma Ido ya kumbura yayi jajir tacewa Mummy ni bazan saba ba Allah,Aisha tace aiki ya samu mata to ya kike so ayi miki in bakyayi ma ai da kyar in zaki haihu,Salma tace ni ina ruwana da yara Bana sonsu indai akan haka ne,Na’im yace kyaleta Aisha taje ta mutu idan tanawa Allah butulci Irfan Ya kara da kuma batayi aure ba ta mutu tab,Salma hawaye ya gangaro mata tace ai yan matan gidan Aljanna zan zama kamar zata narke haka take magana,Mummy tace kyalesu kinji ci abincinki.

 Ummitu kuwa tunda ta gama yiwa Salma masifa ta juyo tare da jawo ledar tsire taga wayam ba komai ta fara salati da sallallami Affa yana shigowa tace kagani ko da kudi ne da tuni ma shigowarta Aljanunta sun sace ta talauta mu,gwara da ta tsaya a naman oh kaga jarabar yarinya azzalima,ta zalincemu Affa sabo da bacin ran da Salma ta kunsa masa ko magana kasa yi yayi.
Ummitu tace je ka duba kudin da ka ajiye a kasan gadona,Affa yace af bari na duba me farar kafa yau ta shigo gidan,Shi kuma kudin an samu matsala tun jiya da Affa ya ajiye bera ya dauka namane yaji kamshin nama a jiki kawai ya janye kudin ya kai can dai dai Raminsa na kasan gadon Bai ci komai ba suna nan lfy amma suna bakin ramin bera,Affa da Ummitu neman duniya ba a ga kudi Dubu uku ba nan suka dinga salati Affa yace kin gani ko Allah ya Isar min tsakanina da wannan yarinya ubanta ya jona mana masifa,dan wannan masifa ce, nan suka dinga zage zage. 

 Yau kwana Uku da fara period din Salma kullum bata da walwala daga kuka sai adduar Allah ya yaye mata,Na'im yace ta shirya suje gidan Dada yawo wai ko zata ji sanyi,tace to ka siyo min Pampers, baki ya bude me zakiyi da Pampers ai sai yara tace uhm to ai pad tayi min kadan sai a gida zan na sa pad tsoro nakeyi kaga kuwa idan Pampers ce shike nan na huta bazan baci ba,wa ya fada miki? da wasu zaki tafi a handbag naki ai sai ki dinga shiryawa a gidan da zamuje, ba musu ta shirya ta cakare kamar zata je party suka fita abinsu sun dace da juna sosai.

 Dada sai murnar ganinsu takeyi gaskiya gidan Dada ma me kyau ne sosai,Salma tunda suka gaisa tayi shuru abinta ta zauna ta nutsu daga Na'im sai Dada suke hirarsu bata sa musu baki, abinci da lemuka iri iri me aiki ta kawo musu Sai da Salma taci tayi nak dama ita akwai ci,kawai ciye ciyenta takeyi bakinta Bai hutawa da tauna.har dare suna gidan saida yaje masallaci yayi sallar Isha yace tazo su tafi,da sauri ta Mike dama ta gaji Dada ta bata turare da Sabulan wanka masu kyau da kamshi,tayi godiya suka dauko hanyar gida,saida ya tsaya ya siya mata kilishi da yawa yaga tana sonsa,tun a mota kuwa ta fara bude ledar tana dan yagowa tana cinyewa,yana satar kallonta sai ji yayi tace a daina kallo na,murmushi yayi Bai ce mata komai ba Driving dinsa yake ta yi, tambayarta yayi kin kuwa canja pad?sabo naga Alama Raheel din naki Bai koya miki wannan ba,ba tare da ta kalleshi ba tace sabo da shi ba dan iska bane ai,
Maimakon Na'im yaji haushi ta zageshi shine dan iskan kenan sai ma murmushi da yayi na birgewa tare da tsuke lips yaja yaji shshiiiii ni kuwa dan iska ne sabo da ina son iskanci thts y my ina ta kula mata.harara Salma ta zuba masa tace to Allah ya shiryeka,da sauri yace Ameen tare dake,dariya tayi tace ka fara iya hausa da yawa yanzu,kansa ya nuna da yatsa yace akwai ganowa( ganewa) a class 1st nake daukowa ,amma ke da gani dakika ce (,dakikiyace) Salma tace tsabar kokarina ma yaro Living things ake ce min kaje garinmu ka tambaya,ko kace wace Salma Colaboration a kasar nan za a fada ma domin na shahara na fetsara,Dariya ta kwace masa sosai  a kasar wa yasanki a kasar nan in ba a kauyenku ba?,

Salma ta rike kugu a zaune tace Doctor Me Imani Na’im Alawwal,the Consilor of UK Embassy,and Also a prince, the most Handsome Arab man,he look alike with my one and Only Raheel my Heart,my soul mate.
Dariya Na’im ya kara yi sannan yace nima tsautsayi ne ya kamani ai,sai kuma wa ya sanki ba ni ba, irin su Governors,Ministers,Business men etc wanda kina fadan su a Nigeria an Sansu?ni ki daina sani ciki wa ya sanni a kasar nan? Masu kudi wanda suka yi fice nake nufi.
Salma ta sosa kai tace idan ba tsoro ba muje fadar shugaban kasa ka gani idan bamu gaisa dashi ba,Muje gidan minister of petrol a gani,karewarta wife din dan Gote kawata ce kamar yanda nake a gidanku haka nakeyi,ka tambayi Adam a zango karewar ta yan film ma sun sanni,Idan kana ji karyane aje gidan Ali Nuhu a gani mana,kai ka daina kallo na wata shuru shuru ba karamar shegiya ce ni a kasar nan ba,Salman Khan nan in kaga yanda muke wasa da dariya dashi sai kanka ya kulle,Amita batchan,su jitandara,kai kasan Sharukhan?to saida yace yana so na kar kaso kaga wulakancin dana masa, an fada ma ni ta wasa ce,bari ma na kaika wajen turawa kasan dai dan Wrestling undertaker ko? to mun dade tare tight frnd nane,Nancy ta Larabawa har yau har gobe kawata ce,Ronaldo da Messi sanda Ina Spain tare muke cin abinci,Governor na jigawa,kano,Taraba duk sun sanni.

Dariya Na’im yashata kamar cikinsa zaiyi ciwo matar da take wannan kurgumin dajin badan ma Aljaninta ba ai da baza tasan ma me akeyi a duniya ba,Na’im yace karya naki ya isheni haka pls, tace yo dama kana dan kauye me ka sani kai,kaifa dan kauye ne ni ban taba ganin kauyis irinka ba wai kamata ace na fika wayewa Allah kiyaye wlh anyi asarar kaika Uk,Salma yanda ta dage tana caccake Na’im kamar gaske,yace na dai fiki kyau ai,tace Allah sittiri bukwi inji kishiyar me doro,farinka ne kawai ya ceceka,hancinka yayi tsayi da yawa ya bataka,lips naka karami da yawa ba kyau yayi red ba wacce zata so ka,gashinka santsi zaisa a tsaneshi ma,Na’im yayi dariya ke fa na fiki manyan Ido wooo,idon naka kamar na mage abin tsoro da dare miyau miyau harda gwada kukan magen, hmm gashinki kamar dutse ba laushi,Salma ta taba na gaban goshinta tayi fari da Ido tace uhmmm laushin Bala’i wlh,kai nifa am sweet komai nawa sweet muahhh tayiwa kanta kiss,Na’im ya tintsire da dariya yace to kawo na taba da kaina naji,da sauri tace ai kana tabawa za aga bingir ka Sume sabo da laushin gashin ina bazai yuwu na karasa gawar da ba tawa ba.haka sukai tayi har suka je gida cike da nishadi.

 Yau gidan Malam musa me kawo musu maganin mata tazo da kwandonta guda,nan fa a kira matan gida ko wacce ta fito harda Maimuna ta ebo dan kudinta ta fito, Hafsatu me magani tace yau fa akwai sabon Harka ta dakko wani me karfe a jiki ta daga musu sama tace kun San wannan?sukace a'a tace to me mukulli kenan,idan kina so ki kulle mijinki ko kishiya yayi miki bakya so ya sadu da ita sai ki dauko shi kice Bissmillahi na kulle mijina wane sai ki saki karfen zaice das shike nan kin kulle mijinki bazai taba Jin sha'awar kishiyarki ko wata mace ba sai ranar da zai shigo dakinki ki kara dakkowa kice bismillahi na bude wane mijina to da yazo dakinki sha'awarki kadai zai ji,amma ko neman mata yake dan Ubansa kina sa masa mukulli kin gama da shege,mata sukace heeeeeee suka saya zasu gwada,can ta dakko wani tace wannan ki karanta Fatiha kafa bakwai ki jefa a tsohuwar Rijiya ba ke ba kishiya ke dai zai makalewa sai kin dinga korarsa,ga me kunama na matsi ne shima Oga ko kurnu ne dole yaji a jikinsa,ga dan kumasa a daga a hada da zuma ayi matsi ahaf ai sai ke ko kishiya ce kece a gaba,ga Sokoto timjim, daga jin sunan ma malama Basai kin mana bayani ba ai zamu Zama timjim cewar Maimuna,nan Malama ta miko hannu suka kashe ana shewa,ta kawo turaren kwanciya a shafa a cibi,kirji,da hips da ya shaki kamshin zai rude miki nan tayi ta karanta musu wasu maganin mata ne normal wasu kuma an hada da shirka a ciki,mata a kula yanzu garin neman maganin mata har abin ya koma shirka da bin malamai,ana rubutu jikin kwai,kaza,da sauran Abubuwa da gani kasan an koma bin malamai,ko ace kar ayi amfani dashi sai  za a sadu za ayi tsarki da ruwan rubutu ko alwala gasu nan iri iri ana kaucewa a fada fushin Allah,har kullum a dinga tunawa da mutuwa,baka San ranar tafiya lahira ba,ko yaushe zata iya zuwa,me zakace da Allah,haka kishiya mene abin kulla mata sharri ko wacce idan ta biya  allonta ta wanke ke dai ki zage kiga ya zaki kiyi zarra wajen mijinku ba ta hanyar bokaye ba ta abinda Allah yace,duniyar nawa take har za a dinga cutar da juna ana jifan juna,wannan ya jefi wannan wannan ya jefi wancan,waccen ma haka kowa wajen malamai ana shirka a juna,tsakanin musulmi da musulmi  maza mata Malamai ana kashe juna,ana kullawa juna Bala'i ya kamata wlh a kiyaye a gyara halaye, malaman nan masu bada maganin kusan yanzu duk bokayene suke fakewa suna shiga rigar malamai,ya shirya karya kamar gaske yana aji tsoron Allah idan magani yaci karki cutar dashi idan kika mallakeshi etc sai ki dauka na gaske ne baki San mashirki bane yana ta tsafi yana yiwa Allah shirka,ayi addua da kanmu mana ki tashi kiyi Zikhri wanda Allah yace,time din da ake amsa adduar bayi,Karatun Qur'an,Nafeela etc kiyi sujjada kuwa Allah kirari ki zubda hawaye kikai kukanki wajen Allah wanda kullum baya Hutu baya bacci,kullum Office din Allah a bude yake kiyi kullum ki gani idan Allah Bai saurareki ba ya amsa miki,ya baki ma abinda baki zata ba a duniya kuma nasa me dorewane,amma tsafi fa karyewa yake baya tasiri,ga fushin Allah.Allah bamu ikon gyarawa,amma da ki ba malam kudi ya miki aiki gwara kici kaza gashashiya ko ki gyara kanki da kudin gyaran jiki.

Kwana biyu Salma ta canja salon Aljanunta yawo take fita kullum ba tare da an sani ba sai dai aga bata nan,da yamma lis ta dawo ko dare,kuma idan ta fita sai ta koma mahaukaciya sosai tuburan take hauka a titi da bola,amma idan ta dawo gidan su Na'im sai a ganta fes,Na'im abin ya damesu gaba daya bashi da sukuni,tana fita yake fitowa da mota amma baya ganin inda ta shiga,Abuja kuma ba a barin mahaukata a titi,Na'im baya ganinta bare yace sai tayi Sallah ko ya mata maganin da Malam ya bashi,haka yauma ta fita ba dankwali a kanta tana ta tsince tsince a titi tana dariya ko ta bata rai,motar dake tsinto mahaukata tazo wucewa ta ganta a hanya aiko suka tsaya caraf suka kamata nan take suka buga mata Allura bacci ya tafi da ita suka jefa ta a mota sai asibitin Mahaukata na Abuja aka kai Salma suka sa mata Sarka kafafu da hannaye dasu take yawo,da ta tayar da Aljanu a maka mata Allurai,yanzu tana can cikin Uniform na mahaukata tana Shan Allurai,Na'im sati guda yaga bata dawo ba,har kauye yaje wajen su Affa ya tambaya saida Suka zageshi tas sannan suka ce bata nan,haka ma Borno yasha cin mutunci iri iri shi dai yace Jahilci ke damun su ko a jikinsa.

Cikin Abuja kullum a yawon nemanta yake lungu da sako,haka Irfan ma sai yanzu yasan ma Ashe son Salma ya kamashi da yawa Bai sani ba,
Mummy da Dada sai jimamin bacewar Salma suke sun damu kwarai,Aisha da Hunaif ma takanas suke daukan mota suyi ta zagayen nemanta layi layi amma ba alamar ta.

Yau Salma da Raheel suna tare a asibitin Mahaukata suna ta hirarsu amma Sam yanzu bata son Raheel tafi son tayi hira da Na'im,sai taji Raheel baya birgeta Sam,Raheel yace na fada miki dama indai kika yarda sukayi miki magani saina haukataki,kuma na daukeki daga gidan,yanzu nan ne gidan zamanki tunda ban gama cika burina a kanki ba sai kin kara ajiye min yara biyu sannan kika gama min aikina,Salma dai tayi banza dashi Na'im kadai take so ta gani a duniya.
Likitoci sunga Salma na magana ita kadai tana Hawaye ta fara shagwaba tana shure shure kawai suka ebo Allurai zasu danna mata Raheel yasa ta shaki daya da karfin Aljanu tayiwa likitoci dukan gaske,amma duk da haka saida securities suka riketa suka tsira mata Allurai har kala Uku ta zube a wajen sharaf sukayi ciki da ita aka kaita can wani daki tare da shinfidar da ita.

Kimanin wata daya kenan da bacewar Salma Mummy ta matsa Na'im dole sai yayi aure duk da cewa yanzu baya kawo mace ko daya gidan sabo da shi ta Salma yake,ya zaiyi ya nemo ta,Mummy ta sameshi har bedroom tace Na'im kasan dai ba wasa nake da kai ba ko? Mahaifiyata nima ita ta bani umarni dole kai da Irfan sai kunyi aure a watan nan,duk kun Rame tunda yarinyar nan ta bace baku da sukuni amma idan kunyi auren zaku ji sauki matarku zata ebe muku kewa.

Na’im ya kalleta nan take ya fara hawaye cike da shagwaba yace ina wani ebe kewa ni Bana son kowa me zata min naji dadi,kawai a daura Min da Salma idan a naso a ganni na samu jin dadi,Mummy tace baka da hankali yarinyar da ta bace bat kuma Aljanu gareta tana yawace yawace shine zaka ce wani zaka aureta,ae ni dai ina sonta haka zan mata magani wlh in dai ba ita ba sai dai ko Dada ta tsine mika Momma Danni ba ruwana.
Fuuu Mummy ta bar masa dakin ta koma wajen Irfan yana kwance yayi wanwar Son Salma ya addabeshi Mummy nan ma ta masa bayani budar bakinsa yace ai sai dai a mutu wlh Dadan me itace Mamanki ai ba tamu bace ni wlh in dai ba Salma ba to ba wani aure da zanyi a kan haka ma kuna takura min zan koma neman matana dama ta dalilinta na shiryu.
Mummy tace to kaima Salman ce kenan?yace yeah,to ai baka dace Da ita ba tunda fada kukeyi,Na’im yafi dacewa da ita Irfan to kuwa indai an bawa Na’im Salma nima sai dai na auro Balarabiya tsohuwar budurwata ta UK wacce kika ce bazan auri yar can ba,Kai kafi Na’im ma rashin kirki Irfan ta bashi dukan wasa a baya bakwajin magana Allah dai ya shirya min Ku addua ta kenan,Allah Zaba abinda yafi Alkhairi.

Haka ake son iyaye ba a dauki Zafi akan yaro ba ayi masa dole karshe abin yazo ya kwabe a samu matsala ana dana sani,wasu kuma a dinga zagin yaro ana masa baki akan ya fadi ra'ayinsa a'a dole abinda iyaye sukace ko na sabon Allah ne sai ace sai yayi,idan ba ayi ba su tsine ma ko su fara kuka Allah yayi fushi,yaron ya lalace karshe rayuwarsa taki albarka.iyaye a daina saurin zagi da tsinewa yaro ko zubarwa da yaro hawaye ayi hakuri a dinga dannewa.

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: ????KAMARSU CE DAYA????

          61-65 

By
AsmaBaffa

Zainab Atiku Salama Happy Birthday to u,Allah karo shekaru masu amfani,Na'eem ma da Salma sunce HBD.sun bada gift na perfume na saceshi???????? Sardauna da Ramlat   Night wears da kayan daukan wanka kala goma suka kawo a baki gift,Lantan shadda yar gaske,Dafta tare da Hajara sun kawo super Holand kala biyu da readymade ta kasa me tsarki suma du nayi sama da fadi dasu????



FLOWER,AUTA, ASYCOOL,MARCYCOOL,MAMAN SAMHA,MAMAN MEENAT wannan page naku ne.









  Wani Malamin Doctor ne ya gano lallai Salma Aljanu gareta kuma tana da hankalinta,sabo da haka kawai yayi magana da Doctors zai fara gwada mata na Musulunci sabo da asibitin sunayi idan an fuskanci Aljanu gareka.
 Sati daya Raheel ya tabbatar za a rabashi da Salma kawai sai ya juyar mata da memory lfy lau take da hankalinta amma bata iya tuna kowa bata gane kowa gaba daya ta manta abinda ya faru baya,Haka Na'im ya fita Office Embassy kawai Ya fito da niyar tafiya gida,Raheel yazo ba wanda ke iya ganinsa kawai yayi sama da Na'im bat suka bace,bai direshi ko ina ba sai can cikin wani kauye can kusa da Katsina state,Kamar anyi masa duka haka aka tsinceshi a gefen titi duk yaji rauni a jikinsa ko motsi baya yi,shima Raheel sabo da bakin ciki kar Salma ta auri Na'im ya raba musu gari sannan shima Na'im ya goge masa Memory na baya,bazai iya tuna kowa ba sai rayuwarsa ta yanzu.

 Kowa yaga Mutum kyakyawan gaske kamar Aljani wasu suce bature gashi kalar kudi komai nasa me tsada ba wanda ya daukeshi haka ya kusa yini yashe a gefen titi,sai da Allah ya kawo wani malami kuma maharbi wato Malam Magaji shine kadai yayi shahada a wannan kauyen ya dauki Na'im ya kaishi gidansa,gidane na na bulon siminti ko ina ba kasa a gidan me kyau,daki Uku ne a gidan sai na Malam dake zaure,Toilet biyu ta wanka ma daban,dayar kuma Masai din irin ta flowshing amma ta siminti,Malam Magaji dama yana da wadatarsa a kauyen yana noma me tarin yawa,ga mutunci da hankali sannan kuma yana zuwa daji farauta.

Har yaran kauyen yana koya musu karatun Allo da safe da yamma,gashi wayayye kamar ba dan kauye ba,haka matarsa Haleematu Dattijuwar kirki ce kwarai gata da bala’in tsafta kamar me komai a wanke a gyare a goge tsaf,gidanta kullum kamshin turaren wuta me dadin gaske,dakunan Bedroom sunsha Red carpet masu kyau da bed kanana dai madaidaita,dakin Malam ma haka,store dinsu da kitchen komai akwai na kauye dai dai me karamin karfi.
Koda ya shigo da Na’im kwance kamar gawa Haka Haleematu ta karbeshi hannu biyu biyu wani magani Malam Magaji ya shafawa Na’im a fuska sai ga Na’im yaja ajiyar zuciya ya Mike zaune yana salatin Annabi,sai kallon Haleematu da Malam Magaji yake faman yi,shi Bai iya tuna komai Bai gano shi waye ma a ina yake Sam ya kasa tuna komai,Malam ya tambayeshi yaro tsintar ka mukayi a titi su waye suka dakeka haka?Kuma daga wanne gari kake? Na’im ya fada tunani yayi yayi amma ya kasa tuna komai,cikin hausarsa da bata da kyau yace wlh bani San kowa ba,bana iya tuna komai,ban san kowa ba,Malam yace subhanallah Wala Allah dukan da mutanen suka yi maka shine yasa sun bugeka a kwakwalwa yasa baka iya tuna komai,yanzu samari Kaci gaba da Zama damu har Allah yasa Kwakwalwarka ta dawo dai dai ka fadi inda kake a maida kai can wajen iyayenka,shi dai Na’im murmushin yake yayi kawai yace to Dad,a’a ka dinga kiranshi Malam ni kuma Umma zakace cewar Haleematu matar Malam,yace to kawai yayi shuru abin duniya ya masa Zafi ya kasa tuna mutane da abinda ya shafeshi sai Hausa da turanci yasan abubuwa bai san ma’anar su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button